John
John 1
John 1:1-3
A cikin farko
Wannan na nufin farkon farin loƙaci kamin Allah ya halicci samai da duniya.
Kalmar
Wannan na nufin Yesu.
Dukan abu ta wurinsa aka yi su
"Allah ya halicci dukan komai ta wurin sa" (Dubi: figs_activepassive|)
babu abin da aka halitta sai ta wurin sa
Idan harshen ku be yarda da kalmar da ba daidai ba yakamata wannan kalman ya bayyana shi da kyau a "An halicci dukkan komai ta wurin sa." AT: "Allah ya halicci komai tare da shi" ko kuma "tare da shi akowai komai da an halitta wadda an riga an halitta " Allah ya halicci tare da shi komai da ya halitta" (Dubi: figs_activepassive and figs_doublenegatives)
John 1:4-5
A cikinsa rai ya ke, kuma wannan rai ya zama haske ga dukan mutane
"A cikinsa rai ya ke" magana ne game da sa komai ya rayu. kuma, "haske" magana na game da "gaskiya." AT: "shi ne ya sa komai ya rayu. Kuma ya bayyana wa mutane game da gaskiya akan Allah" (Dubi: figs_metonymy and figs_metaphor)
cikin sa
A nan "sa" ya na nufin wadda ake kiransa kalma.
Rai
Ku yi amfani da kalma ta musamman na "Rai." Idan ku na so ku daidaita, ku fasara ta kamar "rai ta ruhaniya."
Hasken ya haskaka a cikin duhu, kuma duhun bai rinjaye shi ba
A nan "haske" magana ne game da abin da ke da gaskiya da kuma kyau. Anan "duhu" magana ne game da abin da ba daidai ba ko mugu. (Dubi: figs_metaphor)
John 1:6-8
shaida game da hasken
A nan "haske" magana ne game da wahayin Allah a cikin Yesu. AT: "nuna yaɗa Yesu ya ke kamar hasken gaskiya na Allah"(Dubi: figs_metaphor)
John 1:9
haske na gaskiya
A nan haske magana ne da ke wakilcin Yesu wadda ya bayyana gaskiyan game da Allah kuma shi ne wannan gaskiyan. (Dubi: figs_metaphor)
John 1:10-11
Yana cikin duniya, kuma an halicci duniya ta wurinsa, amma duniya bata san shi ba
"ko da shike yana cikin wannan duniya, kuma Allah ya halicci komai ta wurinsa, mutane basu gane shi ba"
duniya bata san shi ba
Kalmar "duniya" magana ne da ke kamar mutane da suka yi rayuwa a duniya. "Mutanen basu san ko shi waye ne ba"(Dubi:figs_metonymy)
Ya zo wurin nasa, amma nasa basu karbe shi ba
"Ya zo wurin mutanen kasar sa, amma mutanen kasar sa basu karbe shi ba"
karɓe shi
"karɓe shi." Karban wani ya na nufin marabshen sa da kuma martaba shi da daraja da begen gina mutunshi tare da shi.
John 1:12-13
ba da gaskiya ga sunansa
Kalmar "suna" magana ne da ke kamar halin Yesu do komai game da shi. AT: "gaskanta da shi" (Dubi: figs_metonymy)
ya ba su 'yanci
"ya basu yanchin" ko " ya sa komai yiwuwa masu"
'ya'yan Allah
Kalmar "'ya'ya" magana ne da ke nufin dangantakan mu da Allah, wadda yake kamar 'ya'ya da Uba.(Dubi: figs_metaphor)
John 1:14-15
zama jiki
A nan "jiki" na wakilcin "mutum." AT: "zama mutum" (Dubi: figs_synecdoche)
makadaici shi kadai wanda ya zo daga Uban
Jumlan "makadaici" na nufin cewa shi dabam ne, babu wani kamarsa. Jumlan "wanda ya zo daga Uban" na nufin cewa shi ne ɗan Uba. AT: "ɗa na Uba wanda ya na nan dabam" ko kuma "Ɗa wanda shi ne kadai na Uba"
Uba
Wannan laƙani ne na mahimmi ga Allah (Dubi: guidelines_sonofgodprinciples)
cike da alheri
"cike da kyaukyawan aiyuka zuwa gare mu wadda bamu chanchanta ba"
Shi wanda ke zuwa a bayana
Yohanna na magana game da Yesu. Jumlan "zuwa a bayana" na nufin cewa aikin Yohanna ya riga ya fara kuma aikin Yesu ze fara jim kadan.
ya fi ni
"ya fi muhimmi fiye da ni" ko kuma" ya na da ikon fiye da ni"
domin ya kasance kafin ni
Ku yi hankali ka da ku fasara a hanyar da ze nuna cewa Yesu ya fi muhimmi domin ya girmi Yohanna bisa ga shekarun mutuntaka. Yesu ya fi Yahaya domin shi Ɗan Allah ne, wanda ya na da rai kullum.
John 1:16-18
cikarsa
Wannan kalma na nufin alherin Allah da babu iyaka.
alheri akan alheri
"albarka akan albarka"
John 1:19-21
Yahudawa suka aika... zuwa gareshi daga Urushalima
kalmar "Yahudawa" na nufin " shugabannin yahudawa". AT: "Shugabannin yahudawa suka aika... zuwa gareshi daga Urushalima"(Dubi: figs_synecdoche)
Ya fada dalla dalla ... kuma bai musunta ba, yana amsa masu cewa
Jumla na biyu ya bayyana abubuwan da jumla na farko ya bayyana a hanyar da ba daidai ba domin ya nanata cewa Yahaya yana faɗan gaskiya ne, yana kuma cewa ba shi ne Almasihu ba. Mai yiwuwa harshen ku ya na da hanya dabam na yin wannan.
To kai wanene?
"Me ne zancen, idan ba kai ne mai ceto ba?" ko kuma "Me ya ke faruwa?" ko kuma "Me ku ke yi?"
John 1:22-23
Mahaɗin Zance:
Yahaya ya shigaba da magana da fristoci da kuma levites.
sun ce masa
"fristocin da levites sun ce wa Yahaya"
mu
fristocin da levites, ba Yahaya ba (Dubi: figs_exclusive)
ya ce
"Yahaya ya ce"
Ni murya ne, da ke kira cikin jeji
Yahaya ya na cewa anabcin Ishaya na game da shi. Kalmar "murya" anan na nufin mutumin da ke kira a cikin jeji. AT: "ni ne ina kira a cikin jeji"(Dubi: figs_metonymy)
Ku daidaita hanyar Ubangiji,' kamar yadda annabi Ishaya ya fada
A nan an yi amfani da kalmar "hanya". AT: "shirya kanku wa zuwan Ubangiji kamar yadda mutane su ke shirya hanya wa mutum mai daraja" (Dubi: figs_metaphor)
John 1:24-25
Yanzu wadansu daga wurin Farisawa
Wannan bayanin labari ne game da mutane da sun tambaye Yahaya. (Dubi: writing_background)
John 1:26-28
Muhimmin Bayani:
Aya 28 ya faɗa mana asalin bayani game da shirin labarin. (Dubi: writing_background)
wanda ke zuwa a bayana
Ya kamata ku bayyana abin da zai yi idan ya zo. AT: "wanda zai yi maku wa'azi bayan na tafi" (Dubi: figs_explicit)
ni, wanda ko igiyar takalminsa ban isa in kwance ba
Dama kwancen takalma aikin bawa ne.Wannan magana ne na aiki mara daɗi na bawa. AT: "ni, wanda ban cancanta in yi bauta a hanya da ba daɗi" ko "ni. ban cancanci in kwance igiyar takalminsa ba" (Dubi: figs_metaphor)
John 1:29-31
Ragon Allah
Wannan magana ne wadda yake wakilcin cikakken hadayan Allah. Ana kirin Yesu "Ragon Allah" domin an yi hadayarsa domin zunuban mutane. (Dubi: figs_metaphor)
duniya
Kalmar "duniya" magana ne wadda ya ke nufin dukkan mutane a cikin duniya. (Dubi: figs_metonymy)
Shi wanda ke zuwa bayana ya fi ni, domin ya kasance kafin ni
Dubi yadda an fasara wannan a cikin 1:15.
John 1:32-34
saukowa
saukowa daga sama
kamar kurciya
Wannan jumlan tamka ne. "Ruhun" ya sauka kamar yadda kurciya yake sauka a kan mutum. (Dubi: figs_simile)
sama
Kalmar "sama" na nufin "sarari."
Ɗan Allah
Wadansu matanin sun ce "Ɗan Allah"; wadansu kuma suka ce "zaɓi na Allah." (Dubi: translate_textvariants)
Ɗan Allah
Wannan muhimmin laƙani ne wa Yesu, Ɗan Allah.(Dubi: guidelines_sonofgodprinciples)
John 1:35-36
Kuma, washegarin
Wannan wata rana ne. Rana na biyu ne wadda Yahaya ya gan Yesu.
John 1:37-39
sa'a ta goma
"sa'a ta goma." Wannan Jumlan ya na bayyana loƙacci da rana, kafin duhu, wadda ba za a iya yin tafiya zuwa wata gari ba, mai yiwuwa sa'a hudu na yamma.
John 1:40-42
ɗan Yahaya
Wannan ba Yahaya mai baftisma ba ne. "Yahaya" sanannen suna ne.
John 1:43-45
Filibus asalin dan Baitsaida ne, garin Andarawus da Bitrus
Wannan ne labari game da Filibus. (Dubi: writing_background)
John 1:46-48
Natana'ilu ya ce masa
"Natana'ilu ya ce wa Filibus"
za a iya samun wani abu nagari a Nazarat?
Wannan furucin ya bayyana kamar tambaya ne domin a kara nanaci. AT: "Ba bu abu mai kyau da zai fito daga Nazarat!" (Dubi: figs_rquestion)
wanda babu yaudara a cikinsa
AT: "cikakken mutumin gaskiya" (Dubi: figs_litotes)
John 1:49-51
Don na ce maka ... ka gaskanta?
Wannan furucin ya bayyana kamar tambaya domin a ba da nanaci. AT: "ka gaskanta domin na ce, na gan ka a karkashin bishiyan baure'! (Dubi: figs_rquestion)
Hakika, hakika
Ku fasara wannan a yadda harshen ku zai nanata cewa an fahinci muhimmin abin da ke da gaskiya.
John 2
John 2:1-2
Muhimmin Bayani :
An gayyaci Yesu da almajiransa zuwa aure. Wannan ayan ya ba da asalin bayani game da shirin labarin. (Dubi: writing_background)
Bayan kwana uku
Yawancin masu fasara su na karanta wannan da cewa bayan kwana na uku ne Yesu ya kira Filibus da Nataniel don su bi shi. Ranar farko ya faru a cikin 1:35 da kuma na biyun a cikin 1:43.
An gayyaci Yesu da almajiransa zuwa aure
AT: "Wani ya gayyaci Yesu da almajiransa zuwa aure" (Dubi: figs_activepassive)
John 2:3-5
Mace
Wannan ya na nufin Maryamu. Idan ba shi da kyau ɗa ya kira Uwarsa "Mace" a harshenku, sai ku yi amfani da da wata kalma mai kyau ko kuma ku bari.
me yasa kika zo wurina?
An yi wannan tambaya domin a ba da nanaci. AT: "wannan bai shafe ni ba." ko kuma "kadda ku faɗa mani abin da zan yi." (Dubi: figs_rquestion)
Loƙaci na bai yi ba tukuna
Kalmar "loƙaci" magana ne da ke wakilcin loƙacin da ya cancanta wa Yesu don ya nuna cewa shi ne mai ceto ta wurin aikin al'ajibi. AT: "Loƙacin bai kai ba da zan yi baban abu" (Dubi: figs_metonymy)
John 2:6-8
durom biyu ko uku
Za ku iya juya wannan zuwa awu na zamani. AT: "75 zuwa lita 115" (Dubi: translate_bvolume)
makil
Wannan ya na nufin "zuwa sama" ko kuma "cikakke."
shugaban biki
Wannan ya na nufin mutumin da ke dauki da shugabancin abinci da ruwan sha.
John 2:9-10
amma ma'aikatan wadanda suka jawo ruwan sun sani
Wannan ita ce bayanin zancen. (Dubi: writing_background)
shanye
rashin iya bambanta sakanin ruwa mai arha da ruwa mai tsada domin shan giya dayawa
John 2:11
Mahaɗin Zance:
Wannan ayan bata cikin asalin labarin, amma ta na ba da ra'ayi game da labarin. (Dubi: writing_newevent)
Kana
Wannan sunan wuri ne. (Dubi: translate_names)
bayyana daukakarsa
Anan "daukakarsa" ya na nufin baban ikon Yesu. AT: "nuna ikonsa"
John 2:12
tafi
Wannan ya na nuna cewa sun wuce daga wuri mai sauki zuwa wuri mai tsawo. Kafarnahum ya na ta arewankudu na Kana da tsawo mai sauki.
'yan'uwansa
Kalmar "'yan'uwansa" na a hade ne da 'yan'uwa da kuma 'yar'uwa. Yesu ya girme dukkan 'yan'uwaninsa.
John 2:13-14
wuce zuwa Urushalima
Wannan ya na nuna cewa ya wuce daga wuri mai sauki zuwa wuri mai tsawo. An gina Urushalima a kan tudu.
na zaune a wurin
Aya na biye ya nuna cewa wadannan mutanin na cikin fegan haikali. An yi wannan wurin domin sujada ne ba domin kasuwanci ba.
wadanda suke sayar da tumaki da tantabaru
Mutane su na sayan dabbobi a cikin fegan haikali domin su yi hadaya wa Allah.
masu canjin kudi
Hukumomin Yahudawa sun so mutanin da za su saya dabbobi don hadaya da cewa su canza kuɗin su zuwa ga wata kuɗi daga "masu canjin kuɗi."
John 2:15-16
Sai
Wannan kalmomin ya na da alamun abubuwan da ya faru domin wani abin da ya faru a farko. Don hakka, Yesu ya gan masu canza kuɗi a zaune a cikin haikali.
Daina maida gidan Ubana wurin kasuwanci
"Daina saya da sayad da abubuwa a cikin gidan Ubana"
gidan Ubana
Wannan jumla ne wadda Yesu ya yi amfani a matsayin haikali.
Ubana
Wannan lakami ne ta muhimmi da Yesu ya yi amfani wa Allah. (Dubi: guidelines_sonofgodprinciples)
John 2:17-19
a rubuce yake
AT: "wani ya rubuto" (Dubi: figs_activepassive)
gidanka
Wannan ya na nufin haikali, gidan Allah.
cinye
Kalmar "cinye" ya na nuna maganar "wuta." Kaunar Yesu ga haikalin ya na nan ne kamar wuta da ke konewa a cikinsa. (Dubi: figs_metaphor)
alama
Wannan ya na nufin abu ne wadda ya ke nuna cewa abin gaskiya ne.
wadannan abubuwan
Wannan ya na nufin yadda Yesu ya yi wa masu canza kuɗi a cikin haikali.
rushe wannan haikali ... zan gina shi
Yesu ya na bayyana yanayin abin da zai faru idan abin da ba gaskiya ba ne ya zama gaskiya. Don haka, zai gina haikalin idan hukumomin Yahudawa sun rushe ta. Ba wai yana yabon hukumomin Yahudawan don su rushe haikalin ba. Za ku iya fasara kalmomin "rushe" da kuma "gina" ta wurin amfani da kalmomin. AT: "Idan kun rushe wannan haikalin, Haƙiƙa zan gina shi" ko kuma " Za ku iya tabatar da cewa idan kun rushe wannan hakalin, Zan gina shi" (Dubi: figs_hypo and figs_metaphor)
gina shi
"sa shi ya tsaya"
John 2:20-22
shekaru arba'in da shidda ... kwanaki uku
shekaru arba'in da shidda ... kwanaki uku" (Dubi: translate_numbers)
za ka dau kwanaki uku kadai wajen gina shi?
Wannan magana ya bayyana kamar tambaya ne domin ya nuna cewa hukuman Yahudawa sun gane cewa Yesu ya na so ya rushe haikalin sai ya kuma gina ta a kwanaki uku. "gina" karin magana ne na "kafa." AT: "za ku kafa ta a kwanaki uku?" ko kuma "ba za ku iya gina ta a cikin kwanaki uku ba!" (Dubi: figs_rquestion and figs_idiom)
gaskanta
A nan "gaskanta" ya na nufin amsa wani abu ko kuma yarda cewa gaskiya ne.
wannan kalami
Wannan ya na nufin kalamin Yesu a cikin 2:19.
John 2:23-25
Yanzu, a loƙacin da ya na Urushalima
Kalmar "yanzu" yana gabatar da mu zuwa ga sabon abu a cikin labarin.
gaskata ga sunansa, sa'adda suka ga alamun da ya yi
A nan "suna" magana ne da ke wakilcin Yesu. AT: "gaskanta da shi" (Dubi: figs_metonymy)
alamun da ya yi
Ana iya kiran abin ban mamaki "alamu" domin an yin amfani da su don su nuna cewa Allah mai iko ne wadda yake da iko akan duniya.
game da mutum, domin ya san abinda ke cikin sa
A nan kalmar "mutum" ya na wakilcin mutane. AT: "game da mutane, domin ya san abin dake a cikin mutane" (Dubi: figs_gendernotations)
John 3
John 3:1-2
Muhimmin Bayani:
Nikodimu ya zo ya gan Yesu.
Yanzu
An yi amfani da wannan kalma a nan domin a nuna sabon sashin labarin da kuma gabatar da Nikodimu. (Dubi: writing_participants)
mun sani
"A nan "ku" ya na nufin Nikodimu da kuma sauran mutanin majalisan Yahudawa.
John 3:3-4
Mahaɗin Zance:
Yesu da Nikodimu sun cigaba da magana.
Hakika, hakika
Dubi yadda an fasara wannan a cikin 1:51.
sake haifuwa
"haifafe daga sama" ko kuma "haifafe na Allah"
mulkin Allah
Kalmar "mulki" magana ne game da shugabancin Allah. AT: "wurin da Allah yake shugabanci" (Dubi: figs_metaphor)
Yaya za a sake haifuwar mutum bayan ya tsufa?
Nikodimu ya yi amfani da wannan tambayan domin ya nanata cewa ba zai iya faruwa ba. AT: "hakika, ba za a iya haifan mutum kuma bayan ya tsufa ba!" (Dubi: figs_rquestion)
Ba zai iya sake shiga cikin cikin uwarsa kuma a haife shi ba, zai iya?"
Nikodimu ya kuma yi amfani da wannan tambayan domin ya bayyana ra'ayin shi da cewa haifuwa na biyu ba shi yiwuwa. "hakika, ba zai iya shigan cikin cikin Uwarsa na biyu ba! (Dubi: figs_rquestion)
so biyu
"kuma"
ciki
wata sashin jikin mace wadda yaro yake girma a ciki
John 3:5-6
haifafe ta ruwa da kuma Ruhu ba
AT: 1) "yi baftisma a cikin ruwa da kuma ruhu" ko kuma 2) "haifafe ta jiki da kuma ta ruhaniya" (Dubi: figs_metaphor)
shiga cikin mulkin Allah ba
Kalmar "mulki" magana ne game da shugabancin Allah a rayuwan mutum. AT: "ya ji shugabancin Allah a rayuwanrsa" (Dubi: figs_metaphor)
John 3:7-8
dole ne a haife ka kuma
"Dole ne a haife ku daga sama"
Iska takan hura duk inda ta ga dama
A ainahin harshen, iska da Ruhu kalma daya ne. Mai magana anan ya na maganan iska kamar mutum ne. AT: "Ruhu mai Tsarki ya na nan kamar iska wadda yake huruwa a duk inda yake so" (Dubi: figs_personification)
John 3:9-11
Yaya wannan zai yiwu?
Wannan tambayan ya kara bayani ne a jumlan. AT: "Wannan ba ya yiwuwa!" ko kuma "Wannan ba zai iya faruwa ba!" (Dubi: figs_rquestion)
Kai mallami ne na Israila amma ba ka san wadannan al'amura ba?
Wannan tambayan ya kara bayani ne a jumlan. AT: "Kai mallami ne na Israila, Ina mamaki cewa ba ka gane wadannan abubuwa ba!" (Dubi: figs_rquestion)
muna fadin
Yesu bai hada da Nikodimu ba a loƙacin da ya ce "mu". (Dubi: figs_exclusive)
John 3:12-13
to yaya zaka gaskata idan na gaya maka abubuwa na sama?
Wannan tambaya ya nanata rashin gaskantawar Nikodimu. AT: "hakika, ba za ku gaskanta ba idan na gaya maku game da abubuwan sama!" (Dubi: figs_rquestion)
to yaya zaka gaskata idan na gaya maka
A dukkan wuraren "ka" daya ne. (Dubi: figs_you)
abubuwa na sama
abubuwan ruhaniya
sama
Wannan ya na nufin wurin da Allah yake.
John 3:14-15
Kamar yadda Musa ya ta da maciji a jeji, haka ma dole a ta da Dan Mutum
Wannan karin magana ne. Wadansu mutane za su "ta da" Yesu kamar yadda Musa ya "ta da" macijin a cikin jeji. (Dubi: figs_simile)
a cikin jeji
Jejin ya bushe, tsararin wuri, amma a nan ya na nufin wurin da Musa da Isra'ilawa su ka yi tafiya na shekaru arba'in.
John 3:16-18
Gama Allah ya kaunaci duniya sosai
A nan "duniya" magana ne da ke nufin kowa a duniya. (Dubi: figs_metonymy)
kaunaci
Wannan ne irin kauna da ke zuwa daga Allah kuma ya na nan a kan wadansu, ko a loƙacin da bai ribanya ba. Allah da kansa ne kauna kuma shi ne hanyar kauna ta gaskiya.
Gama Allah bai aiko da Ɗansa cikin duniya domin ya kayar da duniya ba, amma domin a ceci duniya ta wurin sa
An bayyana wadannan kalmomin da ke nufin abu daya, na farko daidai sai kuma wadda ba daidai ba. Wadansu harshen su na iya nanata a hanya dabam. AT: "Ainahin dalilin da Allah ya aiko ɗansa a duniya shi ne domin ya cece ta" (Dubi: figs_parallelism and figs_doublenegatives)
ya kayar
"ya hukunta." "Hukunta" ya na nuna cewa Allah ya na karban mutum bayan an hukunta shi. A loƙacin da an kayar da mutum, ana hukunta shi kuma Allah ba ya karban shi.
Ɗan Allah
Wannan muhimmin lakabi ne wa Yesu. (Dubi: guidelines_sonofgodprinciples)
John 3:19-21
haske ya zo duniya
Kalmar "haske" magana ne game da gaskiyar Allah da ke a bayyane a cikin Yesu. Yesu ya yi magana game da kansa a cikin mutum na uku. Idan harshen ku ba ya yarda mutane su yi maganan kansu a cikin mutum na uku, za ku iya bayyana wadda ya kasance hasken. "Duniya" magana ne game da dukkan mutane da suke a cikin duniya. AT: "Wadda yake kamar haske ya bayyana gaskiyar Allah wa dukkan mutane" ko kuma "Ni, wadda nake kamar haske, na zo cikin duniyan" (Dubi: figs_metaphor and figs_metonymy and figs_123person)
mutane suka kaunaci duhu fiye
A nan "duhu" magana ne game da mugu. (Dubi: figs_metaphor)
domin kada ayyukansa su bayyanu
AT: "domin kadda hasken ya nuna abin da yake yi" ko kuma "domin kadda hasken ya bayyana ayukansa" (Dubi: figs_activepassive)
hasken domin ayyukansa
AT: "mutane za su iya ganin ayukansa da kyau" ko kuma "kowa zai iya ganin abubuwan da yake yi da kyau" (Dubi: figs_activepassive)
John 3:22-24
Bayan wannan
Wannan ya na nufin bayan Yesu ya yi magana da Nikodimu. Dubi yadda kun fasara wannan a cikin 2:12.
Ainon
Wannan kalmomin na nufin "rafi," kamar na ruwa.(Dubi: translate_names)
Salim
wata kawye dake kusa da rafin Joda (Dubi: translate_names)
domin akwai ruwa da yawa a can
"domin akwai rafi dayawa a wurin"
sun yi Baftisma
AT: "Yahaya ya na yi masu baftisma" ko kuma "ya na yi masu baftisma" (Dubi: figs_activepassive)
John 3:25-26
Sai gardama ta taso tsakanin almajiran Yahaya da wani Bayahude
AT: "Sai almajiran Yahaya da wani Bayahude suka fara jayayya" (Dubi: figs_activepassive)
gardama
faɗa da amfani da kalmomi
ka shaida, duba, yana baftisma
A cikin wannan jumlan, "duba" umurni ne dake nufin "sa hankali!" AT: "ka shaida, 'duba! Ya na yin baftisma," ko kuma "ka shaida. ;dubi wancan! Ya na yin baftisma," (Dubi: https://git.door43.org/Door43/en_ta/src/master/translate/figs-explicit/01.md)
John 3:27-28
Mutum ba zai iya samun wani abu ba sai
"Ba bu wanda yake da iko saidai"
an ba shi daga sama
A nan maganan "sama" na nufin Allah. AT: "Allah ya ba shi shi" (Dubi: figs_metonymy and figs_activepassive)
Ku da kanku
Wannan "ku" ya na nufin dukkan mutane da Yahaya yake magana da su. AT: "Dukkan ku"(Dubi: figs_you and figs_rpronouns)
an aiko ni kafin shi
AT: "Allah ya aike ni don in isa kafin shi" (Dubi: figs_activepassive)
John 3:29-30
Amaryar ta angon ce
A nan "amarya" da "anga" karin magana ce. Yesu ya na nan kamar "angon" kuma Yahaya ya na nan kamar abokin "angon." (Dubi: figs_metaphor)
Wannan, shi ne, murnata ta cika
AT: "Don haka na yi farinciki sosai" (Dubi: figs_activepassive)
Murnata
Kalmar "na" ya na nufin Yahaya mai baftisma, wadda yake magana.
Dole shi ya karu
"Shi" ya na nufin ango, Yesu, wanda zai cigaba da girma a cikin daraja.
John 3:31-33
Shi wanda ya fito daga sama ya fi kowa
"Shi wanda ya fito daga sama ya fi kowa muhimmi"
Shi Wanda ya zo daga duniya, na duniya ne, kuma game da duniya yake magana
Yahaya ya na nufin cewa Yesu ya fi shi da shike Yesu ya na daga sama, kuma an haife Yahaya a duniya. AT: "shi wadda yake haifaffe a duniyan nan ya na nan kamar kowane mutum da yake rayuwa a duniya kuma yana magana game da abin da yake faruwa a cikin wannan duniya" (Dubi: figs_metonymy)
Shi wanda ya fito daga sama ya fi kowa
Wannan ya na nufin abu daya ne a jumla na farko. Yahaya ya nanata wannan don bayani.
Ya shaida abubuwan da ya ji ya kuma gani
Yahaya ya na magana game da Yesu. AT: "wadda yake sama ya na magana game da abin da ya ji ya kuma gani a sama"
babu wanda ya karbi shaidarsa
Yahaya ya nanata bayanin a nan cewa mutane kadan ne suka gaskanta da Yesu. AT: "mutane kadan ne sun gaskanta da shi" (Dubi: figs_hyperbole)
Duk wanda ya karbi shaidarsa
"Duk wanda ya gaskanta da abin da Yesu ya ce"
ya tabbatar
"nuna" ko "yarda"
John 3:34-36
Domin duk wanda Allah ya aika
"Wannan Yesu, wadda Allah ya aike shi don ya zama wakilinsa"
Domin bai bada Ruhun da ma'auni ba
"Domin shi ne wadda Allah ya ba da dukkan ikon Ruhunsa"
Uban ... Ɗan
Wadannan muhimmin lakabi ne wadda suke kwatanta dangantaka sakanin Allah da Yesu. (Dubi: guidelines_sonofgodprinciples)
bayar ... a hanunsa
Wannan ya na nufin sa a ikonsa. (Dubi: figs_idiom)
Shi wanda ya bada gaskiya
"mutum da ya gaskanta"
fushin Allah na kansa
Ana iya bayyana kalmar "fushi". AT: "Allah zai cigaba da hukunta shi" (Dubi: https://git.door43.org/Door43/en_ta/src/master/translate/figs-abstractnouns/01.md)
John 4
John 4:1-5
Muhimmin Bayani:
Yahaya 4:1-6 ya ba da bayanin abin da zai faru, maganan Yesu da ba-Samarya. (Dubi: writing_background)
Yanzu Yesu ya sani cewa Farisawa sun ji cewa yana yin ... Yahaya (ko da shike ... ke), ya bar ... Galili
"Yanzu yesu ya na yin ... Yahaya (ko da shike ... ke), kuma Farisawa su ka ji game da ci gaban da yake yi. Ya sani cewa Farisawan sun ji, sai ya bar ... Galili"
Yanzu sa'anda Yesu ya sani
An yi amfani da kalmar "yanzu" domin ya nuna ainahin abin da ze faru. A nan Yahaya ya fara faɗan sabon sashin bayyanin.
ko da shike ba Yesu da kansa ke yin baftismar ba, amma almajiransa ne
Maganar "kansa" ya kara bayyana cewa ba Yesu ne ya ke yin baftisma ba, amma almajiransa ne.(Dubi: figs_rpronouns)
John 4:6-8
Ba ni ruwa
"Wannan ruko ne da ladabi, ba umurni ba.
Gama almajiransa sun tafi
Bai ce wa almajiransa su diba ma shi ruwa ba domin sun tafi.
John 4:9-10
Sai ba-Samariyar tace masa
Kalmar "masa" ya na nufin Yesu.
Yaya kai da kake Bayahude kake tambayan .... abin sha?
Wannan magana ya bayyana kamar tambaya domin ya nuna mamakin ba-Samariya, cewa Yesu ya tambaye ta abin sha. AT: "Ban yarda cewa, yadda ke Bayahude, ka na tambayan abin sha ba!" (Dubi: figs_rquestion)
ba su harka da
"ba ya tare da "
ruwan rai
Yesu ya yi amfani da maganan "ruwan rai" don ya nuna Ruhu mai Tsarki wadda yake aiki a cikin mutum domin canza da kuma sabonta rayuwa. (Dubi: figs_metaphor)
John 4:11-12
Ai ba ka fi Ubanmu Yakubu ba, ko ka fi shi ... shanu?
Wannan maganan ya zo kamar tambaya domin karin bayani. AT: "Ba ku fi Uban mu Yakubu ba ... shanu!" (See: figs_rquestion)
Ubanmu Yakubu
"kakaninmu Yakubu"
sha daga cikin ta
"sha ruwan da ya fito daga ita"
John 4:13-14
zai sake jin kishi
"ba zai sake shan ruwa kuma ba"
ruwan da zan bashi zai zama mabulbular ruwa a cikinsa
A nan kalmar "mabulbular" magana ne na rai da ke ba da ruwa. AT: "ruwan da zan ba shi zai zama kamar bulbular ruwa a cikinsa" (Dubi: figs_metaphor)
rai madawwami
A nan "rai" ya na nufin "rai na ruhaniya" wadda Allah ne kadai zai iya ba da.
John 4:15-16
Mallam
A cikin wannan lamarin, ba-Samariyar ta na kiran Yesu "Mallalm," wadda yake a matsayin biyayya ko ladabi.
dibi ruwa
"samu ruwa" ko kuma "ja ruwa daga rijiya" ta amfani da guga
John 4:17-18
Kin fadi daidai da kika ce ... Abinda kika fada gaskiya ne
Yesu ya sake nanata wannan jumala domin ya bayyana cewa ya san matan ta na faɗan gaskiya ne.
John 4:19-20
Na ga kai annabi ne
"Na iya gane cewa kai annabi ne"
Ubaninmu
"Ubaninmu" ko kuma "Kakaninmu"
John 4:21-22
gaskata da ni
gaskanta da mutum ya na nufin yarda da cewa abin da mutumin ya ce gaskiya.
Ku kuna bauta wa abinda ba ku sani ba. Mu na bauta wa abin da mun sani
Yesu ya na nufin cewa Allah ya bayyana kansa da dokokinsa wa mutanin Yahudawa, ba wa yan samariya ba. Ta wurin littafi ne mutanin Yahudawan sun san Allah da kyau fiye da yan Samariya.
za ku yi wa Uban sujada ... ceto daga Yahudawa yake
Ceta na har abada daga zunubi ya na zuwa ne daga Allah Uba, wadda shi ne Yahwe, Allah Yahudawa.
Uba
Wannan muhimmin lakabi ne wa Allah. (Dubi: guidelines_sonofgodprinciples)
gama ceto daga Yahudawa yake
Wannan ba ya nufin cewa mutanin Yahudawa ne za su cece sauran daga zunubinsu. Ya na nufin cewa Allah ya zabi Yahudawa a matsayin mutane wadda za su gaya wa mutane game da cetonsa. AT: "gama dukkan mutane za su san game da ceton Allah saboda Yahudawan"
John 4:23-24
Mahaɗin Zance:
Yesu ya ci gaba da magana da ba-Samariyar.
Koda shike, sa'a tana zuwa, har ma ta yi, wadda masu sujada na gaskiya za su yi
"Koda shike, yanzu ne loƙacin da ya kamata masu sujada na gaskiya su"
Uban
Wannan muhimmin lakabi ne wa Allah. (Dubi: guidelines_sonofgodprinciples)
yi sujada cikin ruhu da gaskiya
"yi masa sujada a hanya mai kyau"
John 4:25-26
Na san Mai ceto ... Almasihu
Duk kalmomin nan suna nufin "sarkin da Allah ya alkawatar."
zai bayyana mana kowane abu
Kalmar "bayyana kowane abu" ya na nufin dukkan abin da yakamata mutane su sani. AT: "zai gaya mana kowane abu da ya kamata mu sani" (Dubi: figs_explicit)
John 4:27
A daidai wannan lokaci, almajiransa suka dawo
"Yayin da Yesu ya na faɗan wannan, almajiransa suka dawo daga gari"
Suna ta mamakin dalilin da yasa yake magana da mace, amma babu wanda yace
Ba sananne abu ne ba-Yahude ya yi magana da mace da bai sani ba, har idan matan ba-Samariyar.
babu wanda yace, Me ... so?" Ko kuma "Don me ... ita?"
AT: 1) Almajiran suke yi wa Yesu tambayoyin ko kuma 2) "ba bu wadda ya tambayi matan, 'Me ... so?' ko kuma tabayi Yesu, 'Me ... ita?"
John 4:28-30
Ku zo ku ga wani mutum wanda ya gaya mani duk wani abu da na taba yi
ba-Samariyar ta zuguiguita domin ta nu na cewa ta yi farinciki da yadda Yesu ya san komai game ta ita. AT: "Zo ku ga wani mutum wadda ya san ni sosai, kodashike ban san shi ba" (Dubi: figs_hyperbole)
Wannan dai ba Almasihun bane, ko kuwa?
Matan ba ta tabatar cewa Yesu ne Almasihu, sai ta yi tambaya da ta ke tsammanin amsan "babu," amma ta sake yin tambaya a maimakon yin magana domin ta na son mutanin su zaba wa kansu.
John 4:31-33
A wannan lokacin
"Loƙacin da matan ta na shigan cikin gari"
almajiransa suna rokansa
"almajiran su na gaya wa Yesu" ko kuma "almajiran su na karfafa Yesu"
ina da abinci da ba ku san komai akai ba
A nan Yesu ba ya maganan asalin "abinci," amma ya na shirya almajiransa domin koyi ta ruhaniya a cikin 4:34.
Babu wanda ya kawo masa wani abu ya ci, ko akwai ne?
Almajiran su na tunani ko ya na magana game da asalin abinci ne. Sun fara tambayan junansu wannan tambaya, su na sa rai da amsan "babu." AT: "hakika ba bu wadda ya kawo masa abinci a loƙacin da muke cikin gari!" (Dubi: figs_rquestion)
John 4:34-36
Abincina shine in yi nufin wanda ya aiko ni, in kuma cika aikinsa
A nan "abinci" magana ce da ke wakilcin "yin biyayya da nufin Allah." AT: "Kamar yadda abinci ya ke ƙosad da mutum mai yunwa, biyayya da nufin Allah ne abin da ke ƙosad da ni" (Dubi: figs_metaphor)
ku kan ce
"ba wannan ne wata sanannan magana ba"
daga idanunku ku ga gonakin, sun rigaya sun isa girbi
Kalmomin "gonaki" da "isa girbi" zance ce. Gonakin na wakilcin mutane. Kalmar "isa girbi" ya na nufin cewa mutanin su na shirye domin su karba sakon Yesu, kamar gonaki da sun isa girbi. AT: "Dubi sama ku ga mutane! Su na a shirye don su gaskanta da sako na, kamar 'ya'ya a gonaki na da sun isa mutane su girba su" (Dubi: figs_metaphor)
kuma tattara amfanin gona zuwa rai na har abada
A nan "amfanin gona zuwa rai na har abada" magana ce dake wakilcin mutane da sun gaskanta da sakon Almasihu sun kuma karbi rai na har abada. AT: "kuma mutanin da sun gaskanta da sakon sun kuma karbi rai na har abada su ne su na nan kamar amfanin gona da mai girbi yake tarawa" (Dubi: figs_metaphor)
John 4:37-38
Wani ya shuka, wani kuma na girbi
Kalmomin "shuka" da kuma "girbi" zance ne. Wadda ya na "shuka" ne yake bayyana sakon Yesu. Wadda yake "girbi" ne yake taimake mutanin don su karbi sakon Yesu. AT: "mutum daya ya na shuka irin, sai kuma wani mutum yana girbe 'ya'yan" (Dubi: figs_metaphor)
kun shiga cikin wahalarsu
"yanzu kana saduwa da aikinsu"
John 4:39-40
gaskanta da shi
"gaskanta da" wani ya na nufin "yarda" da mutumin. A nan, wannan ya na kuma nufin gaskanta cewa shi ne Ɗan Allah.
Ya gaya mani duk abinda na taba yi
Wannan zuguiguita ce. Matan ta ji dadi da yadda yesu ya san game da ita. AT: "ya gaya mani abubuwa dayawa game da rayuwana" (Dubi: figs_hyperbole)
John 4:41-42
kalmarsa
A nan "kalma" magana ne da ke wakilcin sakon da Yesu ya faɗa. AT: "sakonsa" (Dubi: figs_metonymy)
duniya
"duniya" magana ne wa masubi a dukkan duniya. AT: "dukkan masubi a cikin duniya" (Dubi: figs_metonymy)
John 4:43-45
bar wurin
daga Juda
Domin Yesu da kansa yace
An kara kalmar "kansa" domin a bayyana cewa Yesu ya "ce" wannan ... Ku na iya fasara wannan a harshen ku a hanyar da zai bayyana wa mutum. (Dubi: figs_rpronouns)
ba a girmama annabi a kasarsa
"mutane ba su nuna daraja ko girma wa annabin kasarsu" ko kuma "mutane ba su daraja annabi a garinsa"
wurin idin
A nan idin ita ce idin ketarewa.
John 4:46-47
Yanzu
An yi amfani da wannan kalma domin a sa alaman fashi a ainahin labarin, a kuma je wata sashin labarin. Idan ku na da wata hanyar yin wannan a harshen ku, za ku iya amfani da shi.
ma'aikacin fada
wanin da yake aiki wa sarki
John 4:48-50
Sai dai kun ga alamu da mu'ujizai ba, ba za ku gaskanta ba
"Sai dai ... ba za ku gaskanta ba." A wadansu harshuna, yana da kyau a fasara wannan jumla a hanya mai kyau. AT: "da ce kun ga abin al'ajibi ne da kun gaskanta" (Dubi: figs_doublenegatives)
gaskanta da kalman
A nan "kalma" magana ce dake nufin sakon da Yesu ya yi magana. AT: "gaskanta da sakon" (Dubi: figs_metonymy)
John 4:51-52
Yayin
An yi amfani da wannan kalma a abubuwa biyu da ke faruwa a loƙaci daya. Yayin da ma'aikacin ya na tafiya gida, bayinsa suna zuwan samin shi a hanya.
John 4:53-54
Sabili da haka, shi dakansa da dukan gidansa suka bada gaskiya
An yi amfani da kalmar "kansa" domin a bayyana kalmar "shi." Idan ku na da wata hanyar yin wannan a harshen ku, za ku iya amfani da shi.
alama
Ana iya kiran abubuwan al'ajibi "alamu" domin su na nuna cewa Allah mai daraja ne wadda yake da cikakken iko a duniya.
John 5
John 5:1-4
Muhimmin Bayani:
Wannan ne abin da ya faru a labari na biye, wadda Yesu ya tafi Urushalima ya kuma warkad da mutum. Wadannan Ayoyin sun ba da ainahin bayani game da shirin labarin. (Dubi: writing_background)
Bayan wannan
Wannan ya na nufin bayan Yesu ya warkad da ɗan ma'aikacin. Dubi yadda kun fasara wannan a cikin 3:22
akwai idi na Yahudawa
"Yahudawan su na bikin idi"
tafi Urashalima
Urashalima ya na kan tudu. Hanyoyi zuwa Urashalima su na tafiya sama da kasan ƙanƙanin tudu. Idan harshen ku ta na da wata hanya dabam na tafiya a kan tudu fiye da na tafiya a kan hanya, za ku iya yin amfani da shi a nan.
tabki
Wannan rami ne wadda mutane su ke cika da ruwa. Wata loƙaci suna bin su tabkin da tiles ko da aikin duse.
Baitasda
sunan wuri (See: translate_names)
shirayi rufi
jinkan gini wadda bango daya ya bata kuma ya na haɗe da su gini
Taron mutane dayawa
"mutane dayawa"
John 5:5-6
ya na wurin
"ya na tabkin Baitasda" (John 5:1)
shekara talatin da takwas
"shekaru talatin da takwas" (Dubi: translate_numbers)
ya gane
"ya fahinci"
ya ce masa
"Yesu ya ce wa mutum da ya cakume"
John 5:7-8
Malam, bani da
A nan kalmar "Mallam" hanya ce na magana da ladabi.
loƙacin da ruwan ya motsa
AT: "loƙacin da mala'ika ya motsa ruwan" (Dubi: figs_activepassive)
cikin tabkin
Wannan rami ne a kasa wadda mutane su ke cika da ruwa. Wata loƙaci suna bin su tabkin da tiles ko da aikin duse. Dubi yadda kun fasara "tabkin" a cikin 5:2.
wani ya riga ni
"kullum wani dabam ya na riga ni shigan cikin ruwan"
tashi
"tashi tsaye"
ka dauki shimfidarka ka tafi
"dauki shimfidarkuanar ka, ka yi tafiya!"
John 5:9
Mutumin ya warke
"mutumin ya samu lafiya kuma"
Yanzu ranar
Marubucin ya yi amfani da kalmar "yanzu" domin ya nuna cewa kalmomin na bayani ne wadda ke biye.(Dubi: writing_background)
John 5:10-11
Sai Yahudawa suka ce masa
Yahudawa (musamman shugabanin Yahudawa) sun yi fushi a loƙacin da sun ga mutumin ya dauki shimfidarsa a ranar Asabar.
Asabar ce
"Ranar hutun Allah ce"
Shi wanda ya warkar da ni
"mutumin da ya sa ni lafiya"
John 5:12-13
Suka tambaye shi
"Shugabanin Yahudawa su ka tambaye mutumin da an warkar da shi"
John 5:14-15
Yesu ya same shi
"Yesu ya same mutumin da ya warkar"
Dubi
An yi amfani da kalmar "Dubi" a nan domin a jawo hankali zuwa kalmomin da zai bi.
John 5:16-18
Yanzu
Marubucin ya yi amfani da kalmar "yanzu" don ya nuna cewa kalmomin da suke biye ne ainahin bayanin. (Dubi: writing_background)
yana aiki
Wannan ya na nufin yin aiki, tare da ko wane abu da ake yi don a bauta wa mutane.
su Yahudawa
A nan "Yahudawa" magana ce da ke wakilcin "shugabanin Yahudawa." AT: "shugabanin Yahudawa" (Dubi: figs_synecdoche)
maida kansa dai-dai da Allah
"cewa shi kamar Allah ne" ko kuma "cewa ya na da yawan iko kamar Allah"
Ubanna
Wannan muhimmin lakabi ne wa Allah. (Dubi: guidelines_sonofgodprinciples)
John 5:19-20
Mahaɗin Zance:
Yesu ya cigaba da magana da shugabanin Yahudwa.
Hakika, hakika
Dubi yadda kun fasara wannan a cikin 1:51
za ku yi mamaki
"za ku gigice"
Ɗan ba ya yin kome shi kadai, sai abin da ya ga Uba yana yi. Domin Uban na kaunar Ɗan
Yesu, Ɗan Allah, ya bi shugabancin Ubansa a duniya, domin Yesu ya san cewa Uban ya na kaunarsa. (Dubi: guidelines_sonofgodprinciples)
Ɗan ... Uban
Wadannan muhimmin lakabi ne wadda ya ke kwatanta dangantaka sakanin Yesu da Allah. (Dubi: guidelines_sonofgodprinciples)
kaunar
Irin kauna da ya ke zuwa daga Allah ya na duba kirkin wadansu, ko a loƙacin da bai amfane ku ba. Allah da kansa kauna ne kuma shi ne tushen kauna.
John 5:21-23
Uba ... Ɗan
Wadannan muhimmin lakabi ne wadda ya ke kwatanta dangantaka sakanin Yesu da Allah. (Dubi: guidelines_sonofgodprinciples)
rai
Wannan ya na nufin "rai na ruhaniya."
Gama Uban ba ya hukunta kowa, sai dai ya damka dukan hukunci ga Ɗan
Kalmar "gama" ya na nuna kwatanci. Ɗan Allah ya na yin hukunci wa Allah Uba. (Dubi: guidelines_sonofgodprinciples)
girmama Ɗan, kamar yadda ... Uban. Shi wanda ba ya girmama Ɗan, ba ya girmama Uban da ya aiko shi.
Dole a girmama a kuma yabe Allah Ɗa kamar Allah Uba. Idan mun kasa girmama Allah Ɗa, to mun kuma kasa girmama Allah Uba. (Dubi: guidelines_sonofgodprinciples)
John 5:24
shi mai jin Maganata
A nan "magana" zance ne da ke wakilcin sakon Yesu. AT: "duk wanda ya ji sako na" (Dubi: figs_metonymy)
ba zai halaka ba
AT: "za a sharanta shi ya zama da gaskiya" (Dubi: figs_doublenegatives)
John 5:25
matattatu za su ji muryar Ɗan Allah, wadanda suka ji kuwa za su rayu
Muryar Yesu, Ɗan Allah, zai ta da matattatu daga kabari. (Dubi: guidelines_sonofgodprinciples)
Ɗan Allah
Wannan muhimmin lakabi ne wa Allah. (Dubi: guidelines_sonofgodprinciples)
John 5:26-27
Kammar yada Uba ya ke da rai a cikinsa, haka ya ba Dan don ya zama da rai cikin kansa
Kalmar "gama" ya na nuna kwatanci. Ɗan Allah ya na da ikon ba da rai, kamar yadda Uban yake. (Dubi: guidelines_sonofgodprinciples)
Uban ... Ɗan Mutum
Wadannan muhimmin lakabi ne wadda ya ke kwatanta dangantaka sakanin Yesu da Allah. (Dubi: guidelines_sonofgodprinciples)
Uban ya kuma ba Dan ikon zartar da hukunci
Ɗan Allah ya na da ikon Allah Uba don ya yi hukunci.
John 5:28-29
Kada ku yi mamakin wannan
"Wannan" ya nufin cewa Yesu, Ɗan Mutum, ya na da ikon ba da rai na har abada da kuma yin hukunci.
ji muryarsa
"ji murya na"
John 5:30-32
nufin wanda ya aiko ni
Kalmar "shi" ya na nufin Allah Uba.
Akwai wani wanda ya ke bada shaida game da ni
Akwai wani kuma wanda ya na gaya wa mutane game da ni"
wani
Wannan ya na nufin Allah.
shaidar da yake bayarwa game da ni gaskiya ce
"abin da ya ke gaya wa mutane game da ni gaskiya ne"
John 5:33-35
shaidar da na karba bata mutum
"ba na son shaidar mutum"
domin ku sami ceto
AT: "don Allah ya cece ku" (Dubi: figs_activepassive)
Yahaya fitila ne mai ci, mai haske ne kuma, kun yarda ku yi farinciki da haskensa dan lokaci kadan
A nan "fitila" da "haske" zance ne. Yahaya ya koya wa mutanin game da Allah kuma wannan ya na nan kamar fitilar da yake haskaka haskensa a cikin duhu. AT: "Yahaya ya koya maku game da Allah kuma wannan ya na nan kamar fitila da ya ke haskaka haskensa. Abin da Yahaya ya ce a dan loƙaci kadan ne ya sa ku murna" (Dubi: figs_metaphor)
John 5:36-38
ayyukan da Uba ya bani ni in yi ... cewa, Uba ne ya aiko ni
Allah Uba ya aiko Allah Ɗan, Yesu, a duniya. Yesu ya cika abin da Uban ya ba shi ya yi.
Uba wanda ya aiko ni, shi da kansa ya shaide ni
Kalmar "kansa" ya na bayyana cewa Uban ne, ba wani ne da kankancin muhimmi ne wadda ya shaida ba. (Dubi: figs_rpronouns)
Uba
Wannan muhimmin lakabi ne wa Allah. (Dubi: guidelines_sonofgodprinciples)
Maganarsa kuwa ba ta zaune a cikinku, domin baku gaskanta da wanda ya aiko ni ba
" baku gaskanta da wanda ya aiko ni ba. Haka ne na san cewa ba ku da maganarsa a cikinku"
Maganarsa kuwa ba ta zaune a cikinku
Yesu ya yi magana game da yadda mutane suke rayuwa bisa maganar Allah kamar gidaje da kuma maganar Allah kamar mutum da ya ke zama a cikin gidaje. AT: "Ba ku rayuwa bisa maganarsa" ko kuma "ba ku biyayya da maganarsa" (Dubi: figs-metaphor)
Maganarsa
"sakon da ya gaya maku"
John 5:39-40
a cikinsu za ku sami rai madawwami
"za ku samu rai madawwami idan kun karantasu" ko kuma "littafi zai gaya ma ku yadda za ku samu rai madawwami"
baku yi niyyar zuwa wurina ba
"kun ki ku gaskanta da sako na"
John 5:41-42
karbar
amsa
baku da kaunar Allah a zuciyarku
AT: 1) "ba ku kaunar Allah" ko kuma 2) "ba ku karbi kaunar Allah ba."
John 5:43-44
cikin sunan Ubana
A nan kalmar "suna" magana ne da ke nuna ikon Allah. AT: "Na zo da ikon Ubana" (Dubi: figs_metonymy)
Idan wani ya zo da sunan kansa
Kalmar "suna" magana ne da ke wakilcin iko. AT: "idan wani ya zo a ikonsa" (Dubi: figs_metonymy)
Ta yaya za ku ba da gaskiya, ku da kuke karban yabo ... Allah?
Wannan magana ya bayyana a matsayin tambaya domin karin nanaci. AT: "Ba yanda za ku gaskanta domin kun karbi yabo ... Allah!" (Dubi: figs_rquestion)
gaskanta
Wannan ya na nufin gaskanta da Yesu.
John 5:45-47
Mai zargin ku shine Musa, wanda kuka sa begenku
"Musa" a nan magana ne na doka da kansa. AT: "Musa ya yi zargin ku a cikin doka, doka da kun sa begenku" (Dubi: figs_metonymy)
begenku
"amincewar ku" ko kuma "gaskantawar ku"
Idan kuwa ba ku gaskata abin da ya rubuta ba, ta yaya za ku gaskata maganata?"
Wannan magana ya bayyana a matsayin tambaya domin karin nanata. AT: "ba ku gaskanta da rubutun shi ba, don haka ba za ku taba gaskanta da maganganuta ba!" (Dubi: figs_rquestion)
maganata
"abin da na faɗa"
John 6
John 6:1-3
Muhimmin Bayani:
Yesu ya yi tafiya daga Urushalima zuwa Galili. Taru suka bi shi zuwa saman dutse. Waddannan Aya suna faɗan shirin wannan sashin labarin. (Dubi: writing_background)
Bayan waddannan abubuwa
Jumlan "waddannan abubuwa" ya na nufin abubuwan da ya faru a cikin 5:1-46 ya kuma gabatar da abin da zai faru a gaba.
Yesu ya ketare
Ya nuna a cikin littafin cewa Yesu ya yi tafiya a kwalekwale ya kuma dauki al'majiransa tare da shi. AT: "Yesu ya yi tafiya da al'majirinsa a kwalekwale" (Dubi: figs_explicit)
taro mai yawa
"mutane da yawa"
alamu
Wannan ya na nufin abubuwan al'ajibi da an yi amfani a matsayin shaida cewa Allah ne mai iko wadda ya ke da cikakken iko a komai.
John 6:4-6
Yanzu da idin Ketarewa, wato idin Yahudawa, ya kusato
Yahaya ya daina faɗa wa mutane game da abin da zai faru a labarin domin ya ba da tushin bayani game da loƙacin da abin ya faru. (Dubi: writing_background)
Amma Yesu ya fadi haka ne domin ya gwada Filibus, saboda shi kansa ya san abin da zai yi
Yahaya ya daina faɗa wa mutane game da abin da zai faru a labarin domin ya bayyana dalilin da Yesu ya tambaye Filibus wurin da za a saya burodi. (Dubi: writing_background)
saboda shi kansa ya san
Kalmar "kansa" ya bayyana cewa kalmar "shi" ya na nufin Yesu. Yesu ya san abin da zai yi. (Dubi: figs_rpronouns)
John 6:7-9
gurasar dinari biyu
Kalmar "dinari" da ya ne da "su dinari." AT: "kuɗin burodi da ya kai kuɗin aikin kuanaki dari" (Dubi: translate_bmoney)
dunƙule biyar na sha'ir
"dunƙule biyar na sha'ir." Sha'ir sananne abinci ne.
dunƙule
Ana gasa dunƙulan burodi da ya na da siffa. Mai yiwuwa kananan mulmulallen dunƙule ne.
menene wadannan a mutane masu yawa?
Wannan magana ya bayyana kamar tambaya ne domin ya nanata cewa ba su da abinci da za su ciyad da kowa. AT: "wadannan dunƙule da kifi ba za su isa a ciyad da mutane dayawa ba!" (Dubi: figs_rquestion)
John 6:10-12
zauna
"kwanta"
Yanzu, wurin kuwa akwai ciyawa
Yahaya ya daina faɗa wa mutane game da abin da zai faru a labarin domin ya ba da tushen bayani game da wurin da abin ya faru. (Dubi: writing_background)
Sai mazajen suka zauna, sun kai wajen dubu biyar
Bayan mai yiwuwa taron ta shafi mata da 'ya'ya 6:4-5, Yahaya ya na kirga mazaje na kadai anan.
yi godiya
Yesu ya yi addu'a wa Allah Uba, ya kuma gode masa da kifi da kuma su dunƙule.
ya ba da shi
a nan "ya" yana wakilcin "Yesu da al'majiransa." AT: "Yesu da al'majiransa su ka ba da shi" (Dubi: figs_synecdoche)
John 6:13-15
suka taru
"al'majiran sun tara"
wanda ya rage
abincin da ba wadda ya taba ci
wannan alama
Ciyad da mutane dubu biyar da dunƙule da kuma kifi biyu da Yesu ya yi
annabin
annabin na musamman da Musa ya ce zai zo cikin duniya.
John 6:16-18
Mahaɗin Zance:
Wannan ne abu na biye a cikin labarin. Al'majiran Yesu sun fita zuwa rafi a cikin kwalekwale.
A lokacin duhu ya yi, Yesu kuwa bai riga ya iso wurinsu ba tukuna
Yi amfani da yadda harshenku ya na nuna cewa wannan ne tushen bayani. (Dubi: writing_background)
John 6:19-21
suka yi tuki
Kwalekwale ya na yawan kasance da mutane biyu, hudu, ko shida da suke tuki da matuki a kowane gefe. Al'adunku na iya samu hanya dabam na sa kwalekwale ya haye ruwa.
wajen kimanin mil ashirin da biyar ko talatin
"filin wasanni" na da tsawo 185. AT: "wajen mita biyar ko shida" (Dubi: translate_bdistance)
kada ku firgita
"daina jin tsoro!"
suka yarda suka karbe shi a cikin kwalekwale
Wannan ya na nufin cewa Yesu ya shiga cikin kwalekwale. AT: "sun karbe shi zuwa cikin kwalekwale da farinciki" (Dubi: figs_explicit)
John 6:22-25
tekun
"Tekun Galili"
Koda haka, akwai wadansu ... Ubangiji ya yi godiya
Yi amfani da yadda harshen ku ya ke nuna cewa wannan ne tushen bayani. (Dubi: writing_background)
jirage da suka zo daga Tibariya
A nan, Yahaya ya kara ba da tushen bayani. Washegari, bayan Yesu ya ciyad da mutane, wadansu jirage da mutane daga Tibariya sun zo su ga Yesu. Ko da shike, Yesu da al'majiransa sun tafi a cikin daren. (Dubi: writing_background)
John 6:26-29
Hakika, hakika
Dubi yadda an fasara wannan a cikin 1:51.
rai madawwami wanda Dan Mutum zai ba ku, don Allah Uba ya sa hatiminsa a kansa
Allah Uba ya ba da izini wa Yesu, Ɗan Mutum, don ya ba da rai madawwami ga wanda sun gaskanta da shi.
Ɗan Mutum ... Allah Uba
Waddannan muhimmin laƙani ne da ya ke kwatanta dangantaka a sakanin Yesu da Allah. (Dubi: guidelines_sonofgodprinciples)
ya sa hatiminsa a kansa
"sa hatimi" a abu ya nufin saka alama don ya nuna mai shi. Wannan ya na nufin cewa Ɗan na Uban ne kuma Uban ya yarda da shi a komai.(Dubi: figs_metaphor)
John 6:30-31
Ubanninmu
"Kakanninmu"
sama
Wannan ya na nufin wurin da Allah ya ke.
John 6:32-34
Ubana ne ya baku gurasa ta gaskiya daga sama
" gurasa ta gaskiya" magana ce game da Yesu. AT: "Uban ya na ba ku Ɗan a matsayin gurasa ta gaskiya daga sama" (Dubi: figs_metaphor and guidelines_sonofgodprinciples)
Uba na
Wannan muhimmin laƙani ne wa Allah. (Dubi: guidelines_sonofgodprinciples)
ba da rai ga duniya
"ba da rai na ruhaniya ga duniya"
duniyan
A nan "duniya" magana ne na dukkan mutane da suke gaskanta da Yesu. (Dubi: figs_metonymy)
John 6:35-37
Ni ne gurasan rai
Yesu ya kwatanta kansa da gurasa ta wurin gurasan. Kamar yadda gurasa ya na da amfani a rayuwa, Yesu ya na da amfani don rai na ruhaniyar mu. AT: "Kamar yadda abinci yake sa ku rayu, Zan iya ba ku rai ta ruhaniya" (Dubi: figs_metaphor)
gaskanta da
Wannan ya na nufin gaskanta cewa Yesu ne Ɗan Allah, yarda da cewa shi ne mai ceto, da kuma yi rayuwa a hanyar da zai girmama shi.
Duk wanda Uba ya bani zai zo gare ni
Allah Uba da kuma Allah Ɗa zai cece wadda sun gaskanta da shi har abada. (Dubi: guidelines_sonofgodprinciples)
Uba
Wannan muhimmin laƙani ne wa Allah. (Dubi: guidelines_sonofgodprinciples)
wanda kuwa ya zo gare ni ba zan kore shi ba
Wannan Jumla ya bayyana abin da ba shi ne yake nufi ba domin nanaci. AT: "Zan ajiye duk wanda ya zo wuri na" (Dubi: figs_litotes)
John 6:38-40
shi wanda ia aike ni
"Uba na, wadda ya aiko ni"
ba zan rasa ko daya daga cikin wadannan
An yi amfani da karin magana domin a bayyana cewa Yesu zai ajiye duk wadda Allah ya ba shi. AT: "In ajiye dukkansu" (Dubi: figs_litotes)
zan tashe su
A nan tashi karin magana ne na sa mutumin da ya mutu ya kuma rayu kuma. AT: "zan sa su su rayu kuma" (Dubi: figs_idiom)
John 6:41-42
gunaguni
yi magana da rashin farinciki
Nine Gurasar
Kamar yadda gurasa na da amfani a rain mu, haka ne Yesu ya na da amfanai a rai na ruhaniyarmu. Dubi yadda an fasara wannan a cikin 6:35. AT: "Ni ne wadda yake kamar gurasan gaskiya" (Dubi: figs_metaphor)
Ba wannan ne Yesu ... wanda Ubansa da Uwarsa mun san su ba?
Wannan magana ya bayyana kamar tambaya ne domin ya bayana cewa shugabanin Yahudawa ba su yarda cewa Yesu dabam ba ne ba. AT: "Wannan Yesu ne, dan Yusuf, wadda Ubansa da Uwarsa mun sani! (Dubi: figs_rquestion)
Ta yaya yanzu zai ce, 'Na ya sauko daga sama'?
Wannan magana ya bayyana kamar tambaya ne domin ya bayana cewa shugabanin Yahudawa ba su yarda cewa Yesu ya zo daga sama ba. AT: "Ya na karya ne a lokacin da ya ce ya zo daga sama!" (Dubi: figs_rquestion)
John 6:43-45
tashe shi
Wannan karin magana ne. AT: "sa shi ya rayu kuma" (Dubi: figs_idiom)
jawo
AT: 1) "ja 2) "jawo hankali."
A rubuce yake cikin litattafan anabawa
AT: "annabawan sun rubuta" (Dubi: figs_activepassive)
Duk wanda ya ji ya kuma koya daga wurin Uba, ya kan zo gare ni
Yahudawa su na zato cewa Yesu "dan Yusuf ne" (See: John 6:42, amma shi ne Ɗan Allah saboda Uban shi ne Allah, ba Yusuf ba. Waddanda sun koya daga Allah Uba sun gaskanta da Yesu, wadda shi ne Allah Ɗa.
John 6:46-47
Ba cewa wani ya taba ganin Uban ba, sai shi wanda yake daga wurin Allah
Ko da shike ba bu mutum da ke raye a duniya da ya ga Allah Uba, Yesu, Ɗan Allah, ya gan Uban.
wanda ya bada gaskiya, yana da rai Madawwami
Allah ya na ba da "rai Madawwami" ga wadda sun gaskanta da Yesu, Ɗan Allah.
John 6:48-49
Ubanninku
"Kakanninku"
mutu
Wannan ya na nufin asalin mutuwa.
John 6:50-51
Wannan ne gurasan
A nan "gurasa" magana ne da ya ke nuna Yesu wadda shi ne mai ba da rai na ruhaniya kamar yadda gurasa ya na rike rai. AT: "Ina nan kamar gurasar gaskiya" (Dubi: figs_metaphor)
ba zai mutu ba
"rayu har abada." A nan kalmar "mutu"ya na nufin mutuwa ta ruhaniya.
gurasa mai rai
Wannan ya na nufin "gurasa da ya ke sa mutane su rayu" (John 6:35).
don ceton duniya
A nan "duniya" magana ne da ke wakilcin rayuwar dukkan mutane a cikin duniya. AT: "cewa zai ba da rai ga dukkan mutane a cikin duniya" (Dubi: figs_metonymy)
John 6:52-53
Yaya mutumin nan zai iya bamu naman jikinsa mu ci?
Wannan magana ya bayyana kamar tambaya ne domin ya bayyana cewa shugabanin Yahudawa ba su yarda da abin da Yesu ya ce game da "namansa" ba. AT: "Ba bu yadda wannan mutum zai ba mu namansa mu ci!" (Dubi: figs_rquestion)
ci naman jikin Ɗan mutum, da kuma sha jininsa
A nan su jumlolin "ci nama" da " sha jinina" karin magana ne da ya ke nuna yadda gaskanta da Yesu, Ɗan Mutum, yake kamar karban abinci da ruwa na ruhaniya. AT: "karɓa Ɗan Mutum kamar yadda ku na karban abinci da ruwa" (Dubi: figs_metaphor)
ba za ku sami rai a cikin ku ba
"ba za ku karbi rai na har abada ba"
John 6:54-56
Dukan wanda ya ci nama na ya kuma sha jinina yana da rai Madawwami
Su jumlan "ci nama" da " sha jinina" karin magana ne. Kamar yadda wani ya na son abinci da ruwa domin ya samu rai, waddanda sun gaskanta da Yesu za su samu rai na ruhaniya. AT: "Duk wanda ya gaskanta da ni don abincin ruhaniyarsu da kuma ruwa za su samu rai na har abada" (Dubi: figs_metaphor)
a ranar karshe
"a ranar da Allah zai hukunta kowa"
namana abinci ne na gaske ... jinina kuma abin sha ne na gaskiya
Kalmomin "abinci ne na gaske" da kuma "sha ne na gaskiya" maganganu ne da yake nufin cewa Yesu ya tanada abincin ruhaniya da ruwan sha wa waddanda sun gaskanta da shi. Karban Yesu a bangaskiya ya na tanada rai na har abada kamar yadda abinci da ruwan sha ya ke amfana jiki. AT: "Ni ce abincin ruhaniya ta gaskiya da kuma ruwan sha" (Dubi: figs_metaphor)
zamne a ciki na, ni kuma a cikinsa
"na da dangantaka na kusa da ni"
John 6:57-59
sabo da haka wanda ya ci namana
"wadda ya gaskanta da ni"
rayayyen Uba
AT: 1) "Uban da yake ba da rai" ko kuma 2) "Uban da yake rayayye."
Wannan itace gurasar da ta sauko daga sama
"Gurasan" misali ne wa Yesu, wadda ya zo daga sama. AT: "Ina nan kamar gurasa da ya zo daga sama" (Dubi: figs_metaphor)
Dukan wanda ya ci wannan gurasa
Wannan zance ce. Wadda sun yarda da Yesu domin rai na ruhaniyarsu suna nan kamar wadda suke dogara a kan gurasa ko abinci don rayuwarsu. AT: "Duk wadda ya yarda da ni"(Dubi: figs_metaphor)
Ubannin
"kakanin"
Yesu ya fadi wadan nan abubuwa a cikin majami'a ... a Kafarnahum
A nan Yahaya ya ba da tushen bayani game da loƙacin da abin ya faru. (Dubi: writing_background)
John 6:60-61
wa zai iya jinta?
Wannan magana ya bayyana a matsayin tambaya domin ya bayana cewa al'majiran sun sha wuyan fahimtar abin da Yesu ya faɗa. AT: "ba bu wadda zai karbe shi!" ko kuma "ya na da wuyan ganewa!" (Dubi: figs_rquestion)
Wannan ya zamar maku laifi?
"Wannan ya ba ku mamaki?" ko kuma "Wannan ya dame ku?"
John 6:62-63
Yaya Ke nan in kun ga Ɗan Mutum yana hawa inda yake a da?
Yesu ya ba da wannan magana a matsayin tambaya domin ya bayyana cewa al'majiransa za su ga wadansu abubuwa da suke da wuyan fahimta. AT: "Sai ba za ku san abin da za ku yi tunani ba a loƙacin da kun gan ni, Ɗan Mutum, hawa cikin sama!" (Dubi: figs_rquestion)
amfana
Kalmar "amfana" ya na nufin sa abubuwa masu kyau su faru.
Kalmomin
AT: 1)kalmomin Yesu a cikin 6:32-58 ko kuma 2) komai da Yesu ya koyar. (Dubi: figs_metonymy)
Kalmomin da na fada maku
"Abin da na faɗa maku"
ruhu ne, da kuma rai ne
AT:1) "na game da Ruhu da kuma rai na har abada" ko kuma 2) "na daga Ruhu kuma su na ba da rai" ko kuma 3) "na game da abubuwan ruhaniya da rai."
John 6:64-65
Domin tun farko Yesu ya san wadanda ... wanda zai bashe shi
A nan Yahaya ya ba da tushen bayani game da abin da Yesu ya san zai faru. (Dubi: writing_background)
ba mai iya zuwa wurina, sai ta wurin Uban
Dole ne duk wadda yake so ya gaskanta ya zo wurin Allah ta Ɗan. Allah Uba ne kadai ya na yarda mutane su zo wurin Yesu.
zuwa wurina
"bi ni ku kuma karbi rai na har abada"
John 6:66-69
Muhimmin Bayani:
Muhimmin Bayani:
kara tafiya tare da shi ba
Yesu ya tafi wurare da kafa, gaskiya ne cewa ba su yi tafiya a wurin da ya tafiya ba, amma mai sauraran ya gane cewa wannan magana ya na nuna cewa bai so a ji abin ya ke so ya faɗa ba. (Dubi: figs-metaphor)
Ubangiji, gun wa za mu je?
Siman Bitrus ya ba da wannan magana a matsayin tambaya domin ya bayyana cewa ya na so ya bi Yesu kadai. AT: "Ubangiji, ba za mu iya bin wanna ba sai kai!" (Dubi: figs_rquestion)
Al'majiransa
A nan "al'majiransa" ya na nufin muhimmin kungiyar mutane da sun bi Yesu.
sha biyun
Wannan bayani ne na "al'majira sha biyun," takamaiman mutane sha biyu da sun bi Yesu don hidimarsa. "al'majira sha biyun" (Dubi: figs_ellipsis)
John 6:70-71
Ba ni na zabe ku, goma sha biyu ba, amma dayanku Iblis ne?
Yesu ya ba da wannan magana a matsayin tambaya domin ya jawo hankali ga cewa daya daga cikin al'majiransa zai bashe shi. AT: "Na zabe ku da kaina, da haka wani a cikinku bawan shaidan nen!" (Dubi: figs_rquestion)
John 7
John 7:1-2
Muhimmin Bayani:
Yesu ya na magana wa 'yan'uwansa a cikin Galili. Waddannan sura su na magana game da loƙacin da abin ya faru. (Dubi: writing_background)
Bayan wadannan abubuwa
Waddannan kalmomin ya gaya wa mai sauraran cewa marubucin zai fara magana game da sabon abu. "Bayan ya gama magana da al'majiransa" (See: John 6:66-71) ko kuma "da saran loƙaci"
zagaya
Ya kamata mai saurara ya gane cewa mai yiwuwa Yesu ya yi tafiya ne ba kuwa ya hawo mota ko dabba ba.
Yahudawa suna nema su kashe shi
A nan "Yahudawa" magana ne na "shugabanin Yahudawa." AT: "shugabanin Yahudawa su na shirin su kashe shi" (Dubi: figs_synecdoche)
Yanzu Idin Bukkoki na Yahudawa ya kusa
"Yanzu loƙacin idin Yahudawa ya yi kusa"
John 7:3-4
'yan'uwan
Wannan ya na nufin ainahin kananan 'yan'uwanin Yesu, 'ya'yan Maryamu da Yusuf.
ayyukan da kake yi
Kalmar "ayyuka" ya na nufin abin mamaki da Yesu ya yi.
shi kansa
Kalmar " kansa" magana ne da ke bayyana kalmar "shi." (Dubi: figs_rpronouns)
duniyan
A nan "duniya" magana ne game da dukkan mutane a cikin duniya. AT: "dukkan mutane" ko "kowane mutum" (Dubi: figs_metonymy)
John 7:5-7
Domin ko 'yan'uwansa ma basu bada gaskiya gare shi ba
Wannan maganan fashi ne daga ainahin labarin kamar yadda Yahaya ya gaya mana tushen bayanin game da 'yan'uwan Yesu. (Dubi: writing_background)
'yan'uwansa
"kananun 'yan'uwansa"
loƙaci na bai yi ba tukuna
Kalmar "loƙaci" karin magana ne. Yesu ya na nufin cewa loƙaci bai kai da zai gama hidimarsa ba. AT: " loƙaci bai kai da zan daina aiki na ba" (Dubi: figs_metonymy and figs_explicit)
ku koyaushe loƙacin ku ne
"kowane loƙaci ya na da kyau maku"
Duniya baza ta iya kin ku ba
A nan "duniya" magana ne game da mutane da suke cikin duniya. AT: "Dukka mutane a duniya ba za su iya ki ka ba" (Dubi: figs_metonymy)
ina faɗin cewa ayyukanta ba su da kyau
"ina faɗa masu cewa abin da suke yi ba bu kyau"
John 7:8-9
Mahaɗin Zance:
Yesu ya cigaba da magana da 'yan'uwansa.
lokacina bai yi ba tukuna
A nan Yesu ya na nufin cewa idan ya tafi Urushalima, zai kawo aikinsa ga karshe. AT: "loƙaci na bai kai tukuna da zan tafi Urushalima ba"(Dubi: figs_explicit)
John 7:10-11
a loƙa da 'yan'uwansa su ka tafi wurin idin
'Yan'uwannan ne kannen Yesu.
ya tafi
Urushalima ya na tudu fiye da Galili, wurin da Yesu da 'yan'uwansa suke adda.
a asirce ba a fili ba
Waddannan jumla su na nufin abu daya. Ana sake nanata maganan domin bayani. AT: "ɓoyeyye sosai" (Dubi: figs_doublet)
Yahudawa suna neman sa
A nan kalmar "Yahudawa" karin magana ne na "shugabanin Yahudawa." kalmar "sa" ya na nufin Yesu. AT: "Shugabanin Yahudawa suna neman Yesu" (Dubi: figs_synecdoche)
John 7:12-13
tsoro
Wannan ya na nufin rashin dadi da mutum ya ke da shi a loƙacin da akwai kurarin lahani a kansa ko kuma wasu.
Yahudawa
Kalmar "Yahudawa" magana ne na shugabanin Yahudawa da suke hamayya da Yesu. AT: "shugabanin Yahudawa" (Dubi: figs_synecdoche)
yana karkatar da hankalin jama'a
A nan "karkatar" na nufin a rinjaye mutum ya gaskata da abinda ba gaskiya bane. AT: "ya rinjaye mutanin" (Dubi: figs_metaphor)
John 7:14-16
Yaya aka yi wannan mutum ya sami ilimi dayawa haka?
Wannan magana ya bayyana kamar tambaya ne domin ya bayana mamakin da shugabanin Yahudawa sun yi akan cewa Yesu ya na da sani sosai (Dubi: figs_rquestion).
amma ta wanda ya aiko ni ce
"amma ya na zuwa daga Allah, wanda ya aiko ni"
John 7:17-18
amma ko wanene ya nemi darajar wanda ya aiko ni, wannan mutum mai gaskiya ne, babu rashin adalci a cikin sa
"loƙacin da mutum ya na so ya girmama wadda ya aiko shi kadai, mutumin ya na faɗan gaskiya ne. Ba ya karya"
John 7:19-20
Ba Musa ya baku doka ba?
Wannan magana ya bayyana kamar tambaya ne domin ya kara bayani. AT: "Musa ne ya ba ku dokan" (Dubi: figs_rquestion)
Amma duk da haka ba mai aikata dokokin
"bi doka"
Me yasa ku ke so ku kashe ni?
Yesu ya daidaita muradin shugabanin Yahudawa da suke so su kashe shi domin ya karye dokan Musa. Ya na nufin cewa shugabanin da kansu ba su bin dokan. AT: "Ku na karye dokan da kanku kuma ku na so ku kashe ni!" (Dubi: figs_rquestion and figs_explicit)
Ka na da aljani
"Wannan ya nuna cewa kai mahaukaci ne, ko kuma aljani ya na mulki da kai!"
Wanene yake so ya kashe ka?
Wannan magana ya bayyana kamar tambaya ne domin ya kara bayani. AT: "ba bu wadda ya ke so ya kashe ka!" (Dubi: figs_rquestion)
John 7:21-22
aiki daya
"abin al'ajibi daya" ko "alama daya"
dukan ku kuna mamaki
"dukkanku kun gigice"
ba kuwa daga Musa take ba amma daga kakannin kakanni ta ke
Yahaya ya kara tanada karin bayani anan game da kaciya. (Dubi: writing_background)
a ranar Asabar kukan yi wa mutum kaciya
Yesu ya na nufin cewa yin kaciya ya na tare da aiki. AT: "kun yi wa ɗa na miji kaciya a ranar Asabar. Wannan ma aiki ce" (Dubi: figs_explicit)
a ranar Asabar
"a ranar hutun Yahudawa"
John 7:23-24
Idan mutum ya karbi kaciya ranar Asabar, domin kada a karya dokar Musa
"Idan kun yi wa ɗa na miji kaciya a ranar Asabar domin kada ku karye dokar Musa"
don me kuka ji haushi na saboda na mai da mutum lafiyayye sarai ranar Asabar?
Wannan magana ya bayyana kamar tambaya ne domin ya kara bayani. AT: "kadda ku yi fushi da ni domin na sa mutum lafiya a ranar Asabar!" (Dubi: figs_rquestion)
Kada ku yi shari'a ta ganin ido, amma ku yi shari'a mai adalci
Yesu ya na nufin cewa kada mutane su zaba abin da ba daidai ba, amma su tsaya akan abin da su na iya gani. A kowane ayuka akwai wani muradi da ba a iya gani. AT: "Daina hukunta mutane bisa abin da ku na iya gani! Ku fi hankali da abin da ke daidai bisa ga Allah" (Dubi: figs_explicit)
John 7:25-27
wannan ba shine wannan da suke nema su kashe ba?
Wannan magana ya bayyana a matsayin tambaya ne domin karin bayani. AT: "Wannan Yesu ne wadda suke nema su kashe shi!" (Dubi: figs_rquestion)
ba wanda ya ce da shi komai
Wannan yana nufin cewa shugabanin Yahudawa basu yin hamaiya da Yesu. AT: "ba su faɗa komai na hamayya da shi ba"(Dubi: figs_explicit)
Ba zai yiwu ba mahukunta su sani cewa wannan Kristi ne, ko ba haka ba?
Wannan magana ya bayyana a matsayin tambaya ne domin karin bayani. AT: "Watakila sun yarda da gaskiye cewa shi ne Mai ceto!" (Dubi: figs_rquestion)
John 7:28-29
yi magana da karfi
"yi magana da murya mai karfi"
a cikin haikali
Yesu da mutanin su na cikin fadan haikali. AT: "a cikin fadan haikali" (Dubi: figs_explicit)
Kun san ni kuma kun san inda na fito
Yahaya ya yi amfani da karin magana a cikin wannan jumla. Mutanin sun gaskanta cewa Yesu daga Nazarat ne. Ba su san cewa Allah ne ya aike shi daga sama ba kuma an haife shi a cikin Baitalami. AT: "Dukkan ku kun san ni kuma ku na tunani cewa kun san wurin da na fito" (Dubi: figs_irony)
na kaina
"akan iko na." Dubi yadda kun fasara "na kansa" a cikin 5:19.
shi wanda ya aiko ni gaskiya ne
"Allah ne wadda ya aiko ni kuma shi gaskiya ne"
John 7:30-32
sa'arsa ba ta yi ba tukuna
Kalmar "sa'ar" magana ne da ya ke wakilcin loƙacin da ya kamata a kama Yesu, bisa shirin Allah. AT: "ba loƙacin da ya kamata su kama shi ba ne" (Dubi: figs_metonymy)
A loƙacin da Almasihu zai zo, zai yi alamu fiye da wadanda wannan mutum ya yi?
Wannan magana ya bayyana a matsayin tambaya ne domin karin bayani. AT: "A loƙacin da Almasihu zai zo, hakika ba zai iya yin alamu fiye da wadda wannan mutumin ya yi ba!" (Dubi: figs_rquestion)
alamu
Wannan ya na nufin abin al'ajibi da ya nuna cewa Yesu ne Almasihu.
John 7:33-34
Ina tare ku na da dan loƙaci kadan
"Zan kasance tare da ku na da dan loƙaci kadan"
sa'annan in tafi wurin wanda ya aiko ni
A nan Yesu ya na nufin Allah Uba, wadda ya aike shi.
inda na tafi, ba za ku iya zuwa ba
"ba za ku iya zuwa wurin da na ke ba"
John 7:35-36
Yahudawa fa su ka cewa junan su
"Yahudawa" karin magana ne da ke wakilcin shugabanin Yahudawa da suka yi hamayya da Yesu. AT: "shugabanin Yahudawa sun faɗa a sakaninsu" (Dubi: figs_synecdoche)
Helinawa
Wannan ya na nufin Yahudawa da aka baza su a duniyar Greek, a wujen Falistiyawa.
Wace kalma ya ke fadi haka
Wannan "kalma" magana ne da ya ke nufin sakon da Yesu ya bayar, wadda shugabanin Yahudawa sun kasa ganewa. AT: "Me ne ya na magana a kai a loƙacin da ya ce"
John 7:37-38
babbar rana ta idin
"babba" ce domin shi ne karshe, ko kuma muhimmin, ranar idi.
Idan kowa yana jin kishi
A nan kalmar "shi" magana ne da yake nufin yawan son abubuwan Allah, kamar yadda mutum yake "kishi" ruwa. AT: "Waddanda su ke son abubuwan Allah kamar yadda mutum mai kishi yake son ruwa" (Dubi: figs_metaphor)
ya zo wuri na ya sha
Kalmar "sha" magana ne da yake nufin karban rai na ruhaniya da Yesu ya tanada. AT: "Ya zo wuri na don ya kashi ƙishirwa ta ruhaniya" (Dubi: figs_metaphor)
Shi wanda ya bada gaskiya gare ni kamar yadda littafi ya fadi
"kamar yadda littafi ya faɗi game da kowane mutum da ya gaskanta da shi"
rafukan ruwa na rai za su bulbulo
"rafukan ruwa na rai za su bulbulo" magana da yake wakilcin rai da Yesu ya tanada wa waddanda suke "ƙishirwa" ta ruhaniya. AT: "rai na ruhaniya zai bulbulo kamar rafukan ruwa" (Dubi: figs_metaphor)
ruwa na rai
AT: 1) "ruwa da yake ba da rai" ko kuma 2) "ruwa da ya na sa mutane su rayu." (Dubi: figs_metaphor)
daga cikin sa
A nan ciki ya na wakilcin cikin mutum, musamman sashen mutum da ba ya bayyane. AT: "daga cikin shi" ko kuma " daga zuciyarsa" (Dubi: figs_metonymy)
John 7:39
Amma ya
A nan "ya" ya na nufin Yesu.
ba a ba da Ruhun ba tukuna
Yahaya ya na nufin cewa Ruhu zai zo daga baya don ya yi rayuwa a cikin wanda sun gaskanta da Yesu. AT: "Ruhu bai riga ya zo don ya yi rayuwa a cikin masubi ba" (Dubi: figs_explicit)
saboda ba a rigaya an daukaka Yesu ba
A nan kalmar " daukaka" ya na nufin loƙacin da Allah zai girmama Ɗan bayan mutuwarsa da tashinsa.
John 7:40-42
Wannan lallai annabi ne
Da faɗan wannan, mutanin su na nuna cewa sun gaskanta cewa Yesu ne annabi kamar Musa da Allah ya yi alkawari zai aiko. AT: "Wannan lallai annabi ne wadda yake kamar Musa da muke ta jira" (Dubi: figs_explicit)
Almasihu zai fito daga Gallili ne?
Wannan magana ya bayyana a matsayin tambaya ne domin karin bayani. AT: "Almasihun ba zai iya zuwa daga Galili ba!" (Dubi: figs_rquestion)
Ba nassi ya ce Almasihu zai fito daga cikin dangin Dauda daga Baitalami ba, daga kauyen da Dauda ya fito?
Wannan magana ya bayyana a matsayin tambaya ne domin karin bayani. AT: "Littafi ya koya cewa Almasihu zai zo daga layin Dauda kuma daga Baitalami, daga kauyen da Dauda ya fito!" (Dubi: figs_rquestion)
Ba littafi ya ce
Ana maganar littafi kamar su na iya magana yadda mutum ya na magana. AT: "Annabawa sun rubuta a cikin littafi" (Dubi: figs_personification)
Inda Dauda fito
"inda Dauda ya yi rayuwa"
John 7:43-44
Sai aka sami rabuwa a cikin taron saboda shi
Taron ba su iya yarda da menene ko wanene Yesu ba.
amma ba wanda ya sa masa hannu
Sa hanu a akan mutum karin magana ne da ke nufin a kama shi ko kuma jingina akan wani abu. AT: "amma ba bu wadda ya ƙwace shi don a kama shi" (Dubi: figs_idiom)
John 7:45-46
Jami'an
"masu tsaron haikali"
Ba mutumin da ya taba yin magana kamar haka
Yan Jami'an sun zuguiguita domin su nuna farincikinsu ga abin da Yesu ya ce. Za ku iys sa a bayyane cewa Jami'an ba su ce sun san komai da kowane mutum a dukkan loƙaci da wurare sun taba faɗa ba. "Ba mu taba gin wani ya fada irin wannan abin ban mamaki kamar wannan mutum ba!" (Dubi: figs_explicit and figs_hyperbole)
John 7:47-49
Don haka Farisawa
"Domin sun faɗa cewa, Farisawa"
amsa masu
"amsa Jami'an"
an karkatar da ku?
Wannan magana ya bayyana a matsayin tambaya ne domin karin bayani. Farisawa sun yi mamakin amsan Jami'an. AT: "An karkatar da ku ma!" (Dubi: figs_rquestion)
Ko wani daga cikin mahukunta ya bada gaskiya gare shi, ko kuwa daga cikin Farisawa?
Wannan magana ya bayyana a matsayin tambaya ne domin karin bayani. AT: "Ba bu wani daga mahukunta ko Farisawa da sun gaskanta da shi!" (Dubi: figs_rquestion)
doka
Wannan daga dokan Farisawa ne ba dokar Musa ba.
Amma wannan taro da basu san doka ba, la'anannu ne
"Ga wannan taro da basu san doka ba, Allah zai sa su halaka!"
John 7:50-53
daya daga cikin Farisawa, da ya zo wurin Yesu
Yahaya ya ba da wannan bayani domin ya tunashar da mu game da Nikodimus. Harshen ku na iya samun wata hanyar nuna tushen bayani.(Dubi: writing_background)
Shari'armu bata hana hukunta mutum ... abin da ya aikata?
Wannan magana ya bayyana a matsayin tambaya domin karin bayani. AT: "shari'ar mu na Yahudawa bai yarda mana mu hukunta mutum ba ... abin da ya aikata!" (Dubi: figs_rquestion)
Shari'armu ta na hukunta mutum ne
A nan Nikodimus ya yi maganan shari'a kamar mutum ne. Idan wannan ba ya al'adan harshenku, za ku iya fasara ta da wata kalma. AT: "Mu na hukunta mutum" ko "Ba mu hukunta mutum"(Dubi: figs_personification)
kai ma daga Galili ka fito?
shugabanin Yahudawa sun san cewa Nikodimus ba daga Galili ba ne. Sun yi masa wannan tambaya don su yi masa ba'a. AT: "Kai daya daga cikin mutanin baya ne daga Galili!" (Dubi: figs_rquestion and figs_explicit)
Yi bincike ka gani
Wannan karin magana ne. Za ku iya sa bayani da ba bu a nan. AT: "Yi bincike da kyau a kuma yi karantun abin da an rubuta a cikin littatafe" (Dubi: figs_ellipsis)
ba annanbin da zai fito daga Galili
Mai yiwuwa wannan ya na nufin cewa an haife Yesu a cikin Galili.
John 8
John 8:1-3
Mahaɗin Zance:
Sura daya ya faɗa mana inda Yesu ya tafi a karshen Sura da ya rigaya wuce.
Muhimmin Bayani:
Sa'an da waddansu litattafe su ke da 7:53-8:1, litattafe na farko musa kyau ba su sa su ba.
dukka mutanin
Wannan ne ainahin yadda ana magana. Ya na nufin "mutane dayawa."
marubuta da Farisawa suka kawo
A nan jumlan "marubuta da Farisawa" karin magana ne da yake wakilcin waddansu mutanin wannan kungiyoyi biyu. AT: "Waddansu marubuta da Farisawa sun kawo" ko kuma "Waddansu mazaje wadda sun koya wa Yahudawa dokoki da waddansu da suke Farisawa" (Dubi: figs_synecdoche)
mace wadda aka kama ta tana zina
Wannan jumla ce. AT: "macen da su ka samu ta ke yin zina" (Dubi: figs_activepassive)
John 8:4-6
irin wandannan mutane
"mutane irin haka" ko "mutane da suke yin haka"
me ka ce game da ita?
"Don haka kun gaya mana. Me za mu yi game da ita?
don a kama shi
Wannan ya na nufin yin amfani da wata tambaya.
domin su iya sami abinda za su zarge shi
Ana iya sa abin da za a zarge a bayyane. AT : "domin su iya yin zargin sa da faɗan abin da ba daidai ba" ko kuma "domin su iya zargin sa da rashin bin dokan Musa ko na Romawa" (Dubi: figs_explicit)
John 8:7-8
A loƙacin da su ka cigaba
Kalmar "su" ya na nufin marubuta da Farisawa.
shi wanda ba shi da zunubi a cikin ku
Ana iya bayyana kalmar "zunubi." AT: "shi wanda bai taba yin zunubi a cikin ku ba" ko kuma "Idan wani a cikin ku bai taba yin zunubi ba" (Dubi: figs_abstractnouns)
bari ya
"bari mutumin"
Ya sake sunkuyawa
"ya durkusa"
John 8:9-11
ɗaya bayan ɗaya
"daya bayan daya"
Mace, ina masu zargin ki?
A loƙacin da Yesu ya kira ta "mace," ba wai ya na sun ya sa ta ta ji kamar mara amfani bba ne. Idan mutane a harshenku za su yi tunani cewa ya na yin haka, ana iya fasara ba tare da kalmar "Mace" ba.
John 8:12-13
Ni ne hasken duniya
A nan "haske" misali ne na wahayin da ya ke zuwa daga Allah. AT: "Ni ne wadda na ke ba da haske a duniya" (Dubi: figs_metaphor)
duniya
Wannan magana ne na mutanin. AT: "mutanin duniya" (Dubi: figs_metonymy)
shi wanda ya biyo ni
Wannan karin magana ne da ya ke nufin "kowane mutum da yake yin abin da ke daidai" ko "kowane mutum da ya ke biyayya da ni" (Dubi: figs_idiom)
ba zai yi tafiya cikin duhu ba
Yi "tafiya a cikin duhu" magana ne na yin rayuwan zunubi. AT: "ba zai yi rayuwa kamar ya na cikin duhun zunubi ba" (Dubi: figs_metaphor)
hasken rai
"Hasken rai" magana ne na gaskiya daga Allah wadda yake ba da rai na ruhaniya. AT: "gaskiya da yake kawo rai madawammi" (Dubi: figs_metaphor)
Kana bada shaida a kan ka
"Kana faɗan waddannan abubuwa game da kanka"
shaidarka ba gaskiya ba ce
Farisawa su na nufin cewa shaidar mutum daya kadai ba gaskiya ba ne domin ba za a iya bincikawa ba. AT: "ba za ka iya zama shaidar kanka ba" ko " abin da ka faɗa game da kanka ba zai iya zama gaskiya ba" (Dubi: figs_explicit)
John 8:14-16
Ko ma na bada shaida a kai na
"ko da na faɗa waddannan abubuwa game da ni"
jikin
"ma'aunin mutum da kuma dokokin mutane"
ban yi wa kowa shari'a ba
AT: 1) "ban yi wa kowa shari'a tukuna ba" ko 2) "ba zan yi wa kowa shari'a yanzu ba."
idan na yi shari'a
AT: 1) "idan na yi wa mutane shari'a" ko kuma 2) "duk loƙacin da na yi wa mutane shari'a"
shari'ata gaskiya ce
AT: 1) "shari'ata zai zama daidai" ko "shari'ata daidai ne."
ba ni kadai ba ne, amma ina tare da Uba wanda ya aiko ni
Yesu, Ɗan Allah, ya na da iko domin dangantaka na musamman da Ubansa. (Dubi: guidelines_sonofgodprinciples)
ba ni kadai ba ne
Abin da bayanin ya ke nufi shi ne Yesu ba shi kadai ba ne a shari'an. AT: "ba ni kadai ba ne a yadda na ke yin shari'a" ko "ba na yin shari'a ni kadai" (Dubi: figs_explicit)
ina tare da Uba
Uba da Ɗa su na shari'ata tare. AT: "Uban ya na yin shari'a tare da ni" ko "Uban ya na yin shari'a kamar yadda na ke yi"
Uban
Wannan muhimmin lakabi ne wa Allah. Idan dole ne harshen ku zai faɗa Uban wa ne wannan, za ku iya ce " Uba na"
John 8:17-18
I, a cikin dokarku
"kalmar "I" ya na nuna cewa Yesu ya na kara akan abin da dama ya na faɗa.
an rubuta
Wannan jumla ce. AT: "Musa ya rubuto"(Dubi: figs_activepassive)
shaidar mutum biyu gaskiya ce
hikiman a nan shi ne cewa mutum daya ya na iya duba kalmomin dayan mutumin. AT: "Idan mazaje biyu sun faɗa abu daya, mutane sun san cewa gaskiya ne" (Dubi: figs_explicit)
Ni ne ni ke shaidar kaina
Yesu ya shaida kansa. AT: "Na ba ku alamun kai na"
Uba wanda ya aiko ni ya na shaida ta
Uban kuma ya na shaida akan Yesu. Za ku iya sa a bayyane cewa wannan ya na nufin shaidar Yesu gaskiya ce. AT: "Uba na wadda ya aiko ni ya kuma kawo alamu game da ni. Don haka ku yarda cewa abin da mu na faɗa maku gaskiya ne" (Dubi: figs_explicit)
John 8:19-20
baku san ni ba balle Ubana, in da kun san ni da kun san Uba na kuma.
Yesu ya nuna cewa saninsa, ya na nan kamar sanin Uban ne kuma. Ɗa da Uba Allah ne. "Uba" muhimmin lakami ne wa Allah. (Dubi: guidelines_sonofgodprinciples)
Ubana
Wannan muhimmin lakabi ne wa Allah. (Dubi: guidelines_sonofgodprinciples)
sa'arsa bata yi ba tukuna
Kalmar "sa'a" magana ne na loƙacin da Yesu zai mutu. AT: "loƙaci bai kai da Yesu zai mutu ba"(Dubi: figs_metonymy)
John 8:21-22
mutu cikin zunubinku
A nan kalmar "mutu" ya na nufin mutuwa ta ruhaniya. AT: "mutu a loƙacin da ku na cikin zunubi" ko "za ku mutu a loƙacin da ku na yin zunubi"
ba za ku iya zuwa ba
"ba ku iya zuwa ba"
Yahudawa su ka ce
A nan "Yahudawa" magana ce na "shugabanin Yahudawa." AT: "shugabanin Yahudawa sun ce"(Dubi: figs_synecdoche)
John 8:23-24
ku daga kasa kuke
"An haife ku a cikin wannan duniya"
Ni kuwa daga bisa ni ke
"na zo daga sama"
Ku na wannan duniya ne
"Ku na wannan duniya ne"
Ni kuwa ba na wannan duniya ba ne
"NI ba na wannan duniya ba ne"
za ku mutu cikin zunubanku
"zu ku mutu da ba Allah ya yafe ku zunuben ku ba"
cewa NI NE
AT: 1) Yesu ya na bayyana kansa a kamar Yahweh, wadda ya ke nufin "Ni ne" ko 2) "Yesu ya so mutanin su gani cewa ya na nufin abin da ya rigaya ce shi ne: "Ina daga sama."
John 8:25-27
Suka ce
Kalmar "Su" ya na nufin shugabanin Yahudawa. (Dubi: John 8:22)
wadannan abubuwan su ne na ke gaya wa duniya
A nan "duniya" magana ne na mutanin da suke rayuwa a cikin duniya. AT: "waddannan abubuwa da na faɗa wa dukka mutane" (Dubi: figs_metonymy)
John 8:28-30
Sa'adda kuka tada
Wannan ya na nufin sa Yesu a kan giciye don a kashe shi.
Dan Mutum
Yesu ya yi amfani da wannan lakabin "Dan Mutum" wa kansa.
NI NE
Kamar Allah Ɗa, Yesu ya san Allah Uba fiye da kowa. AT: 1) Yesu ya na bayyana kansa a mastayin Yahweh ta wurin cewa, "Ni ne Allah" ko 2) Yesu ya na cewa, "ni ne wadda na ke faɗa."
Kamar yadda Uba ya koya mani, haka nike fadin wadannan abubuwa
"Ina faɗan abinda Ubana ya koya mani in faɗa." Kalmar "Uba" muhimmin lakami ne wa Allah. (Dubi: guidelines_sonofgodprinciples)
Shi wadda ya aiko ni
Kalmar "shi" ya na nufin Allah.
Sa'adda Yesu ya ke faɗin wadannan abubuwa
"Sa'adda Yesu ya faɗa waddannan kalmomin"
dayawa suka bada gaskiya gare shi
"mutane dayawa sun yarda da shi"
John 8:31-33
tsaya a cikin magana ta
Wannan karin magana ne da ya ke nufin "yin biyyaya da Yesu." AT: "yi biyyaya da abin da na faɗa" (Dubi: figs_idiom)
almajiraina
"masu bi na"
gaskiya zata 'yantar da ku
Wannan karin magana ne. Yesu ya yi magana akan "gaskiyan" kamar mutum ne. AT: "Idan kun yi biyyaya da Allah, Allah zai yantar da ku" (Dubi: figs_personification)
gaskiyan
Wannan ya na nufin abin da Yesu ya bayana game da Allah. AT: "abin da ke gaskiya game da Alla"
yaya za ku ce, 'Za a 'yantar da ku'?
Wannan magana ya bayyana kamar tambaya ne domin ya nuna mamakin shugabanin Yahudawa a abin da Yesu ya faɗa. AT: "Ba mu neman a cece mu!" (Dubi: figs_rquestion)
John 8:34-36
Hakika, hakika
Dubi yadda an fasara wannan a cikin 1:51.
bawan zunubi ne
A nan kalmar "bawa" karin magana ne. Wannan ya na nufin cewa "zunubi" ya na nan kamar maigida ne ga wadda yake yin zunubi. AT: "ya na nan kamar bawan zunubi" (Dubi: figs_metaphor)
a cikin gida
A nan "gida" magana ne na "iyali." AT: "A matsayin cikkaken dan iyalin" (Dubi: figs_metonymy)
ɗan ya zama har abada
Wannan karin magana ne. Za ku iya fasara shi ta amfani da kalmomin. AT: "ɗan dan gidan ne har abada" (Dubi: figs_ellipsis)
idan Dan ya 'yantar da ku zaku zama 'yantattu sosai
Ya na nufin cewa Yesu ya na magana game da yanci daga zunubi, wadda magana ne na rashin iya yin zunubi. AT: "Idan Ɗan ya 'yantar da ku, zaku iya yantuwa daga zunubi" (Dubi: figs_explicit and figs_metaphor)
idan Ɗan ya 'yantar da ku
"Ɗan" muhimmin lakabi ne na Yesu, Ɗan Allah. Yesu ya yi magana game da kansa ne. AT: "Idan Ni, Ɗan, ya yantar da ku" (Dubi: guidelines_sonofgodprinciples and figs_123person)
John 8:37-38
kalma ta bata da wurin zama a cikin ku
A nan "kalma" magana ne na "koyarswa" ko "sakon" Yesu, wadda shugabanin Yahudawa ba karba ba. AT: "ba ku karbi koyarswa na ba" ko kuma "ba ku yarda sako na ta canza rayuwarku ba" (Dubi: figs_metonymy)
Na fadi abubuwan da na gani da Ubana
"Ina gaya maku game da abubuwan da na gani a loƙacin da ina tare da Uba na"
kuna yin abubuwan da kuka ji daga wurin ubanku
Shugabanin Yahudawa ba su gane cewa ta wurin "Ubanku" Yesu ya na nufin shaidan ne ba. AT: "kun kuma cigaba da yin abin da Ubanku ya gaya maku ku yi"
John 8:39-41
uba
kakane
Ibrahim bai yi wannan ba
"Ibrahim bai taba gwada kashe wani da ya gaya mashi gaskiyan wahayi daga Allah ba"
Kuna yin ayyukan ubanku
Yesu ya na nufin cewa shaidan ne ubansu. AT: "a'a! Ku na yin abubuwan da ainahin ubanku ya yi" (Dubi: figs_explicit)
ba a haife mu cikin fasikanci ba
A nan shugabanin Yahudawa su na nufin cewa Yesu bai san wa ne ainahin Ubansa ba. AT: "Ba mu san game da kai ba, amma ba mu ne ainahin 'ya'yan ba" ko kuma "An haife mu daga aurya da ya kamata" (Dubi: figs_explicit)
muna da Uba daya: Allah
A nan shugabanin Yahudawa sun amince cewa Allah ne Ubansu na ruhaniya. Wannan mihimmin lakabi ne wa Allah. (Dubi: guidelines_sonofgodprinciples)
John 8:42-44
kaunace
Wannan ne irin kauna da ya ke zuwa daga Allah kuma ya na kan kyauwawan mutane (tare da makiyanmu), ko bai amfane mutum ba.
Meyasa baku gane magana ta ba?
Yesu ya na amfani da wannan tambaya domin ya tsauta wa shugabanin Yahudawa domin rashin jin su. AT: "Zan gaya maku dalilin da ba ku gane abin da na faɗa!" (Dubi: figs_rquestion)
Ai saboda ba za ku iya jin maganata ba ne
A nan "magana" ya na nufin "koyarswan" Yesu. AT: "Ai saboda ba za ku yarda da koyarswa ta ba. (Dubi: figs_metonymy)
Ku na ubanku, shaidan ne
"ku na ubanku, shaidan"
uban karya
A nan "uba" magana ne na wadda ya soma karya. AT: "shi ne wadda ya halittce dukka karya a farko" (Dubi: figs_metaphor)
John 8:45-47
domin ina faɗin gaskiya
"domin ina faɗa maku abubuwan gaskiya game da Allah"
Wanene a cikin ku ya kama ni da zunubi?
Yesu ya yi amfani da wannan tambaya domin ya bayana cewa bai taba yin zunubi ba. AT: "Ba bu wani a cikin ku da zai iya nuna cewa na taba yin zunubi!" (Dubi: figs_rquestion)
Idan na fadi gaskiya
"Idan na faɗa abubuwan da suke gaskiya"
don me ba ku gaskanta ni ba?
Yesu ya yi amfani da wannan tambaya don ya tswata shugabanin Yahudawa domin rashin gaskanta. AT: "ba ku da dalilin rashin gaskanta da ni!" (Dubi: figs_rquestion)
maganar Allah
A nan "maganar" ya na nufin "sakon" Allah. AT: "sakon Allah" ko kuma "gaskiya da ya ke zuwa daga Allah" (Dubi: figs_metonymy)
John 8:48-49
Yahudawa
"Yahudawa" karin magana ne da ya ke wakilcin "shugabanin Yahudawa" da suke hamayya da Yesu. AT: "shugabanin Yahudawa" (Dubi: figs_synecdoche)
Bamu fadi gaskiya ba da muka ce kai Basamariye ne kuma kana da aljani?
shugabanin Yahudawa sun yi amfani da wannan tambaya domin su kushe Yesu su kuma ci masa mutunci. AT: "Hakika mun yi daidai da mu ka ce kai ba-Samariye ne kuma aljani ya na rayuwa a cikin ka!" (Dubi: figs_rquestion)
John 8:50-51
akwai wanda ke nema yana kuma hukuntawa
Wannan ya na nufin Allah.
kiyaye maganata
A nan "magana" zance ne na "koyarswan" Yesu. AT: "yi biyayya da koyarswa na" ko "yi abin da na ce" (Dubi: figs_metonymy)
ga mutuwa
Wannan karin magana ne da yake nufin taba mutuwa. Anan Yesu ya na nufin mutuwa ta ruhaniya. AT: "mutu a ruhaniya" (Dubi: figs_idiom)
John 8:52-53
Yahudawa
A nan "Yahudawa" magana ne na "shugabanin Yahudawa" wadda suke hamayya da Yesu. AT: "shugabanin Yahudawa" (Dubi: figs_synecdoche)
Idan wani ya yi biyayya da maganata
"Idan wani ya yi biyayya da koyarswata"
dandana mutuwa
Wannan karin magana ne da yake nufin taba mutuwa. Shugabanin Yahudawa sun yi kuskure ta tunani cewa Yesu ya na magana akan mutuwa ta jiki ne kadai. AT: "mutu" (Dubi: figs_idiom)
Ai baka fi ubanmu Ibrahim girma ba wanda ya mutu, ko ka fi shi?
Shugabanin Yahudawa sun yi amfani da wannan tambaya domin su bayana cewa Yesu bai fi Ibrahim ba.AT: "Hakika ba ka fi Ubanmu Ibrahim wanda ya mutu ba!" (Dubi: figs_rquestion)
Wa kake daukar kanka ne?
Yahudawa sun yi amfani da wannan tambaya don su kwaɓe Yesu domin ya na tunani cewa ya fi Ibrahim muhimmi. AT: "Kada ka yi tunani cewa ka na da muhimmi!" (Dubi: figs_rquestion)
John 8:54-56
Ubana ne ya daukaka ni-Wanda kuka ce shi ne Allahnku
Kalmar "Uba" muhimmin lakami ne wa Allah. Ba bu wadda ya san Allah Uba kamar Yesu, Ɗan Allah. AT: "Uba na ne ya na daukaka na, sai kuma ku na ce shi ne Allahnku" (Dubi: guidelines_sonofgodprinciples)
kiyaye kalmarsa
A nan "kalma" magana ne na abin da Allah ya ce. AT: "Ina biyayya da abin da ya ce a yi" (Dubi: figs_metonymy)
rana ta
Wannan magana ne na abin da Yesu zai cika a loƙacin rayuwarsa. AT: "abin da zan yi a loƙacin rayuwata" (Dubi: figs_metonymy)
ya gan ta kuma ya yi murna
"ya gan zuwa na ta wurin wahayin Allah sai ya yi murna"
John 8:57-59
Yahudawa su ka ce masa
A nan "Yahudawa" magana ne na "shugabanin Yahudawa" wadda sun yi hamayya da Yesu. AT: "shugabanin Yahudawa sun ce masa" (Dubi: figs_synecdoche)
Baka riga ka kai shekara hamsin ba tukuna, kuma ka taba ganin Ibrahim?
Shugabanin Yahudawa sun yi amfani da wannan tambaya domin su bayana mamakin sun cewa Yesu ya ce ya gan Ibrahim. AT: "Ka na kasa da shekaru hamsin. Da ba ka iya ganin Ibrahim ba!" (Dubi: figs_rquestion)
kafin a haifi Ibrahim, NI NE
Kamar Allah Ɗa, Yesu ya san Allah Uba fiye da kowa. AT: 1) Yesu ya na bayyana kansa kamar Yahweh ta wurin cewa, "Ni ne Allah" ko kuma 2) Yesu ya na cewa, kafin Ibrahim ya kasance, Na kasance."
Sa suka dauki duwatsu za su jefe shi
Shugabanin Yahudawa sun yi fushi a abin da Yesu ya ce. A nan ya na nufin cewa sun so su kashe shi domin ya sa kanshi daidai da Allah. AT: "Sai sun dauki duwasu su kashe shi domin ya ce shi daidai ne da Allah" (Dubi: figs_explicit)
John 9
John 9:1-2
Muhimmin Bayani:
Sa'ad da Yesu da almajiransa su na tafiya, sun hadu da wani makaho.
Yanzu
Wannan kalma ya nuna cewa marubucin ya na so ya kwatanta sabon abu.(Dubi: writing_newevent)
da Yesu yana wucewa
Anan "Yesu" magana ne na Yesu da almajiransa. AT: "sa'ad da Yesu da almajiransa suka wuce"(Dubi: figs_synecdoche)
wa yayi zunubi, mutumin ne ko iyayensa ... makaho?
Wannan tambaya ya nuna tsohon amincewa na Yahudawa da cewa zunubi ne ya na sa dukka cituttuka da sauran mugun aibi ga jiki. Mallamai sun zata cewa yaro ya na iya yin zunubi daga cikin ciki. AT: "Mallam, mun san cewa zunubi ya na sa mutum makaho. Zunubin wa ne ya sa an haife wannan mutum makaho? Mutumin nan da kansa ne ya yi zunubi, ko iyayensa ne?" (Dubi: figs_explicit)
John 9:3-5
Mu
Wannan "mu" ya na tare da Yesu da almajiran da yake magana da su. (Dubi: figs_inclusive)
rana ... dare
A nan "rana" da "dare" karin magana ne. Yesu ya na kwatanta loƙacin da mutane su na iya yin aikin Allah har rana, loƙacin da mutane su na aiki, da kuma dare loƙacin da ba za su iya yin aikin Allah ba. (Dubi: figs_metaphor)
cikin duniya
A nan "duniya" magana ne na mutanin da suke cikin duniya. AT: "yin rayuwa a sakanin mutanin wannan duniya" (Dubi: figs_metonymy)
hasken duniya
A nan "haske" magana ne na gaskiyan wahayin Allah. AT: "wadda ya ke nuna abin da yake gaskiya kamar yadda haske ya na barin mutane su gani abin da yake cikin duhu" (Dubi: figs_metaphor)
John 9:6-7
kwaba kasar da yawunsa
Yesu ya yi amfani da yatsun shi ya kwaba datti da yawu. AT: "ya yi amfani da yasunsa ya kwaba dattin da yawu don ya yi laka" (Dubi: figs_explicit)
wanke ... wanke
Za ku iya sa a bayyane cewa Yesu ya so mutumin ya wanke lakan a idonshi a cikin tafkin kuma haka mutumin ya yi. (Dubi: figs-explicit)
wadda an fasara: "aike"
An sami dan yanka a cikin labarin don haka Yahaya zai iya bayana wa masu karatunsa abin da "Siloam" ya ke nufi. AT: "wadda yake nufin "aike" (Dubi: writing_background)
John 9:8-9
Ba wannan mutum ne wanda ya ke zaune yana roko ba?
Wannan magana ya bayyana kamar tambaya domin ya nuna mamakin mutanin. AT: "Wannan mutumin ne wadda ya saba zaune yana roko!" (Dubi: figs_rquestion)
John 9:10-12
Mahaɗin Zance:
maƙwabcin mutumin da ya taba makwace sun cigaba da magana da shi.
To yaya aka bude maka idanu?
"To mai ne ya sa ka iya gani?" ko kuma "Ta yaya ka na iya gani yanzu?"
shafa mani a idanuna
"yi amfani da yatsunsa don ya rufe mun idanu na da laka." Dubi yadda kun fasara irin wannan jumla a cikin 9:6.
John 9:13-15
Suka kawo mutumin da yake makaho a da wurin Farisawa
Mutanin sun nace cewa sai mutumin ya tafi da su wurin Farisawa. Bu su tilasa shi da karfi ya je ba.
Ranar asabar
"Ranar hutun Yahudawa"
Sai kuma Farisawan suka tambaye shi
"Sai Farisawa sun kuma tambaye shi"
John 9:16-18
ba ya kiyaye ranar Asabar
Wannan ya na nufin cewa Yesu ba ya kiyaye doka game da yin aiki a ranar hutun Yahudawa.
Yaya mai zunubi zai yi irin wadannan alamu?
Wannan magana ya bayyana kamar tambaya ne domin ya nanata cewa alamun Yesu ya nuna cewa shi ba mai zunubi ba ne. "Mai zunubi ba zai iya yin wannan abu ba!" (Dubi: figs_rquestion)
alamu
Wannan wata kalma ne na abin al'ajibi. "Alamu" ya na ba da shaida cewa Allah shi ne mai dukka iko, kuma wadda yake da iko akan duniya.
shi annabi ne
"Ina tunani shi annabi ne"
Har yanzu Yahudawan basu yarda ba
A nan "Yahudawa" magana ne na "shugabanin Yahudawa" wadda suka yi hamayya da Yesu. AT: "Yanzu shugabanin Yahudawa ba su yarda ba.(Dubi: figs_synecdoche)
John 9:19-21
Su ka tambayi iyayen
"Su" ya na nufin shugabanin Yahudawa.
shi cikakken mutum ne
"shi na miji ne" ko "shi ba yaro ba ne kuma"
John 9:22-23
suna ji tsoron Yahudawan
A nan "Yahudawa" ya na nufin shugabanin Yahudawa" wadda sun yi hamayya da Yesu. AT: "sun ji tsoron abin da shugabanin Yahudawa za su iya yi masu" (Dubi: figs_synecdoche)
tsoro
Wannan ya na nufin rashin dadi da mutum ya ke da shi a loƙacin da akwai wata kurarin lahani a kansa ko waddansu.
zai ce Yesu Almasihu ne
"zai faɗa cewa Yesu Almasihu ne"
za a fitar dashi daga majami'a
A nan "fitar daga majami'a" magana ne na rashin yarda a sake shiga majami'a kuma ba bu sake kasancewa a kungiyar mutane da suke zuwa sujada a majami'a. AT: "ba za a yarda masa ya shiga cikin majami'a ba" ko "ba zai cigaba da zama ɗan majami'a ba" (Dubi: figs_metaphor)
John 9:24-25
Suka kira mutumin
A nan "su" ya na nufin Yahudawa. ([Yahaya 9:18]
Girmama Allah
Wannan karin magana ne da mutane suke amfani da shi a loƙacin daukan rantsuwa. AT: "A gaban Allah, faɗa gaskiya" ko kuma "Faɗa gaskiya a gaban Allah" (Dubi: figs_idiom)
wancan mutum
Wannan ya na nufin Yesu.
wannan mutum
Wannan ya na nufin mutumin da ada shi makaho ne.
John 9:26-29
Don me ku na so ku ji kuma?
Wannan magana ya bayyana kamar tambaya ne domin ya bayana mamakin mutumin da cewa shugabanin Yahudawa sun ce masa ya gaya masu abin da ya faru kuma. (Dubi: figs_rquestion)
kuna so ku zama almajiransa, haka ne?
Wannan magana ya bayyana kamar tambaya ne domin karin fasara a maganan mutumin. Ya san cewa shugabanin Yahudawa ba su so su bi Yesu. Ya na so ya yi masu ba'a anan. AT: "kamar ku na so ku zama almajiransa!" (Dubi: figs_rquestion and figs_irony)
Ku almajiransa ne
"Ku na bin Yesu!"
amma mu almajiran Musa ne
Kalmar "mu" ya na a bayyane. shugabanin Yahudawa su na maganan kansu ne kadai. AT: "amma muna bin Musa" (Dubi: figs_exclusive)
Mun san cewa Allah ya yi magana da Musa
"Mun tabata cewa Allah ya yi magana da Musa"
ba mu san inda wannan ya fito ba
A nan shugabanin Yahudawa su na nufin Yesu. Suna nufin cewa ba shi da ikon kiran almajirai. AT: "ba mu san inda ya fito ba ko kuma inda ya sami ikonsa" (Dubi: figs_explicit)
John 9:30-31
cewa baku san inda ya fito ba
Mutumin ya na mamakin cewa shugabanin Yahudawa su na tuhunta ikon Yesu bayan sun san cewa ya na da ikon warkarwa. AT: "cewa ba ku san inda ya ke samu ikonsa ba" (Dubi: figs_explicit)
baya jin masu zunubi ... jin sa
"baya amsa addu'an masu zunubi ... Allah ya na amsa addu'ar sa"
John 9:32-34
ba a taba jin cewa wani ya bude
Wannan jumla ne. AT: "ba bu wadda ya taba ji game da wani da ya taba warkar da mutum makaho tun daga haifuwa ba" (Dubi: figs_activepassive)
In mutumin nan ba daga Allah yake ba, ba zai iya yin komai ba
Wannan jumla ya yi amfani da hanyoyi dabam dabam. "Mutum daga Allah ne kadai zai iya yin abu irin wannan!" (Dubi: figs_doublenegatives)
An haife ka a cikin zunubai, yanzu kana so ka yi mana koyarwa?
Wannan magana ya bayyana kamar tambaya ne domin karin bayani. Ya na kuma nufin cewa an haife mutumin da makance domin zunuban iyayensa. AT: "An haife ka dalilin zunuban iyayenka. Ba ka kai ka koyar da mu ba!" (Dubi: figs_rquestion)
suka fitar da shi
"suka fitar da shi daga majami'a"
John 9:35-38
gaskanta da
Wannan ya na nufin "gaskanta da Yesu," gaskanta cewa shi ne Ɗan Allah, yarda cewa shi ne mai ceto, ku kuma yi rayuwa a hanyar da zai girmama shi.
John 9:39-41
zo cikin wannan duniya
Kalmar "duniya" ya na nufin "mutane da suke rayuwa a cikin duniya." AT: "zo ya yi rayuwa a sakanin mutanin wannan duniya" (Dubi: figs_metonymy)
domin wadanda ba su gani su gani, saboda kuma wadanda suke gani su zama makafi
A nan "gani" da "makanta" karin magana ne. Yesu ya banbanta mutane da su ke makance ta ruhaniya da makance na jiki. AT: "domin waddanda suka makance a ruhaniya, amma waddanda su ke so su gan Allah, su na iya ganin shi, kuma waddanda sun riga sun yi tunani cewa za su iya ganin Allah ne za su cigaba a cikin makantansu"(Dubi: figs_metaphor)
Muma makafi ne?
"Ka na tunani cewa mun makance a ruhaniya ne?"
Inda ce ku makafi ne, da ba ku da zunubi
A nan "makanta" magana ne na rashin sanin gaskiyar Allah. AT: "Inda ce kun so ku san gaskiyar Allah, za ku iya gani.(Dubi: figs_metaphor)
amma yanzu kun ce, 'Muna gani', don haka zunubinku ya tabbata
A nan "gani" magana ne na sanin gaskiyar Allah. AT: "Tunda ku na tunani cewa kun riga kun san gaskiyar Allah, za ku cigaba da makance" (Dubi: figs_metaphor)
John 10
John 10:1-2
Mahaɗin Zance:
Yesu ya cigaba da magana da Farisawa. Wannan ne sashen labari wadda ya fara a cikin 9:35.
Muhimmin Bayani:
Yesu ya fara magana a cikin misalai. (Dubi: figs_parables)
Hakika, hakika
Dubi yadda kun fasara wannan a cikin 1:51.
garken tumaki
Wannan wurin danga ne wadda makiyayi ya na sa tumakinsa.
barawo da dan fashi
Wannan ya na nufin yadda ake amfani da kalmomi biyu makamanci domin karin nanaci. (Dubi: figs_doublet)
John 10:3-4
Mai gadin kofar ya na bude masa
"Mai gadin kofar ya na bude wa tumaki kofa"
Mai gadin kofa
Wannan mutum ne wadda an yi hayarsa domin ya duba kafar garken tumaki da dare a loƙacin da makiyayin ba ya nan.
Tumakin suna jin muryarsa
"Tumakin ya gi muryan makiyayi"
yana tafiya a gabansu
"ya na tafiya a gabansu"
domin sun san muryarsa
"domin sun gane muryarsa"
John 10:5-6
basu gane
AT: 1) "almajiran ba su gane ba" ko 2) "taron ba su gane ba."
wannan misali
Wannan kwatanci ne daga aikin makiyayi, ta wurin amfani da karin magana. "Makiyayi" karin magana ne na Yesu. "Tumaki" su na wakilcin waddanda suke bin Yesu, kuma "ɓaki" su ne shugabanin Yahudawa, hade da Farisawa, wadda sun gwada rudin mutane. (Dubi: figs_metaphor)
John 10:7-8
Ni ne kofar tumaki
A nan "kofa" magana ne da yake nufin cewa Yesu ya tanada hanya zuwa garken tumaki, wurin da mutanin Allah suke zama a gabansa. AT: "Ina nan kamar kofa da tumaki suke amfani don su shiga cikin garken tumaki"(Dubi: figs_metaphor)
Dukan wadanda suka zo kamin ni
Wannan Ya na nufin wadansu mallamai da su ka koyar da mutanen, tare da Farisawa da kuma wadansu shugabanin Yahudawa. AT: "Dukan malaman da suka zo ba tare da iko na ba" (Dubi: figs_explicit)
John 10:9-10
Ni ne kofa
A nan "kofa" ƙarin magana ne. Ta wurin kiran kansa "kofa," Yesu ya na nuna cewa shi ne yake ba da hanyar gaskiya na shiga mulkin Allah. AT: "Ni da kai na ina nan kamar kofa" (Dubi: figs_metaphor)
kiwata
Kalmar "kiwata"ya na nufin wuri mai ciyawa da tumaki ke ci.
ba ya zuwa sai don ya yi sata
Wannan biyu ne. A wadansu harshuna ya fi kyau a yi amfani da jumla mai kyau. AT: "zuwa don ya yi sata kadai" (Dubi: figs_doublenegatives)
yi sata, ya kashe, ya kuma hallakar
Maganar a nan shi ne "tumaki," wadda ya na wakilcin mutanin Allah. AT: "sata, kashe, da kuma hallakar da tumaki" (Dubi: figs_explicit and figs_metaphor)
domin su sami rai su
Kalmar "su" ya na nufin tumaki. "Rai" ya na nufin rai madawami. AT: "domin su rayu, ba tare da rashi ba"
John 10:11-13
Ni ne makiyayi mai kyau
A nan "Makiyayi mai kyau" magana ne da yake wakilcin Yesu. AT: "Ina nan kamar Makiyayi mai kyau" (Dubi: figs_metaphor)
bada ransa
Ba da wani abu ya na nufin ka mika ranka. Wata hanya ne na mara tsanani da yake nufin mutuwa. AT: "mutu" (Dubi: figs_euphemism)
mai aikin kudi
"mai aikin kudi" magana ne da ya na wakilcin shugabanin Yahudawa da kuma mallamai. AT: "wadda yake kamar mai aikin kudi" (Dubi: figs_metaphor)
saki tumakin ya ... bai damu da tumakin ba
A nan kalmar "tumaki" magana ne da ya na waklicin mutanin Allah. Kamar mai aikin kudi wadda ya saki tumakin, Yesu ya ce shugabanin yahudawa da mallamai ba su damu da mutanin Allah ba. (Dubi: figs_metaphor)
John 10:14-16
Uban ya san ni, ni ma na san Uban
Allah Uba da Allah Ɗa sun san juna fiye da yadda wani ya san su. "Uba" muhimmin lakami ne wa Alla. (Dubi: guidelines_sonofgodprinciples)
Na ba da raina domin tumakin.
Wannan karamin hanya ne da Yesu zai ce zai mutu domin ya kare tumakinsa. AT: "Na mutu don tumakin" (Dubi: figs_euphemism)
Ina da wadansu tumaki
A nan "wadansu tumaki" karin magana ne na masu bin Yesu wadanda ba Yahudawa ba. (Dubi: figs_metaphor)
garke daya da makiyayi daya
A nan "garke" da "makiyayi" karin magana ne. Dukka masubin Yesu, Yahudawa da wadanda ba Yahudawa ba, za su zama kamar garkin tumaki. Zai zama kamar makiyayi wadda ya damu da dukkan su. (Dubi: figs_metaphor)
John 10:17-18
Domin wannan ne Uban yake kauna ta: Na bada raina
Madauwamin shirin Allah shi ne Allah Ɗa ya ba da rainsa domin ya biya zunuban 'yan Adam. Mutuwar Yesu a kan giciye ya bayyana kaunar Ɗan wa Uban kuma na Uban zuwa ga Ɗan.
Uba
Wannan muhimmin lakabi ne wa Allah. (Dubi: guidelines_sonofgodprinciples)
Kauna
Wannan irin kauna ya na zuwa daga Allah ne ya na bisa kyaun mutane, ko bai amfani wani ba. Irin wannan kauna ya na kula da mutane, ko mai abin da sun yi.
Na bada raina domin in same shi kuma
Wannan karamin hanya ne da Yesu zai ce zai mutu sai ya kuma rayu kuma. AT: "Na yarda in mutu domin in sake rayu" (Dubi: figs_euphemism)
ina bayar da shi da kaina
An yi amfani da "kaina" anan domin a nanata cewa Yesu ya ba da rainsa. Ba bu wadda zai karɓa daga wurinsa. AT: "Ni da kai na bayar" (Dubi: figs_rpronouns)
Na karbi wannan umarnin daga wurin Ubana
"Wannan ne abin da Uba na ya umurce ni in yi." Wannan kalmar "Uba" muhimmin lakami ne wa Allah. (Dubi: guidelines_sonofgodprinciples)
John 10:19-21
Don me ku ke sauraronsa?
Wannan magana ya bayyana kamar tambaya ne domin ya nanata maganar cewa kada mutane su saurare Yesu. AT: "Kada ku saurare shi!" (Dubi: figs_rquestion)
Aljani zai iya bude idanun makaho?
Wannan magana ya bayyana kamar tambaya ne domin karin bayani. AT: "Hakika aljani ba zai sa makaho ya iya gani ba!" ko kuma "Hakika aljani ba zai iya sa makafe gani ba!" (Dubi: figs_rquestion)
John 10:22-24
Idin Tsarkakewa
Wannan hutun ɗari ne na kwana takwas wadda Yahudawa suke amfani don tunawa da wata abin al'ajibi wadda Allah ya sa mai kadan ya cigaba da ba da haske a fitila har kwana takwas. Sun haska fitilar domin su tsarkake haikalin Yahudawa wa Allah. Tsarkaka abu ya na nufin yin alkawari cewa za ku yi amfani da shi a nufi mai kyau.
Yesu yana tafiya a cikin haikalin
Wurin da Yesu ya yi tafiya wuri ne da yake wajen filin haikalin. AT: "Yesu ya na tafiya a cikin filin haikali"(Dubi: figs_explicit)
shirayi
Wannan abu ne da an kafa da ya ke a hade da kofan gini; ya na da jinka kuma ya na iya samu katanga ko ba bu.
Sai Yahudawa suka zagaye shi
A nan "Yahudawa" ya na nufin shugabanin Yahudawa wadda sun yi hamayya da Yesu. AT: "Sai shugabanin Yahudawa suka zagaye shi" (Dubi: figs_synecdoche)
bar mu cikin shakka
Wannan karin magana ne. AT: "sa mu mamaki" ko kuma "hana mu sanin takamaiman?" (Dubi: figs_idiom)
John 10:25-26
a cikin sunan Ubana
A nan "suna" magana ne na ikon Allah. Anan "Uba" muhimmin lakami ne wa Allah. Yesu ya yi abin al'ajibi ta wurin ikon Ubansa. AT: "ta wurin ikon Ubana" ko "da ikon Ubana" (Dubi: figs_metonymy and guidelines_sonofgodprinciples)
wadannan ke yin shaida a kaina
Al'ajibinsa ya ba da shaida game da shi kamar yadda mutumin da yake yin shaida zai ba da shaida a kotun shari'a. AT: "ba da shaida game da ni" (Dubi: figs_personification)
ba tumakina ba ne
Kalmar "tumaki" magana ne na masubin Yesu. AT: "ba masubina ba" ko "ba almajirai na ba" (Dubi: figs_metaphor)
John 10:27-28
Tumakina suna jin murya ta
Kalmar "tumaki" misali ce ta masubin Yesu. An bayyana Yesu kamar "makiyayi." AT: "Yadda tumaki su na bin muryan makiyayinsu na gaskiya, masu bi na su na jin murya na" (Dubi: figs_metaphor)
babu wanda zai kwace su daga hannu na
Kalmar "hanu" anan magana ne da ya na wakilcin karewa da kula na Yesu. AT: "babu wadda zai sata su daga wuri na" ko kuma "za su kasance lafiya a kulawa na" (Dubi: figs_metonymy)
John 10:29-31
Ubana, wanda ya bani su
Kalmar "Uba" muhimmin lakabi ne wa Allah. (Dubi: guidelines_sonofgodprinciples)
hannun Uban
Kalmar "hanu" ya na nufin dukiya da kiyayewar Allah. AT: "Ba bu wadda zai sata su daga Ubana"(Dubi: figs_metonymy)
Ni da Uban daya ne
Yesu, Allah Da, da Allah Uba daya ne. Kalmar "Uba" muhimmin lakami ne wa Allah. (Dubi: guidelines_sonofgodprinciples)
Sai Yahudawa suka dauki duwatsu
Kalmar "Yahudawa" ya na nufin shugabanin Yahudawa wadda suka yi hamayya da Yesu. AT: "Sai shugabanin Yahudawa suka fara dauka duwatsu kuma" (Dubi: figs_synecdoche)
John 10:32-33
Yesu ya amsa masu, "Na nuna maku kyawawan ayyuka masu yawa daga wurin Uban
Yesu ya yi su abubuwan al'ajibi ta wurin ikon Allah. Kalmar "Uba" muhimmin lakami ne wa Allah. (Dubi: guidelines_sonofgodprinciples)
Saboda wane daga cikin wadannan ayyukan kuke jefe ni?
Yesu ya san cewa shugabanin Yahudawa ba su so su jefe shi ba domin ya yi kyauwawan ayyaka.(Dubi: figs_irony)
Sai Yahudawa suka amsa masa
Kalmar "Yahudawa" karin magana ne da ya na wakilcin shugabanin Yahudawa wadda suka yi hamayya da Yesu. AT: "gefen Yahudawan suka amsa" ko kuma "shugabanin Yahudawa sun amsa masa" (Dubi: figs_synecdoche)
mayar da kanka Allah
"cewa shi Allah"
John 10:34-36
A rubuce yake ... alloli"'?
Wannan magana ya bayyana kamar tambaya ne domin karin bayani. AT: "Ya kamata kun san cewa a rubuce ya ke a shari'ar ku cewa, 'ku alloli ne." (Dubi: figs_rquestion)
ku alloli ne
Yesu a nan ya yi magana daga nassi inda Allah ya kira masubinsa "alloli," watakila domin ya zabe su ne su wakilce shi a duniya.
maganar Allah ta zo
Yesu ya yi maganar sakon Allah kamar mutum ne wanda ya maso kusa da wadanda sun ji shi. AT: "Allah ya faɗi sakonsa" (Dubi: figs-metaphor)
ba za a iya karya nassi ba
AT: 1) "ba bu wani da zai iya canza nassi" ko kuma 2) "a ko yaushe nassi yakan kasance gaskiya."
kuna gaya wa wanda Uban ya kebe ya kuma aiko cikin duniya, 'Kana sabo', domin Na ce, 'Ni dan Allah ne'?
Yesu ya yi amfani da wannan tambaya don ya tsawata abokan gabansa domin sun ce ya na sabo a loƙacin da ya kira kansa "Ɗan Allah." AT: "kada ku ce wa wanda Allah ya kebe don ya aika cikin duniya, 'kana sabo; a loƙacin da na ce ni ne Ɗan Allah!" (Dubi: figs_rquestion)
Kana sabo
"ka na zagin Allah." Abokan gaban Yesu sun gane cewa a loƙacin da an ce shi ne Ɗan Allah, ya na nufin cewa shi daidai ne da Allah.
Uba ... Dan Allah
Wadannan muhimmin lakabi ne da ya na kwatanta dangantaka a sakanin Allah da Yesu.(Dubi: guidelines_sonofgodprinciples)
John 10:37-39
gaskata da ni
A nan kalmar "gaskanta" ya na nufin amincewa ko kuma yarda cewa abin da Yesu ya faɗa gaskiya ne.
gaskata da ayyukan
A nan "gaskanta da" shi ku yarda cewa ayyukan da Yesu ya yi daga Uban ne.
Uban yana ciki na, ni kuma ina cikin Uban
Wadannan karin magana ne da su na bayyana dangantaka na ƙwarai sakanin Allah da Yesu. AT: "Ni da Ubana daya ne a haɗe" (Dubi: figs_idiom)
fita daga hannunsu
Kalmar "hannu" magana ne da ya na wakilcin kula ko dukiyar shugabanin Yahudawa. AT: "tafi daga su kuma" (Dubi: figs_metonymy)
John 10:40-42
gaba da kogin Urdun
Yesu ya na gefen yamma na rafin Urdun. AT: "zuwa gabas na rafin Urdun" (Dubi: figs_explicit)
ya kuma zauna a wurin
Yesu ya tsaya ta gabas Urdun na dan loƙaci kadan. AT: "Yesu ya zauna na kuanaki dayawa a wurin" (Dubi: figs_explicit)
Yahaya bai yi wasu alamu ba, amma dukan abubuwan da Yahaya ya ce game da wannan mutum gaskiya ne
"gaskiya ne cewa Yahaya bai yi wani alamu ba, haƙiƙa bai faɗa gaskiya game da wannan mutum ba, wadda yake yin alamu."
alamu
Wadannan abubuwan al'ajibi ne wadda ya ke nuna cewa wani abin gaskiya ne ko kuma ya na amince mutum.
gaskanta a
A nan "gaskanta a" ya na nufin amince ko kuma yarda da abin da Yesu ya faɗa gaskiya ne.
John 11
John 11:1-2
Muhimmin Bayani:
Wadannan Sura su na gabatar da labarin Lazarus da kuma ba da tushen bayana game da shi da kuma yar'uwarsa Maryamu. (Dubi: writing_participants and writing_background)
Maryamu ne wadda ta shafe Ubangiji ... da gashin kanta
Sa'adda Yahaya ya gabatar da Maryamu, yar'uwar Mata, ya ba da bayani game da abin da zai faru anjuma a cikin labarin. (Dubi: writing_background)
John 11:3-4
aika wa Yesu
"roke Yesu ya zo"
kauna
A nan "kauna" ya na nufin kaunar 'yan'uwa, ta halitta, kauna na mutum a sakanin abokai da dangi.
Wannan ciwo ba zai kai ga mutuwa ba
Yesu ya na nufin cewa ya san abin da zai faru da Li'azaru da ciwonsa. AT: "Mutuwa ba zai zama .karshen sakamakon wannan ciwo ba" (Dubi: figs_explicit)
mutuwa
Wannan ya na nufin mutuwa ta jiki.
amma domin daukakar Allah ne, domin Dan Allah ya sami daukaka tawurin ta
Yesu ya na nufin cewa ya san abin da zai faru. AT: "amma wannan nufin shi don mutane su gan girman Allah domin abin da ikonsa zai yarda min in yi" (Dubi: figs_explicit)
Ɗan Allah
Wannan muhimmin lakabi ne wa Allah. (Dubi: guidelines_sonofgodprinciples)
John 11:5-7
Yesu yana kaunar Matta, da 'yar'uwarta da Li'azaru
Wannan tushen bayani ne. (Dubi: writing_background)
John 11:8-9
Mallam, harwayau Yahudaya na neman ka domin su jefe ka da duwatsu, kuma kana son komawa can?
Wannan magana ya bayyana kamar tambaya ne domin ya nanata cewa almajiran ba su son Yesu ya tafi Urushalima. AT: "Mallam, haƙiƙa ba ka so ka koma can! Yahudawa sun so su jefe ka a loƙacin da ka na wurin!" (Dubi: figs_rquestion)
su Yahudaya
Wannan magana ne na shugabanin Yahudawa wadda su ka yi hamayya da Yesu. AT: " shugabanin Yahudawa" (Dubi: figs_synecdoche)
Ba sa'a goma sha biyu ce ta haske a rana guda ba?
Wannan magana ya bayyana kamar tambaya ne domin karin bayani. AT: "kun san cewa rana ya na da sa'a sha biyu na haske!" (Dubi: figs_rquestion)
Idan mutum ya yi tafiya da rana, ba za ya yi tuntube ba, domin yana gani ta wurin hasken wannan duniya
Mutane da suke tafiya a cikin hasken rana su na iya gani da kyau kuma ba su yin tuntuɓe. "haske" magana ne na "gaskiya." Yesu ya na nufin cewa mutane da suke rayuwa bisa gaskiya su iya yin abubuwan da Allah ya na so su yi" (Dubi: figs_metaphor)
John 11:10-11
Mahaɗin Zance:
Yesu ya cigaba da magana da almajiransa.
idan mutum ya yi tafiya chikin dare
A nan "dare" magana ne da ya na nufin tafiyar mutum da babu hasken Allah. (Dubi: figs_metaphor)
haske ba ya cikinsa
AT: 1) "ba ya iya gani" ko "ba shi da hasken Allah."
Abokinmu Li'azaru ya yi barci
A nan "barci" karin magana ne da ya na nufin Li'azaru ya mutu. Idan ku na da wata hanyar faɗa wannan a harshenku, za ku iya yin amfani da shi a nan. (Dubi: figs_idiom)
amma zan je don In tashe shi daga barci
Kalmomin " tashe shi daga barci" karin magana ne. Yesu ya na bayyana shirinsa na sa Li'azaru ya rayu kuma. Idan ku na da karin magana na wannan a harshen ku, za ku iya amfani da shi ana. (Dubi: figs_idiom)
John 11:12-14
idan barci yake yi
Da shike almajiran ba su fahimci abin da yesu ya na nufi ba, sun ce ko Li'azaru ya na hutawa ne kuma zai warke.
Sai Yesu ya yi masu bayani cewa
"Sai yesu ya gaya masu a kalmomin da za su iya gane"
John 11:15-16
domin ku
"domin amfanin ku"
da bani a wurin domin ku gaskata
"da ba na wurin. Domin wannan za ku iya gaskanta da ni sosai."
wanda ake kira Ɗan tagwaye
AT: "wadda su ke kira Ɗan tagwaye" (Dubi: figs_activepassive)
Dan tagwaye
Wannan sunan na miji ne wadda ya na nufin "yan biyu." (Dubi: translate_names)
John 11:17-20
ya tarar cewa Li'azaru ya rigaya ya yi kwana hudu a kabari
AT: "ya ji cewa mutane sun riga sun sa Li'azaru a cikin kabari har kwana hudu kafin" (Dubi: figs_activepassive)
'yar tafiya marar nisa
"nisar kilomita uku." "filinwasanni" mita dari da tamanin da biyar. (Dubi: translate_bdistance)
game da dan'uwansu
Li'azaru kaninsu ne. AT: "game da kaninsu" (Dubi: figs_explicit)
John 11:21-23
da dan'uwana baya mutu ba
Li'azaru ne kanin. AT: "har yanzu kani na zai rayu" (Dubi: figs_explicit)
Dan'uwanki za ya rayu kuma
Li'azaru ne kanin. AT: "kanin ki zai rayu kuma"(Dubi: figs_explicit)
John 11:24-26
zaya tashi kuma
"zai rayu kuma"
ko ya mutu
A nan "mutu" ya na nufin mutuwa ta jiki.
zai rayu
A nan "rayu" ya na nufin rayuwa ta ruhaniya.
duk wanda yake raye, ya kuma bada gaskiya gare ni, ba zai taba mutu ba
"wadanda su na raye kuma sun gaskanta da ni ba za a raba su daga Allah har abada ba" ko "wadanda su na raye kuma sun gaskanta da ni za su rayu ta ruhaniya tare da Allah har abada"
ba zai taba mutu
A nan "mutu" ya na nufin mutuwa ta ruhaniya.
John 11:27-29
Ta ce masa
"Matta ta ce wa Yesu"
I, Ubangiji, Na gaskata cewa kaine Almasihu, Dan Allah ... zuwa duniya
Matta ta gaskanta cewa Yesu Ubangiji ne, Almasihu, (Mai ceto), Dan Allah.
ta je ta kira yar'uwarta Maryamu
Maryamu kanuwar Matta ne. AT: "ta je ta kira kanuwarta Maryamu" (Dubi: figs_explicit)
Mallam
Wannan lakabi ne da ya na nufin Yesu.
yana kiran ki
"ya ce ki zo"
John 11:30-32
Yanzu Yesu bai rigaya ya shiga kauyen ba
Yahaya ya ba da yanka a labarin domin ya ba da tushen bayani game da inda Yesu yake. (See: writing_background)
faɗi gaban sawayensa
Maryamu ta kwanta ko ta durkusa a sawayen Yesu don ta nuna ladabi.
John 11:33-35
ya yi juyayi a ruhu ya damu kuma ya damu
Yahaya ya hada wadannan jumloli masu ma'ana iri daya domin ya bayyana tsananin wuya da kuma fushi mai yiwuwa da Yesu ya ji. AT: "hankalinsa ya tashi sosai" (Dubi: figs_doublet)
A ina kuka kwantar da shi
Wannan wata hanyar tambaya, "A inane kuka binne shi?" (Dubi: figs_euphemism)
Yesu ya yi kuka
"Yesu ya fara kuka"
John 11:36-37
kaunar
Wannan ya na nufin kaunar yan'uwa ko kaunar mutum wa aboki ko ɗan iyali.
Shi wannan mutum da ya iya ba makaho ganin gari, da bai iya hana wannan mutum mutuwa ba?
Wannan magana ya bayyana kamar tambaya ne domin ya nuna mamakin Yahudawa da cewa Yesu bai warkad da Li'azaru ba. AT: "Ya iya warkad da makaho, ai da ya iya warkad da wannan mutum don kadda ya mutu!" ko "Tun da bai hana mutumin nan daga mutuwa ba, watakila bai warkad da mutumin da an haife shi makaho ba, kamar yadda sun ce ya yi!" (Dubi: figs_rquestion)
bude idanu
AT: "warkad da idanun" (Dubi: figs_idiom)
John 11:38-40
Yanzu, kogo ne an kuma rufe bakinsa da dutse
Yahaya ya tsayar da labarin domin ya kwatanta kabarin da mutanin suka binne Li'aziru. (Dubi: writing_background)
Matta yar'uwar Li'azaru
Matta da Maryamu yayun Li'azaru ne. AT: "Matta, yayar Li'azaru" (Dubi: figs_explicit)
Yanzu jikin ya ruba
"Yanzu za a sami wari" ko "jikin ya na doyi"
Ba na ce maki idan kin gaskata za ki ga daukakar Allah ba?
Wannan magana ya bayyana kamar tambaya ne domin ya nanata cewa Allah zai yi abin ban mamaki. AT: "Na gaya maki cewa indan kin yarda da ni, za ki gan abin da Allah zai yi!" (Dubi: figs_rquestion)
John 11:41-42
Yesu ya daga idanunsa
Wannan karin magana ne da ya na nufin duba sama. AT: "Yesu ya duba sama" (Dubi: figs_idiom)
Uba, na gode maka domin kana ji na
Yesu ya yi addu'a wa Allah domin wadanda suke akewaye da shi su ji addu'ar sa. "Uba, Na gode da ka ji ni" ko "Uba, Na gode da ka ji addu'a na"
Uba
Wannan muhimmin lakabi ne wa Allah. (Dubi: guidelines_sonofgodprinciples)
domin su bada gaskiya cewa kaine ka aiko ni
"Ina so du gaskanta da cewa kaine ka aiko ni"
John 11:43-46
Bayan ya yi wannan magana
"bayan da Yesu ya yi addu'a"
ya daga murya
"ya yi ihu"
kafafunsa da hannayensa na daure da likkafani, fuskarsa kuma na lullube da tsumma
Al'adan biso na wannan lokacin shi ne a ana nada gawa a cikin dogon likkafani. AT: "Wani ya nade likkafani a hannayensa da kafafunsa. Sun kuma daura likkafani a fuskarsa da tsumma" (Dubi: figs_activepassive)
Yesu ya ce masu
Kalmar "masu" ya na nufin mutane da suke wurin kuma sun gan abin al'ajibin.
John 11:47-48
Sai manyan firistoci
"Sai shugabane a cikin firistoci"
Sai
Marubucin ya yi amfani da wannan kalma domin ya gaya wa mai karatun cewa abin da ya faru a farkon Aya 47 abin da ya faru ne 11:45-46.
menene za mu yi?
Wannan ya na nufin cewa mutanin majalisa su na maganar Yesu ne. AT: "me nene za mu yi game da Yesu?" (Dubi: figs_explicit)
duka za su gaskata da shi
Shugabanin Yahudawa sun ji tsoro cewa mutanin za su gwada sa Yesu ya zama sarkin su. AT: "kowa zai yarda da shi su kuma yi wa Romawa tawaye" (Dubi: figs_explicit)
Romawa za su
Wannan magana ne na sojojin Romawa. AT: "sojojin Romawa za su zo" (Dubi: figs_synecdoche)
kwace wurinmu da al'ummar mu
"halaka haikalinmu da al'ummar mu"
John 11:49-50
wani mutum daga cikin su
Wata hanya ne na gabatar da sabon mutum a cikin labarin. Idan ku na da yadda za ku yi shi a harshen ku, za ku iya amfani da shi anan. (Dubi: writing_participants)
baku san komai ba
Wannan zuguiguitawa ne da Kayafas ya yi amfani don ya zage masu sauraransa. AT: "ba ku gane abin da ya na faruwa ba" ko kuma "ku na magana kamar ba ku san komai ba" (Dubi: figs_hyperbole)
a maimakon dukan al'umma ta hallaka
Kayafas ya na nufin cewa sojojin Romawa za su kashe dukka mutanin al'ummar Yahudawa idan an yarda Yesu ya zauna ya kuma sa tawaye. Kalmar "al'umma" magana ne da ya na wakilcin dukkan mutanin Yahudawa. AT: "a maimakon Romawa su kashe dukkan mutanin al'ummar mu" (Dubi: figs_explicit and figs_synecdoche)
John 11:51-53
mutu domin al'ummar
Kalmar "al'umma" magana ne da ya na nufin mutanin al'ummar Isra'ila. (Dubi: figs_synecdoche)
za a tara zuwa daya
Wannan karin magana ne. Kalmar "mutane" ya na a bayyane a mahallin. AT: "za a tara zuwa mutane daya" (Dubi: figs_ellipsis)
'ya'yan Allah
Wannan ya na nufin mutane da sun zama na Allah ta wurin bangaskiya a cikin Yesu kuma 'ya'yan Allah ne ta ruhaniya.
John 11:54-55
tafiya a sarari cikin Yahudawa
A nan "Yahudawa" magana ne na shugabanin Yahudawa kuma "tafiya a sarari" ya na nufin "zama a inda kowa zai iya ganin shi." AT: "zamna a inda dukkan Yahudawa za su iya ganin shi" ko kuma "yi tafiya a sarari a sakanin shugabanin Yahudawa da su ka yi hamayya da shi" (Dubi: figs_synecdoche and figs-metaphor)
yanki
kauyen da su na wujen gari da mutane kadan suke zama.
A can kuma ya zamna da almajiransa
Yesu da almajiransa sun zamnaIfraimu na dan lokaci. AT: "A caan ya zamna da almajiransa na dan lokaci" (Dubi: figs_explicit)
tafi Urushalima
An yi amfani da jumlar "tafi" domin Urushalima ya na tudu fiye da sauran wuraran.
John 11:56-57
Su na neman Yesu
Kalmar "su" ya na nufin mutanin Yahudawa wanda sun tafi Urushalima.
Me kuke tunani? Ba za ya zo idin bane?
Wadannan tambayoyi sun bayyana shakkan cewa Yesu zai zo idin ketarewa. Tambaya na biyu karin magana ne da ya bayyana "kuke tunani."Masu magana su na tunani ko Yesu zai zo idin tun da akwai alamar kamar shi. "Watakila Yesu ba zai zo idin ba. Ya na iya jin tsoro kar a kama shi!" (Dubi: figs_rquestion and figs_ellipsis)
Babban firist
Wannan tushen bayani ne da ya na fasara dalilin da Yahudawa masubi sun yi tunani ko Yesu zai zo idin ko babu. Idan harshenku ya na da wata hanyar sa tushen bayani, sai ayi amfani da shi anan. (Dubi: writing_background)
John 12
John 12:1-3
Muhimmin Bayani:
Yesu ya na cin abinci a Baitany a lokacin da Maryamu ta shafa kafafunsa da turare.
Kwana shidda kafin idin ketarewa
Marubucin ya yi amfani da wannan kalmomin domin ya nuna farawan sabon abu. (Dubi: writing_newevent)
ya tada daga matattu
AT: "ya sa shi ya rayu kuma" (Dubi: figs_idiom)
Lita na turare
Za ku iya mai da wannan zuwa awu na zamani. "lita" kusan rabin kilo ne. Ko kuma ku yi amfani da wani abu da zai iya rike yawan turaran. AT: "rabin kilo na turare" ko "kwalbar turare" (Dubi: translate_bweight)
turare
Wannan wata ruwa-ruwan abu ne mai kamshi da kuma kyau ne da an yi shi daga man itace da fure mai kamshi.
nard
Wannan turane ne da an yi shi daga wata fure a cikin duwasun Nepal, China da kuma India. (Dubi: translate_unknown)
Sai gida ya cika da kamshin turaren
AT: "kamshin turarenta ya cika gidan" (Dubi: figs_activepassive)
John 12:4-6
Yahuza Iskariyoti, daya daga cikin almajiransa, wanda zai bashe shi, ya ce
"wadda ya sa an iya kama Yesu"
Me yasa ba a sayar da wannan turare dinari dari uku a ba gajiyayyu ba?
Wannan tambaya ne da ba ya neman amsa. Za ku iya fasara shi kamar babban jumla. AT: "za a iya sayar da wannan turare dinari dari uku a kuma yi amfani da kudin don a taimake talakawa!" (Dubi: figs_rquestion)
dinari dari uku
AT: "dinari dari uku" (Dubi: translate_numbers)
dinari
Dainari kudin azurfa ne da ma'aikaci ya ke samuwa a rana daya. (Dubi: translate_bmoney)
Yanzu ya fadi haka ... zai sata daga daga abin da an sa a ciki
Yahaya ya bayyana dalilin da ya sa Judas ya yi tambaya game da talakawa. Idan harshen ku ya na da wata hanyar nuna tushen bayani, zaku iya yin amfani da shi a nan. (Dubi: writing_background)
Ya fadi haka ba don ya damu da talakawa ba, amma domin shi barawo ne
"ya fadi haka domin shi barawo ne. Bai damu da talakawa ba"
John 12:7-8
Ku kyale ta ta ajiye abinda ta tanada domin jana'iza ta
Yesu Ya na nufin cewa ayukkan matan ya nuna cewa su na saurarar mutuwa da bisonsa. AT: "Bar ta ta nuna yadda take kauna na! A haka ne ta shirya biso na" (Dubi: figs_explicit)
Talakawa suna tare da ku a koyaushe
Yesu ya na nufin cewa akwai hanyoyi dayawa da za a iya taimakon talakawa. AT: "za a sami talakawa koyaushe a sakaninku, kuma za ku iya taimake su a duk loƙacin da ku na so" (Dubi: figs_explicit)
ba zan kasance da ku koyaushe ba
A haka, Yesu ya na nufin zai mutu. AT: "Amma ba zan kasance tare da ku kayaushe ba" (Dubi: figs_explicit)
John 12:9-11
Yanzu
An yi amfani da wannan kalma domin a sa layi a ainahin labarin. Anan Yahaya ya yi magana game da sabon kungiyar mutane da sun zo Betini daga Urushalima. (Dubi: writing_background)
domin saboda shi
Rayuwar Li'azarus ne ya sa Yahudawa dayawa suka gaskanta da Yesu.
bada gaskiya ga Yesu
Wannan ya na nufin cewa mutanin Yahudawa dayawa sun na ba da gaskiya ga Yesu" (Dubi: figs_explicit)
John 12:12-13
Kashegari
Marubucin ya yi amfani da wadannan kalmomi domin ya fara sabon abu. (Dubi: writing_newevent)
babban taro
"babban taron mutane"
Hosanna
Wannan na nufin "Bari Allah ya cece mu yanzu"
albarka
Wannan ya bayyana yadda Allah ya na so ya sa abubuwa masu kyau su faru wa mutum.
zuwa cikin sunan Ubangiji
A nan kalmar nan " suna" magana ne na karfi da ikon mutum. AT: "zuwa kamar wakilin Ubangiji" ko "zuwa a cikin sunan Ubangiji" (Dubi: figs_metonymy)
John 12:14-15
Yesu ya sami wani Aholakin jaki
A nan Yahaya ya ba da tushen bayani cewa Yesu ya sami jaki. Ya na nufin cewa Yesu zai hawo jaki zuwa Urushalima. AT: "ya sami aholakin jaki sai ya zanna a kai, tafiya zuwa Urushalima" (Dubi: writing_background and figs_explicit)
yadda aka rubuta
AT: "yadda annabawa suka rubuta a cikin nassi"(Dubi: figs_activepassive)
'yar Sihiyona
"'Yar Sihiyona" ya na nufin mutanin Urushalima. AT: "ku mutanin Urushalima" (Dubi: figs_metonymy)
John 12:16
Almajiransa basu fahimci wannan al'amari ba
Anan kalmomin "wannan al'amari" ya na nufin kalmomin da annabi ya rubuta game da Yesu.
loƙacin da aka ɗaukaka Yesu
AT: "loƙacin da Allah ya ɗaukaki Yesu" (Dubi: figs_activepassive)
sun yi masa wadannan abubuwa
Kalmomin "wadannan abubuwa" ya na nufin abin da mutane sun yi a loƙacin da Yesu ya shiga cikin Urushalima a kan jaki (yabon shi da kuma nuna reshen giginya).
John 12:17-19
sun ji cewa ya yi wannan alama
"sun ji wadansu su na ce ya yi wannan alama"
wannan alama
"Alama" abu ne ko abin da ya faru, wadda ya na nuna cewa abin gaskiya ne. A wannan magana, "Alamar" ta da Li'azaru ya nuna cewa Yesu ne mai ceto.
Duba, babu abinda zaku iya yi
Farisawan su na nufin anan cewa ba za a iya hana Yesu ba. AT: "kamar ba za mu iya yin komai don mu hana shi ba" (Dubi: figs_explicit)
kun ga, duniya ta gama bin sa
Farisawa sun yi amfani da wannan zuguiguitawa domin su bayyana mamakin cewa mutane da yawa sun fito don su gan Yesu. AT: "kamar kowa ya na zama almajiransa" (Dubi: figs_hyperbole)
duniya
A nan " duniya" magana ne da ya na wakilcin (cikin zuguiguitawa) dukkan mutanin cikin duniya. Za ku so ku sa shi a bayyane cewa masu sauraran su na iya gane cewa Farisawa su na maganan mutanin Judea ne kadai. (Dubi: figs_metonymy and figs_explicit)
John 12:20-22
Yanzu wadansu Helinawa
Wannan jumla "Yanzu wadansu" ya nuna gabatarwar sabobin mutane a cikin labarin. (Dubi: writing_participants)
suka je sujada a idin
Yahaya ya na nufin cewa wadannan "helinawa" su na tafiya zuwa yabon Allah a loƙacin ketarewa. AT: "don a yabe Allah a idin ketarewa"(Dubi: figs_explicit)
Betsaida
Wannan gari ne a yankin Galili.
suka gaya wa Yesu
Fillibus da Andrawas sun faɗa wa Yesu game da rokon da Helinawa sun yi don su gan shi. AT: "Sun gaya wa Yesu abin da Helinawan sun ce" (Dubi: figs_ellipsis)
John 12:23-24
sa'a ta zo da za'a daukaka Dan mutum
Yesu ya na nufin cewa yanzu ne daidan loƙaci da yakamata Allah ya ɗaukaki Ɗan Mutum ta wurin wahala mai zuwa, mutuwa da tashiwa. AT: "Allah zai ɗaukake ni a loƙacin da in na mutu da kuma tashi" (Dubi: figs_explicit)
Hakika, hakika, Ina ce maku
Fasara shi a yadda harshenku ya na nanata cewa abu na-biye ya na da muhiminci kuma gaskiya ne. Dubi yadda kun fasar "Hakika, hakika" a cikin 1: 51.
in ba kwayar alkama ta fadi kasa ba ta mutu ... za ta bada 'ya'ya masu yawa
A nan "kwayar alkama" ko "iri" magana ne na mutuwa, biso, da kuma tashin Yesu.Yadda ana shuka iri kuma ya na girma zuwa shuka da zai ba da 'ya'ya, haka ne mutane dayawa za so gaskanta da Yesu a bayan an kashe shi, an binne shi, ankuma ta da shi daga mattatu. (Dubi: figs_metaphor)
John 12:25-26
Duk wanda yake son ransa, zai rasa shi
A nan "son ransa" ya na nufin yadda ka na duba rai na jikinka da amfani fiye da rayukan wadansu. AT: "duk wadda ya na ɗaukakar ransa fiye da wadansu ba zai karɓi rai na har abada ba" (Dubi: figs_explicit)
wanda ya ki ransa a duniyan nan za ya kiyaye shi domin rayuwa ta har abada
A nan wanda ya "ki ransa" ya na nufin wanda ya na son ran wadansu fiye da ransa. AT: "duk wanda ya ɗauki rayukan wadansu da muhiminci fiye da ransa zai rayu da Allah har abada" (Dubi: figs_explicit)
inda nike, a can bawana zai kasance kuma
Yesu ya na nufin cewa wadanda sun bauta masa ne za su kasance tare da shi a cikin sama. AT: "Bawa na zai kasance tare da ni a wurin, loƙacin da ina cikin sama" (Dubi: figs_explicit)
Uban zai girmama shi
A nan "Uba" muhimmin lakabi ne wa Allah. (Dubi: guidelines_sonofgodprinciples)
John 12:27-29
to me zan ce? 'Uba, ka cece ni daga wannan sa'a?
Wannan magana ya bayyana kamar tambaya ne. Kodashike Yesu ya so ya ki giciye, ya zaba ya yi biyyaya ga Allah a kuma kashe shi. AT: "Ba zan yi addu'a, 'Uba, ka cece ni gaga wannan sa'a!'" (Dubi: figs_rquestion)
Uba
Wannan muhimmin lakabi ne wa Allah. (Dubi: guidelines_sonofgodprinciples)
wannan sa'a
A nan "wannan sa'a" magana ne da ya na wakilcin loƙacin da Yesu zai sha wahala ya kuma mutu a kan giciye. (Dubi: figs_metonymy)
ɗaukaka sunanka
A nan kalmar "suna" magana ne da ya na nufin Allah. AT: "sa ɗaukakar ka sananne" ko "bayyana ɗaukakar ka" (Dubi: figs_metonymy)
murya ya zo daga sama
Wannan ya na wakilcin maganar Allah. Wadansu loƙaci, mutane su na kin kiran Allah domin suna daraja shi. AT: "Allah ya yi magana daga sammai" (Dubi: figs_metonymy and figs_euphemism)
John 12:30-31
Yanzu za'a shar'anta wannan duniya
A nan "wannan duniya" ya na nufin dukka mutane a cikin duniya. AT: "Yanzu ne loƙaci da Allah zai sharanta dukka mutane" (Dubi: figs_metonymy)
Yanzu za'a kori mai mulkin duniyan nan
A nan "mai mulki" ya na nufin shaidan. AT: "Yanzu ne loƙacin da zan hukunta ikon shaidan da ya na mulkin wannan duniya" (Dubi: figs_activepassive)
John 12:32-33
A loƙacin da an daga ni daga duniya
Yesu ya na nufin giciyewarsa. AT: "A loƙacin da mutane sun daga ni sama a kan giciye" (Dubi: figs_activepassive)
zai jawo dukan mutane zuwa gare shi
Ta wurin giciyensa, Yesu zai tanada hanyar wa kowa don ya gaskanta da shi.
Ya fadi wannan ne domin ya nuna irin mutuwar da za ya yi
Yahaya ya fasara kalmomin Yesu cewa mutane za su giciye shi. AT: "Ya faɗi wannan domin ya sa mutanin su san yadda zai mutu" (Dubi: writing_background)
John 12:34-36
dole ne a daga dan mutum
Jumlar "daga" ya na nufin giciye. Za ku iya fasara shi da karin "a kan giciye." AT: "dole ne a daga dan mutum a kan giciye" (Dubi: figs_ellipsis)
Wanene wannan dan mutum?
AT: 1) "Menene ainahin wannan Ɗan Mutum? ko kuma 2) "Wa ne irin Ɗan Mutum ne ka na magana a kai?"
Yesu ya ce masu, "Nan da lokaci kadan za ku kasance da haske, ku yi tafiya tun haske na tare da ku, kada duhu ya mamaye ku. Wanda ke tafiya cikin duhu, bai san inda za shi ba
A nan "haske" ya na nufin koyarswar yesu da ya bayyana gaskiyar Allah. Yi "tafiya cikin duhu" magana ne da ya na nufin yin rayuwa da ba tare da gaskiyar Allah ba. AT: "Magana ta ya na nan kamar haske ne a gareku, domin ya taimake ku ku fahimci yadda za ku yi rayuwa kamar yadda Allah ya na so ku yi. Ba zan kasance tare da ku sosai ba. Yakamata ku bi dokokina tun ina tare da ku. Idan kun ki magana ta, zai zama kamar tafiya ne a cikin duhu kuma ba za ku iya ganin inda za ku je ba" (Dubi: figs_metaphor)
Ku gaskata ga haske tun yana tare da ku domin ku zama 'ya'yan haske
"Haske" magana ne na koyarswar Yesu da ya bayyana gaskiyar Allah. "'ya'yan haske" magana ne na wadanda sun karba sakon Yesu kuma su na rayuwa a bisa gaskiyar Allah. AT: "Tun ina tare da ku, ku gaskanta da abin da ina koyar maku domin gaskiyar Allah ya kasance da ku" (Dubi: figs_metaphor)
John 12:37-38
Saboda maganar annabi Ishaya ta cika
AT: "domin a cika sakon annabi Ishaya" (Dubi: figs_activepassive)
Ubangiji, wa ya gaskata rahoton mu? Ga wa kuma hannun Ubangiji ya bayyana?
Wannan ya bayyana kamar tambaya ne da ba ya neman amsa domin ya nuna tsoratawar annabin cewa mutanin basu gaskanta da sakon shi ba. AT: "Ubangiji, Da ker ne idan wanni ya gaskanta da sakon mu, kodashike sun gan cewa ka na da ikon cece su!" (Dubi: figs_rquestion)
hannun Ubangiji
Wannan magana ne da ya na nufin ikon ceton Ubangiji. (Dubi: figs_metonymy)
John 12:39-40
ya kuma taurare zuciyarsu ... su kuma sami fahimta da zuciyarsu
A nan "zuciya" magana ne na hankalin mutum. Jumlar "taurare zuciyarsu" magana ne na sa wani ya zama da taurin kai. Kuma, "fahimta da zuciyarsu" ya na nufin "fahimta sosai." AT: "ya sa su taurin kai ... fahimta sosai" (Dubi: figs_metonymy and figs_metaphor)
su kuma juyo
A nan "juyo" magana ne na "tuba." AT: "kuma za su tuba" (Dubi: figs_metaphor)
John 12:41-43
domin kada a kore su daga majami'a
AT: "domin kada mutane su hana su daga tafiya zuwa majami'a. (Dubi: figs_activepassive)
Suna son yabo daga mutane fiye da yabon dake zuwa daga Allah
"Sun so mutane su yaɓe su fiye da yadda sun so Allah ya yaɓe su"
John 12:44-45
Yesu ya yi magana da babbar murya, ya ce
A nan Yahaya ya na nufin cewa taron mutane sun taru domin su ji Yesu ya yi magana. AT: "Yesu ya yi wa taron da suka taru ihu" (Dubi: figs_explicit)
wanda ke gani na, yana ganin shi wanda ya aiko ni
A nan kalmar "shi" ya na nufin Allah. AT: "wanda ya gan ni ya gan Allah, wadda ya aike ni"
John 12:46-47
Mahaɗin Zance:
Yesu ya cigaba da magana da taron.
Na zo ne a matsayin haske
A nan "haske" magana ne na gurbin Yesu. AT: "Na zo ne in nuna gaskiyan" (Dubi: figs_metaphor)
ba za ya yi tafiya cikin duhu ba
A nan "duhu" magana ne na yin rayuwa a rashin sanin gaskiyar Allah. AT: "ba za ya cigaba da makanta a ruhaniya ba" (Dubi: figs_metaphor)
uk wanda ya ji maganata baya gaskata ba, ba ni hukunta shi; gama ban zo in yi wa duniya hukunci ba, amma don in ceci duniya
A nan "yi wa duniya hukunci" ya na nufin hukunci. Yesu bai zo don ya hukunta mutane ba. AT: "idan wani ya ji koyarswa ta ya kuma ki, ban hukunta shi ba. Ban zo don in hukunta mutane ba. Maimako, Na zo ne don in cece wadanda sun gaskanta da ni" (Dubi: figs_explicit)
John 12:48-50
a rana ta karshe
"a lokacin da Allah ya na hukunta zunuban mutane"
Na san umarninsa rai ne madawwami
"Na san cewa kalmomin da ya umurce ni in fada kalmomi ne da ya na ba da rai na har abada"
John 13
John 13:1-2
Muhimmin Bayani:
Ketarewa bai kai ba kuma Yesu ya na tare da almajiransa a abincin dare. Wadannan ayoyin sun bayyana shirin wannan labari, sun kuma ba da tushen bayani game da Yesu da Yahuza. (Dubi: writing_background)
Uba
Wannan muhimmin lakabi ne wa Allah. (Dubi: guidelines_sonofgodprinciples)
Kaunar
Wannan irin kauna ya na zuwa daga Allah ne ya na bisa kyaun mutane, ko bai amfani wani ba. Irin wannan kauna ya na kula da mutane, ko mai abin da sun yi
Iblis ya rigaya ya sa a zuciyar Yahuza Iskariyoti dan Saminu, ya bashe da Yesu
Jumlar "sa a zuciyar" karin magana ne da ya na nufin a sa wani ya yi tunanin wani abu. AT: "Iblis ya riga ya sa Yahuza Iskariyoti, dan Saminu, da yin tunanin cin amanar Yesu" (Dubi: figs_idiom)
John 13:3-5
Mahadin Zance"
Aya uku ya cigaba da gaya mana game da tushen bayani game da abin da Yesu ya sani. Abin ya fara a aya hudu. (Dubi: writing_background)
ya bada kome a hannunsa
A nan "hannunsa" magana ne da ya na nufin iko da karfi. AT: "ya ba ni cikakken iko a komai" (Dubi: figs_metonymy)
ya zo daga wurin Allah, kuma zai koma wurin Allah
Yesu ya saba kasancewa da Uban, kuma zai koma wurin bayan aikinsa a duniya ya kare.
Ya tashi daga cin abincin, ya tube tufafinsa ... ya fara wanke kafafun almajiran
Domin yankin na da kura, al'ada ne wa mai gidan da ya ba da abincin ya ba da bawan da zai wanke kafafun baki.
John 13:6-9
Ubangiji, za ka wanke mani kafa?
Tambayar Bitrus ya nuna cewa bai so Yesu ya wanke mashi kafa. AT: "Ubangiji, ba daidai ba ne ka wanke mani kafa na ba, mai zunubir!" (Dubi: figs_rquestion)
In ban wanke maka ba, ba ka da rabo da ni
Yesu ya yi magana domin ya sa Bitrus ya yarda ya wanke mashi kafa. Yesu ya na nufin cewa dole Bitrus ya yarda Yesu ya wanke masa kafa idan ya na so ya cigaba da zama almajiransa. AT: "Idan na wanke ka, kullum za ka kasance nawa" (Dubi: figs_doublenegatives and figs_explicit)
John 13:10-11
Duk wanda ya yi wanka ba ya da bukata, sai dai a wanke kafafunsa
A nan "wanka" magana ne da ya na nufin cewa Allah ya wanke ruhaniyar mutum. AT: "Idan wani ya riga ya karbi yafewar Allah, yanzu ya kamata ya karbi wankewa daga zunubansa na kullum" (Dubi: figs_metaphor)
Ba dukanku ne ke da tsarki ba
Yesu ya na nufin cewa wadda zai bashe shi, Yahuza, bai gaskanta da shi ba. Don haka Allah bai yafe masa zunubansa ba. AT: "Ba dukkan ku ne kun karbi yafewar Allah ba" (Dubi: figs_explicit)
John 13:12-15
Kun san abin da na yi muku?
Wannan magana ya bayyana kamar tambaya ne don Yesu ya iya bayana muhimincin abin da ya na koyar wa almajiransa. AT: "Ya kamata ku fahimci abin da na yi maku!" (Dubi: figs_rquestion)
kuna kirana, 'Malam, da Ubangiji,'
A nan Yesu ya na nufin cewa almajiransa su na da babban daraja masa. AT: "Kun nuna mani babban daraja a lokacin da kun kira ni "Mallam" da "Ubangiji." (Dubi: figs_explicit)
saboda ku yi yadda na yi maku
Yesu ya na nufin cewa almajiransa su yarda su bi gurbinsa su kuma bauta wa junansu. AT: "ku kuma bauta wa junanku da ladabi" (Dubi: figs_explicit)
John 13:16-18
Hakika, hakika
Dubi yadda kun fasara wannan a cikin 1:51.
fi
wanin da yafi muhiminci ko iko, ko wanin da ya kamata ya sami saukin rayuwa ko dadin rayuwa sosai.
ku masu albarka ne
A nan "albarka" na nufin sa kyaun abubuwa su faru da mutum. AT: "Allah zai albakarkance ka" (Dubi: figs_activepassive)
wannan ne domin Nassi ya cika
AT: "wannan domin nassi ya cika" (Dubi: figs_activepassive)
Shi Wanda ya ci gurasata, ya tayar mani
Jumlar "ci gurasata" anan karin magana ne na wani da ya na yi kamar aboki. Jumlar "tayar" magana ne kuma da ya na nufin mutum da ya zama abokin gaba. Idan ku na da karin magana a harshen ku da ke da wannan ma'ana, za ku iya yin amfani da shi anan. AT: "wadda ya yi kamar shi abokina ne ya koma ya zama makiya na" (Dubi: figs_idiom)
John 13:19-20
Ina fada maku wannan yanzu tun kafin haka ta faru domin sa'adda ta faru
"Ina gaya maku abin da zai faru yanzu kafin ya faru"
ku gaskata Ni ne
"Za ku iya gaskanta cewa ni ne wadda na ce ni ne" ko "Za ku iya gaskanta cewa ni ne mai ceto"
John 13:21-22
damu
damu
Almajiran suka kalli juna, suna juyayin ko akan wa yake magana
"Almajiran sun kalli juna da mamaki: "Wa nene zai ci amanar Yesu?
John 13:23-25
Daya daga cikin almajiransa, wanda Yesu yake kauna
Wannan ya na nufin Yahaya.
a jingine teburi
A zamanin Almasihu, Yahudawa su na yawan cin abinci tare kamar salon Greek, wadda suke zauna a gefe daya a kujeru kanana. (Dubi: figs_explicit)
Yesu, ya ce masa
An dauke kukwance da kai a gefen wani mai cin abinci a salon Greek kamar nuna babban kauna ne a sakaninsu.
John 13:26-27
Yahuza
Wannan ya nuna cewa Yahuza daga kawyen Kerot ne. (Dubi: writing_background)
To bayan gurasar
An fahimci kalmomin "Yahuza ya dauke" a mahalli.
shaidan ya shige shi
Wannan karin magana ne da ya na nufin shaidan ya dauki cikakken shugabancin Yahuza. AT: "Shaidan ya dauke shugabancinsa" ko "Shaidan ya fara umurce shi" (Dubi: figs_idiom)
sai Yesu ya ce masa
A nan Yesu ya na magana da Yahuza.
Abinda kake yi, ka yi shi da sauri
"Ya sauri da abin da ka ke shirin aikatawa!"
John 13:28-30
kuma ya bada wani abu domin gajiyayyu
"je ka ba da kudade wa talakawa."
ya fita nan da nan. Da daddare ne kuwa.
Yahaya ya so ya jawo hankali da cewa Yahuza zai aikata muguntarsa ko ayyukan "duhu" a cikin duhun dare. AT: "ya fita nan da nan cikin duhun dare" (Dubi: writing_background)
John 13:31-33
Yanzu an daukaka Dan mutum, kuma an daukaka Allah a cikinsa
AT: "Yanzu mutane za su ga yadda Ɗan Mutum zai karba daukaka kuma da yadda Allah zai karbi daukaka ta wurin abin da Ɗan Mutum ya ke yi" (Dubi: figs_activepassive)
Allah zai daukaka shi a cikin kansa, kuma zai daukaka shi nan da nan
Kalmar "shi" ya na nufin Ɗan Mutum. Wannan kalmar "kansa" magana ne da ya na nufin Allah. AT: "Allah zai ba da daukaka wa Ɗan Mutum nan da nan" (Dubi: figs_rpronouns)
'Ya'ya kanana
Yesu ya yi amfani da wannan magana "'Ya'ya kanana" domin ya nuna cewa ya na kaunar almajiransa kamar su 'ya'yan shi ne.
kamar yadda na fadawa Yahudawa
A nan "Yahudawa" magana ne na shugabanin Yahudawa da su ka yi hamayya da Yesu. AT: "kamar yadda na fadawa Yahudawa" (Dubi: figs_synecdoche)
John 13:34-35
kauna
Wannan irin kauna ya na zuwa daga Allah ne ya na bisa kyaun mutane, ko bai amfani wani ba. Irin wannan kauna ya na kula da mutane, ko mai abin da sun yi
kowa
Za ku iya sa a bayyane cewa wannan zuguiguitawa ya na nufin mutane da suka gan yadda almajiran sun kaunace juna. (Dubi: figs_hyperbole)
John 13:36-38
bada raina domin ka
"ba da raina" ko "mutu"
Za ka bada ranka domina?
Wannan magana ya bayyana kamar tambaya ne domin karin bayani game maganar Yesu. AT: "Ka ce za ka mutu domina, amma gaskiyan shi ne ba za ka yi ba!" (Dubi: figs_rquestion)
kafin zakara ya yi cara zaka yi musu na sau uku
"za ka ce baka san ni sau uku kafin zakara ya yi cara"
John 14
John 14:1-3
Mahadin Zance:
An cigaba da sashin labarin daga Aya da ta wuce. Yesu ya ja baya a teburin da almajiransa sai ya cigaba da magana da su.
Kada zuciyarku ta bachi
A nan "zuciya" magana ne na cikin mutum. AT: "daina damuwa" (Dubi: figs_metonymy)
A gidan Ubana akwai wurin zama dayawa
"akwai wuraran zama dayawa a gidan Ubana"
A gidan Ubana
Wannan ya na nufin sama, wurin da Allah ya na zama.
Uba
Wannan muhimmin lakabi ne wa Allah. (Dubi: guidelines_sonofgodprinciples)
wurin zama dayawa
Kalmar "daki" ya na iya nufin daki daya, ko babban wurin zama.
zan tafi in shirya maku wuri
Yesu zai shirya wuri a sama wa kowane mutum da ya gaskanta da shi. "Ku" ya na nufin dukka almajiransa. (Dubi: figs_you)
John 14:4-7
yaya za mu san hanyar?
"ta yaya zamu san yadda za mu kai wurin?"
hanya
AT: 1) "hanya zuwa Allah" ko 2) "wadda ya ke kai mutane zuwa wurin Allah." (Dubi: figs_metaphor)
gaskiyan
AT: 1) "mutumin gaskiyan" ko 2) "wadda ya ke fada kalmomin gaskiya game da Allah." (Dubi: figs_metaphor)
ran
Wannan magana ne da ya na nufin cewa Yesu zai iya ba da rai wa mutane. AT: "Wadda zai iya san mutane su rayu" (Dubi: figs_metaphor)
Ba mai zuwa wurin Uba sai ta wurina
Mutane za su iya zuwa wurin Allah su kuma yi rayuwa da shi idan sun gaskanta da Yesu. AT: "Babu wadda zai iya zuwa wurin Uba ya yi rayuwa da shi sai dai ta wurinsa" (Dubi: figs_explicit)
John 14:8-9
Ubangiji, ka nuna mana Uban
"Uba" muhimmin lakabi ne wa Allah. (Dubi: guidelines_sonofgodprinciples)
Ina tare da ku da dadewa, amma har yanzu baka san ni ba, Filibus?
Wannan magana ya bayyana kamar tambaya ne domin a kara nanata kalmomin Yesu. AT: "Filibus, Na kasance tare da ku almajirai na tsawon loƙaci. Ya kamata kun san ni yanzu!" (Dubi: figs_rquestion)zu
Duk wanda ya gan ni, ya ga Uban
Ganin Yesu, wadda shi ne Allah, shi ne ganin Allah Uba. "Uba" muhimmin lakabi ne wa Allah. (Dubi: guidelines_sonofgodprinciples)
Yaya za ka ce, 'Nuna mana Uban'?
Wannan magana ya bayyana kamar tambaya ne domin a nanata maganar Yesu wa Filibus. AT: " Kada ku dinga ce, "nuna mana Uban!'" (Dubi: figs_rquestion)
John 14:10-11
Baka gaskata ... ciki na?
Wannan magana ya bayyana kamar tambaya ne domin a nanata maganar Yesu wa Filibus. AT: "yakamata ka gaskanta ... ciki na." (Dubi: figs_rquestion)
Maganganun da nake fada maku, ba da ikona nake fadi ba
"Abin da ina faɗa maku ba daga ni bane" ko "kalmomin da na faɗa ma ku ba daga ni ba ne"
Maganganun da nake fada maku
Yanzu Yesu ya na magana da dukka almajiransa.
ina cikin Uban, Uban kuma na ciki na
Wannan karin magana ne da ya na nufin Allah Uba kuma Yesu ya na da dangantaka da babu kamarsa. AT: "Ni ɗaya ne da Uba, kuma Uban ya na tare da ni" ko kuma "Ni da Uba na mu na nan kamar ɗaya ne" (Dubi: figs_idiom)
John 14:12-14
Hakika, hakika
Dubi yadda kun fasara wannan a cikin 1:51.
gaskata da ni
Wannan ya na nufin cewa Yesu ne Ɗan Allah.
Duk abinda kuka roka da sunana
A nan "suna" magana ne da ya na wakilcin ikon Yesu. AT: "Duk abin da kun roke ni, da amfani da iko na" (Dubi: figs_metonymy)
domin a daukaka Uban cikin Dan
AT: "don in iya nuna wa kowa yadda Uba na yake" (Dubi: figs_activepassive)
Uba ... Ɗan
Waɗannan muhimmin lakabi ne da ya na kwatanta dangantaka a sakanin Allah da Yesu. (Dubi: guidelines_sonofgodprinciples)
Idan kuka roke ni komai cikin sunana, zan yi shi
A nan "suna" magana ne da ya na wakilcin ikon Yesu. AT: "Idan kun tambaye ni komai kamar masubi na, zan yi shi" ko kuma "Duk abin da kun tambaye ni, zan yi shi domin ku nawa ne" (Dubi: figs_metonymy)
John 14:15-17
ta'aziya
Wannan ya na nufin Ruhu mai Tsarki.
Ruhun gaskiya
Wannan ya na nufin Ruhu mai tsarki wadda ya na koya wa mutane abin da ya ke gaskiya game da Allah.
duniya ba zata iya karba ba
A nan "duniya" magana ne da ya na nufin mutane da su na hamayya da Allah. AT: "mutane da ba su gaskanta ba za su marabshe shi ba" ko kuma "Wadda su na hamayya da Allah ba za su karbe shi ba" (Dubi: figs_metonymy)
John 14:18-20
barku ku kadai ba
Anan yesu ya na nufin cewa ba zai bar almajiran shi kadai ba tare da wadda zai kula da su ba. AT: "barku kadai ba tare da wadda zai kula da ku"(Dubi: figs_explicit)
duniya
A nan "duniya" magana ne da ya na wakilcin mutane da ba na Allah ba. AT: "marasa bi" (Dubi: figs_metonymy)
zaku san cewa ina cikin Ubana
Allah Uba da Yesu sun zauna kamar mutum ɗaya. AT: "za ku san cewa Ubana da Ni ɗaya ne kamar mutum ɗaya"
Ubana
Wannan muhimmin lakabi ne wa Allah. (Dubi: guidelines_sonofgodprinciples)
kuna ciki na, ni ma ina cikin ku
"Ni da Ku muna nan kamar mutum ɗaya"
John 14:21-22
kauna
Wannan irin kauna ya na zuwa daga Allah ne ya na bisa kyaun mutane, ko bai amfani wani ba. Irin wannan kauna ya na kula da mutane, ko mai abin da sun yi
shi wanda ke kauna ta Ubana zai kaunace shi
AT: "Ubana zai kaunace duk wadda ya kaunace ni" (Dubi: figs_activepassive)
Yahuza (ba Iskariyoti ba)
Wannan ya na nufin wani almajiri wadda sunan sa Yahuza, ba ga almajiri wadda ya na daga ƙaukyen Keriot wadda ya ci amanar Yesu ba. (Dubi: translate_names)
meyasa za ka nuna kanka a gare mu
Anan kalmar "nuna" ya na nufin bayyana al'ajibin Yesu. AT: "Don me za ka bayyana kanka wa mu kadai" ko " Don me ba za ka bar mu mu gan al'ajibin ka ba?"
ba ga duniya ba
A nan "duniya" magana ne da ya na wakilcin mutane da suna hamayya da Allah. AT: "ba ga wadda ba su gaskanta da Allah ba" (Dubi: figs_metonymy)
John 14:23-24
Idan wani ya na kauna ta, zai kiyaye maganata
"Wadda ya na kauna na zai yi abin da na gaya masa ya yi"
za mu zo wurinsa mu zauna tare da shi
Uban da Ɗan za su yi rayuwa da waɗanda su na biyayya da abin da Yesu ya umurta. AT: "za mu zo mu zauna da shi, mu kuma samu dangantaka da shi" (Dubi: figs_explicit)
Maganar da kuke ji ba daga gareni take ba, amma daga Uba wanda ya aiko ni
"Abubuwan da na gaya maku ba abubuwan da na su in faɗa da kaina ba ne"
Maganar
"sakon"
da kuke ji
Loƙacin da Yesu ya ce "ku" ya na magana da dukkan almajiransa ne.
John 14:25-27
cikin sunana
A nan kalmar "suna" magana ne da ya na wakilcin ƙarfi da ikon Yesu. AT: "saboda ni" (Dubi: figs_metonymy)
duniya
"duniya" magana ne da ya na wakilcin mutane da ba su kaunar Allah. (Dubi: figs_metonymy)
Kada zuciyarku ta baci, kuma kada ku tsorata
A nan "zuciya" magana ne da ya na wakilcin cikin mutum. AT: "Don haka ku daina damuwa, kuma kada ku ji tsoro" (Dubi: figs_metonymy)
John 14:28-31
kauna
Wannan irin kauna ya na zuwa daga Allah ne ya na bisa kyaun mutane, ko bai amfani wani ba. Irin wannan kauna ya na kula da mutane, ko mai ne abin da sun yi
Za ni wurin Uban
A nan Yesu ya na nufin cewa zai koma wurin Uban shi. AT: "Zan koma wurin Uban" (Dubi: figs_explicit)
Uban ya fi ni girma
A nan Yesu ya na nufin cewa Uban ya na da babban iko fiye da Ɗan sai kuma Ɗan ya na kan duniya. AT: "Uban ya na da babban iko fiye da yadda na ke da shi a nan" (Dubi: figs_explicit)
mai mulkin wannan duniya
A nan "mai mulki" ya na nufin Shaidan. Dubi yadda kun fasara wannan a cikin 12:31. AT: "Shaidan da yake mulkin wannan duniya"
mai mulki ... na zuwa
A nan Yesu ya na nufin cewa Shaidan ya na zuwa ya yi mashi hari. AT: "shaidan ya na zuwa ya yi mani hari" (Dubi: figs_explicit)
domin duniya ta sani
A nan "duniya" magana ne wa mutane da ba na Allah ba ne. AT: "domin waɗanda ba na Allah ba su iya sani" (Dubi: figs_metonymy)
Uban
Wannan muhimmin laƙani ne wa Allah. (Dubi: guidelines_sonofgodprinciples)
John 15
John 15:1-2
Mahaɗin Zance:
An cigaba da sashin labarin daga Aya da ta wuce. Yesu ya ja baya a teburin da almajiransa sai ya cigaba da magana da su.
Nine itacen inabi na gaskiye
A nan "itacen inabi" karin magana ne. Yesu ya kwatanta kansa da itacen inabi. Shi ne tushen rai da ya na sa mutane su rayu a hany da ya cancanci Allah. AT: "ina nan kamar itacen inabi da yake ba da 'ya'ya mai kyau. (Dubi: figs_metaphor)
Ubana kuwa shi ne manomin
"manomin" karin magana ne. "Manomi" mutum ne wadda ya na kula da itacen inabi don ya gan ya ba da 'ya'ya. AT: "Ubana ya na nan kamar manomi" (Dubi: figs_metaphor)
Ubana
Wannan muhimmin lakabi ne wa Allah. (Dubi: guidelines_sonofgodprinciples)
Yakan cire duk wani rashe a cikina da ba ya bada 'ya'ya
A nan "duk wani rashe" ya na wakilcin mutane, kuma "'ba da 'ya'ya ya na wakilcin yin rayuwa a hanyar da Allah yake so. (Dubi: figs_metaphor)
cire
"sare da cire"
gyara kowane rashe
"shirya kowane rashe"
John 15:3-4
Kun rigaya kun tsarkaka saboda maganar da na yi muku
Maganar da ana nufi a nan shi ne "tsarkakar reshe" wadda an riga an "gyara." AT: "Kamar an riga an gyara ku kuma ku tsarkakan reshe ne domin kun yi biyayya da abin da na koya maku"(Dubi: figs_metaphor)
Ku
Kalmar "ku" ya na nufin almajiran Yesu. (Dubi: figs_you)
Ku zauna ciki na, Ni kuma cikin ku
"Idan kun zauna a hade da ni, zan zauna a hade da ku"
sai kun zauna ciki na
Ta wurin zauna a cikin Almasihu, wadda sun zama na shi su na dogara akan shi don kokai. AT: "sa dai kun kasance a hade da ni ku kuma dogara da ni ma komai"
John 15:5-7
Ni ne itacen inabi, ku ne rassan
"itacen inabi" magana ne da ya na wakilcin Yesu. "rassan" magana ne da ya na wakilcin wadda su na gaskanta da Yesu sun kuma zama na shi. AT: "Ina nan kamar itacen inabi, kuma ku na nan kamar rassan da ya ke a haɗe da itacen inabi"(Dubi: figs_metaphor)
Shi wadda ya zauna a ciki na, ni kuma cikin sa
A nan Yesu ya na nufin cewa masubinsa su na a haɗe da shi kamar yadda ya na a haɗe da Allah. AT: "shi wadda ya zauna a haɗe da ni, kamar yadda ina zaune a haɗe da Ubana" (Dubi: figs_explicit)
yana bada 'ya'ya dayawa
Maganan ana ya na nufi reshe mai ba da 'ya'ya wadda ya na wakilcin maibi da ya na sa Allah jin dadi. Yadda reshe da ya na a haɗe da itacen inabi ya na ba da 'ya'ya dayawa, waɗanda sun kasance a haɗe da Yesu za su yi abubuwa dayawa da zai sa Allah ya ji dadi. AT: "za ku ba da 'ya'ya dayawa" (Dubi: figs_metaphor)
akan jefar da shi kamar reshe, ya bushe
Maganan anan shi ne reshe mara ba da 'ya'ya da ya na wakilcin waɗanda ba su a haɗe da Yesu. AT: "mai gyaran itacen inabi ya na jefad da shi kamar reshe kuma ya na bushe" (Dubi: figs_metaphor and figs_activepassive)
a na kone su
AT: "wutan ya na kone su" (Dubi: figs_activepassive)
roki duk abinda kuke so
Yesu ya na nufin cewa dole masubi su roki Allah ya amsa adduwowinsu. AT: "roki Allah komai da ku ke so" (Dubi: figs_explicit)
za a kuwa yi maku
AT: "zai yi maku" (Dubi: figs_activepassive)
John 15:8-9
Ta haka ake ɗaukaka Ubana
AT: "Ya na sa mutane su girmama Ubana" (Dubi: figs_activepassive)
cewa ku bada 'ya'ya dayawa
A nan "ya'ya" magana ne na yin rayuwa don ku sa Allah ya ji dadi. AT: "loƙacin da kun yi rayuwa a hanya da zai ya na sa shi jin dadi" (Dubi: figs_metaphor)
almajiraina ne
"nuna cewa ku almajirai na ne"
Kamar yadda Ubana ya kaunace ni, haka Ni ma na kaunace ku
Yesu ya ba da kaunar da Allah Uba ya na da shi mashi da kuma wadda su na kaunar sa. Anan "Uba" muhimmin lakabi ne wa Allah. (Dubi: guidelines_sonofgodprinciples)
Zauna cikin kaunata
"cigaba amincewa da kuana ta"
John 15:10-11
Idan kun kiyaye dokokina, za ku zauna cikin kaunata kamar yadda Na kiyaye dokokin Ubana, na kuma zauna cikin kaunarsa
Loƙacin da masubin Yesu sun yi masa biyayya, su na nuna kaunar su masa. AT: "loƙacin da kun yi abubuwan da na gaya maku ku yi, ku na zama a cikin kauna ta, kamar yadda ina yin biyayya ga Ubana da kuma zama a cikin kaunarsa" (Dubi: figs_explicit)
Ina gaya maku wadannan al'amura domin farincikina ya kasance a cikin ku
"Na riga na gaya ma ku wannan abubuwa domin ku sami irin farinciki da ina da shi"
domin farincikinku ya zama cikakke
AT: "domin ku zama cikakke da farinciki" ko "domin farincikinku kada ya rasa komai" (Dubi: figs_activepassive)
John 15:12-13
Babu wanda ke da kaunar da tafi haka
Irin wannan kauna ya na zuwa ne daga Allah kuma ya na son amfanin sauran, ko bai amfane shi ba. Irin wannan kauna ya na lura da sauran, ko da me sun yi. AT: "Ba za ku samu babban kauna kamar wannan ba"
Rai
Wannan ya na nufin rai na jiki.
John 15:14-15
domin na sanar da ku duk abinda na ji daga wurin Ubana
"Na gaya maku dukka abin da Uba na ya gaya ma ni"
John 15:16-17
Ba ku zabe ni ba
Yesu ya na nufin cewa ba masubin sa ne suka zeba da kansu cewa za su zama almajiransa ba. AT: "Ba ku zaba cewa ku zama almajirai na ba" (Dubi: figs_explicit)
je ku bada 'ya'ya
A nan "'ya'ya" magana ne da ya na wakilcin rayuwa da ya na girmama Allah. AT: "yi rayuwar da zai girmama Allah" (Dubi: figs_metaphor)
'ya'yanku kuma su tabbata
"cewa abin da ku ka yi ya dadai har abada"
duk abinda kuka roki Uba a cikin sunana, zai baku
Anan "suna" magana ne da ya na wakilcin ikon Yesu. AT: "Domin ku nawa ne, duk abin da kun roke Uban, zai ba ku shi" (Dubi: figs_metonymy)
Uban
Wannan muhimmin lakabi ne wa Allah. (Dubi: guidelines_sonofgodprinciples)
John 15:18-19
In duniya ta ki ku ... don haka duniya take kin ku
Yesu ya yi amfani da wannan kalmar "duniya" a waɗannan ayoyin kamar magana ne da ya na nufin mutane da ba na Allah ba kuma suna hamayya da shi. (Dubi: figs_metonymy)
kauna
Wannan ya na nufin kauna na mutum, kauna na 'yan'uwa ko kauna wa aboki ko ɗan gida.
John 15:20-22
Ku tuna da maganar da na yi muku
A nan "maganar" sako ne na Yesu. AT: "Ku tuna da sakon da na faɗa ma ku" (Dubi: figs_metonymy)
saboda sunana
A nan "saboda sunana" magana ne da ya na wakilcin Yesu. Mutane za su sa masubinsa su sha wahala domin su nashi ne. AT: "domin ku nawa ne" (Dubi: figs_metonymy)
Da ban zo na yi masu magana ba, da basu da zunubi, amma yanzu, basu da wata hujja don zunubinsu
Yesu ya na nufin anan cewa ya ba da sakon Allah tare da wadda ba su yarda da shi ba. AT: "Domin na zo in gaya masu sakon Allah, ba su da hudja a loƙacin da Allah zai hukunta su domin zunubansu" (Dubi: figs_explicit)
John 15:23-25
Shi wadda ya ki ni ya ki Ubana ... sun gani, sun kuma ki ni da Ubana duka.
Kin Allah Ɗan shi ne kin Allah Uba.
Uba
Wannan muhimmin laƙani ne wa Allah. (Dubi: guidelines_sonofgodprinciples)
Da ban yi ayyukan da babu wanda ya taba yinsu a cikin su ba, da basu da zunubi, amma
AT: "Domin na yi a cikinsu ayyukan da ba bu wani da ya yi. da basu da zunubi, kuma" (Dubi: figs_doublenegatives)
da basu da zunubi
"ba su da wani zunubi." Dubi yadda kun fasara wannan a cikin 15:22.
domin a cika maganar da ke rubuce a cikin shari'arsu
"Maganar" dukka sakon Allah. AT: "domin a cika annabci a cikin shari'arsu " (Dubi: figs_activepassive and figs_metonymy)
shari'a
Wannan ya na nufin Tsohon Alkawari, wadda ya na da dukka dokokin Allah ga mutane.
John 15:26-27
Mai Ta'aziya
Wannan ya na nufin Ruhu mai Tsarki. Dubi yadda an fasara wannan a cikin 14:16.
zai iko ... daga wurin Uban ... Ruhun gaskiya ... zai bada shaida a kai na
Allah Uba ya aiko Allah Ruhu don ya nuna wa duniya cewa Yesu shi ne Allah Ɗa.
Ruhun gaskiya
Wannan lakabi ne wa Ruhu mai Tsarki. AT: "Ruhun da ya na faɗan gaskiya game da Allah da kuma ni" (Dubi: figs_explicit)
Ku ma kuna bada shaida
A nan "shaida" ya na nufin gaya wa sauran game da Yesu. AT: "Ku kuma dole ne ku gaya wa kowa abin da kun sani game da ni" (Dubi: figs_explicit)
farkon
A nan "farko" magana ne da ya na nufin farkon ranakun hidimar Yesu. AT: "Daga farkon ranakun da na fara koya wa mutane da kuma yin abubuwan a'lajibi" (Dubi: figs_metonymy)
John 16
John 16:1-2
Mahaɗin Zance:
An cigaba da sashin labarin daga Aya da ta wuce. Yesu ya ja baya a teburin da almajiransa sai ya cigaba da magana da su.
kada kuyi tuntube
A nan jumlar "tuntube" ya na nufin daina gaskantawa a cikin Yesu. AT: "ba za ku daina gaskanta da ni ba domin wahalan da za ku gani" (Dubi: figs_explicit and figs_activepassive)
Amma, sa'a tana zuwa, wadda idan wani ya kasheku, zai yi zaton aikin Allah yake yi
"zai faru wata rana cewa mutum zai kashe ku, zai kuma yi tunani cewa ya na yin abu mai kyau ne wa Allah."
John 16:3-4
Za suyi haka ne kuwa domin ba su san Uban ko ni ba
Za su kashe waɗansu masubi domin ba su san Allah Uba ko Yesu ba.
Uba
Wannan muhimmin laƙani ne wa Allah. (Dubi: guidelines_sonofgodprinciples)
loƙacin da zasu faru yayi
A nan "loƙaci" magana ne da ya na nufin loƙacin da mutane za su tsananta masubin Yesu. AT: "a loƙacin da za su sa ku ku sha wahala" (Dubi: figs_metonymy)
a cikin farko
Wannan magana ne da ya na nufin ranakun farko na hidimar Yesu. AT: "a loƙacin da kun fara bi na"(Dubi: figs_metonymy)
John 16:5-7
bakin ciki ya cika zuciyarku
A nan "zuciya" magana ne na cikin mutum. AT: "yanzu ku na bakin ciki" (Dubi: figs_metonymy)
Domin in ban tafi ba, Mai Ta'aziyya ba zai zo gare ku ba
AT: "sadai in na tafi ne mai Ta'aziyya zai zo wurin ku"(Dubi: figs_doublenegatives)
Mai Ta'aziyya
Wannan lakabi wa Ruhu mai Tsarki wadda zai kasance da almajiran bayan ya tafi. Dubi yadda kun fasar wannan a cikin 14: 26.
John 16:8-11
Mai Ta'aziyyar zai fadarkar da duniya a kan zunubi ... adalci ... domin za ni wurin Uba
Loƙacin da Ruhu mai Tsarki ya zo, ya fara nuna wa mutane cewa su masu zunubi ne.
duniya
Wannan magana ne da ya na nufin mutane a cikin duniya. (Dubi: figs_metonymy)
Game da zunubi, domin basu gaskata da ni ba
"su na da laifin zunubi domin ba su gaskanta da ni ba"
Game da adalci, domin za ni wurin Uba, kuma ba za ku sake ganina ba
"Idan na koma wurin Allah, kuma ba su gan ni kuma ba, za su san cewa na yi abubuwa da ya kamata"
game da hukunci kuma, domin an yanke wa mai mulki duniyan nan hukunci
"Allah zai rike su da alhaki kuma zai hukunta su domin zunuban su, kamar yadda zai hukunta Shaidan, wadda yake mulki da wannan duniya"
mai mulkin wannan duniya
A nan "mai mulki" ya na nufin Shaidan. Dubi yadda kun fasara wannan a cikin 12:31. AT: "Shaidan da ya na mulki da wannan duniya"
John 16:12-14
abubuwa da zan gaya maku
"su sako maku" ko "kalmomi maku"
Ruhu na gaskiya
Wannan suna ne wa Ruhu mai Tsarki wadda zai gaya wa mutane game da Allah.
zai bishe ku a cikin dukkan gaskiyar
"Gaskiya" ya na nufin gaskiya ta ruhaniya. AT: "zai koya maku dukkan gaskiyar ruhaniya da za ku so ku sani"(Dubi: figs_explicit)
zai faɗa duk abin da ya ji
Yesu ya na nufin cewa Allah Uba zai yi magana wa Ruhun. AT: "zai faɗa dukka abin da Allah ya gaya mashi ya faɗa" (Dubi: figs_explicit)
zai dauko abubuwa dake nawa ya sanar da ku
A nan "abubuwan hankali" ya na nufin koyarwan Yesu da babban ayyuka. AT: "zai bayyana maku cewa abin da na faɗa, na kuma yi hakika gaskiya ne" (Dubi: figs_explicit)
John 16:15-16
Ruhun zai dauko daga abin da yake nawa ya sanar da ku
Ruhu mai Tsarki zai gaya wa mutane cewa magana da ayyukan Yesu gaskiya ne. AT: "Ruhu mai Tsarki zai gaya wa kowa cewa magana na da ayyuka na gaskiya ne" (Dubi: figs_explicit)
A dan lokaci kadan
"jim kaɗan" ko "kafin loƙaci dayawa su wuce"
bayan dan loƙaci kadan kuma
"kuma, kafin loƙaci dayawa su wuce"
John 16:17-18
Muhimmin Bayani:
Wannan ɗan fashi ne a maganar Yesu a yayin da almajiran su ka tambaye juna game da abin da Yesu ya na nufi.
Bayan dan loƙaci kadan ba zaku gan ni ba
Almajiran ba su gane cewa wannan ya na nufin mutuwar Yesu a kan giciye ba.
bayan dan loƙaci kadan kuma zaku gan ni
AT: 1) Wannan na iya nufin tashiwar Yesu ko 2) Wannan na iya nufin zuwan Yesu a loƙacin karshe.
Uban
Wannan muhimmin laƙani ne wa Allah. (Dubi: guidelines_sonofgodprinciples)
John 16:19-21
Wato kuna tambayar juna ne abinda nake nufi da cewa, ... gan ni'?
Yesu ya yi amfani da wannan tambaya domin almajiransa su yi binbini da abin da ya gaya masu, domin ya iya fasara a gaba. AT: "Ku na tambayan junanku abin da ina nufi loƙacin da na ce, ... gan ni." (Dubi: figs_rquestion)
Hakika, hakika, ina gaya maku
Fasara wannan a yadda harshenku na nanata cewa abin da yake bi ya na da muhiminci kuma gaskiya ne. Dubi yadda kun fasara wannan a cikin 1:51.
amma duniya za ta yi farin ciki
A nan "duniya" magana ne wa mutane da suke hamayya da Yesu. AT: "amma mutane da suke hamayya da Yesu za su yi farin ciki" (Dubi: figs_metonymy)
amma bakin cikinku zai koma farin ciki
AT: "amma bakin cikinku zai zama murna" ko "amma daga baya a maimakon yin bakin ciki za ku yi murna sosai" (Dubi: figs_activepassive)
John 16:22-24
zuciyar ku za ta yi farin ciki
Anan "zuciya" magana ne na cikin mutum. AT: "za ku yi murna sosai" ko "za ku yi farin ciki sosai" (Dubi: figs_metonymy)
komai kuka roki Uba a cikin sunana zai ba ku shi
A nan kalmar "suna" magana ne da ya na nufin mutuntaka da ikon Yesu. AT: "idan kun roki komai na Uban, zai ba ku domin ku nashi ne"(Dubi: figs_metonymy)
cikin sunana
A nan "suna" magana ne da ya na nufin mutuntaka da ikon Yesu. Uban zai ɗaukaki rokon masubi domin dangantakar su da Yesu. AT: "domin ku masubi na ne" ko " a iko na" (Dubi: figs_metonymy)
farin cikin ku ya zama cikakke
AT: "Allah zai ba ku babban farin ciki" (Dubi: figs_activepassive)
John 16:25
cikin karin magana
"a harshen da babu sauƙin ganewa"
sa'a tana zuwa
"ba da jumawa ba zai faru"
gaya maku a sarari game da Uba
"gaya ma ku game da Uban a hanyar da za ku gane da kyau."
John 16:26-28
zaku yi roko a cikin sunana
A nan "suna" magana ne na mutumtaka da ikon Yesu. AT: "za ko roka domin ku nawa ne" (Dubi: figs_metonymy)
Uba da kansa yana kaunarku, domin kun kaunace ni
idan mutum ya na kaunar Yesu, Ɗan, su na kuma kuanar Uban, domin Uban da Ɗan ɗaya ne.
Daga wurin Uban na fito ... zan bar duniya in koma wurin Uba
Bayan mutuwarsa da tashin sa, Yesu zai koma wurin Allah Uba.
Daga wurin Uban na fito ... in koma wurin Uba
A nan "Uba" muhimmin laƙani ne wa Allah. (Dubi: guidelines_sonofgodprinciples)
John 16:29-31
kun gaskanta yanzu?
Wannan magana ya bayyana kamar tambaya ne domin ya nuna cewa Yesu ya yi mamaki cewa almajiran sa yanzu ne sun shirya su gaskanta da shi. AT: "don haka, yanzu ne kun gaskanta da ni! (Dubi: figs_rquestion)
John 16:32-33
za a warwatsa ku
AT: "sauran za su watsar da ku" (Dubi: figs_activepassive)
Uba yana tare da ni
Wannan muhimmin lakabi ne wa Allah. (Dubi: guidelines_sonofgodprinciples)
domin a ciki na ku sami salama
A nan salama" ya na nufin salama na ciki. AT: "domin ku samu salama na ciki don dangantakar ku da ni" (Dubi: figs_explicit)
na yi nasara da duniya
A nan "duniya" ya na nufin damuwowi da tsanantawa da masubi za su sha daga waɗanda suke hamayya da Allah. AT: "na yi nasara da damuwowin wannan duniya" (Dubi: figs_metonymy)
John 17
John 17:1-2
Mahaɗin Zance:
An cigaba da sashin labarin daga Aya da ta wuce. Yesu ya na ta magana da almajiransa, amma yanzu ya far addu'a ga Allah.
ya tada idanunsa zuwa samai
Wannan karin magana ne da ya na nufin duba sama. AT: "ya dubi sama ga sarari" (Dubi: figs_idiom)
samai
Wannan ya na nufin sarari.
Uba ... ka ɗaukaka Ɗanka, domin Ɗan ya ɗaukaka ka
Yesu ya roki Allah Uba don ya girmama shi domin ya iya ba da ɗaukaka wa Allah.
Uba ... Ɗan
Waɗannan muhimmin lakabi ne da su na kwatanta dangantaka sakanin Allah da Yesu.(Dubi: guidelines_sonofgodprinciples)
sa'a ta zo
A nan kalmar "sa'a" magana ne da ya na nufin loƙaci ne wa Yesu da zai sha wahala ya kuma mutu. AT: "loƙaci ya kai da zan sha wahala in kuma mutu" (Dubi: figs_metonymy)
dukkan 'yan adam
Wannan ya na nufin dukka mutane.
John 17:3-5
Wannan ne rai madawwami ... san ka, Allah makadaici na gaskiya, da ... Yesu Almasihu
Rai madawwami shi ne sanin Allah makadaici na gaskiya, Allah Uba da Allah Ɗa.
aikin da ka ba ni in yi
A nan "aiki" magana ne da ya na nufin hidimar Yesu gabadaya. (Dubi: figs_metonymy)
Uba, ka ɗaukaka ni ... da ɗaukaka wadda ni ke da ita tare da kai tun kafin a yi duniya
Yesu ya na da ɗaukaka da Allah "kafin a yi duniya" domin Yesu ne Allah Ɗan. "Uba, ka ba ni ɗaukaka ta wurin kawo ni zuwa gabanka kamar yadda muke kafin mu yi duniya" (Dubi: figs_explicit)
Uba
Wannan muhimmin laƙani ne wa Allah. (Dubi: guidelines_sonofgodprinciples)
John 17:6-8
Na bayyana sunanka
A nan "suna" magana ne da ya na nufin Allah. AT: "Na koya masu game da kai da kuma abin da kake" (Dubi: figs_metonymy)
daga duniya
A nan "duniya" magana ne da ya na nufin mutanen duniya da sun yi hamayya da Allah. Wannan ya na nufin cewa Allah ya raba masubi ta ruhaniya daga mutanen da basu gaskanta da shi ba. (Dubi: figs_metonymy)
kiyaye maganarka
Wannan karin magana ne da ya na nufin biyayya. AT: "bi koyarswan ka" (Dubi: figs_idiom)
John 17:9-11
Ba na addu'a domin duniya
A nan kalmar "duniya" magana ne da ya na nufin mutanen da sun yi hamayya da Allah. AT: "Ba na addu'a wa waɗanda ba na ka na" (Dubi: figs_metonymy)
cikin duniya
Wannan magana ne da ya na nufin kasancewa a duniya da kuma kasancewa a cikin mutane da suka yi hamayya da Allah. AT: "a cikin mutane da ba na ka ba" (Dubi: figs_metonymy)
Ya Uba mai Tsarki, ka adanasu cikin ... domin su zama daya ... kamar yadda muke daya
Yesu ya roki Uban ya adana waɗanda sun gaskanta da shi domin su iya samin dangantaka da Allah.
ka adanasu cikin sunanka da ka ba ni
A nan kalmar "suna" magana ne na karfi da ikon Allah. AT: "ka adanasu da kyau a cikin karfi da ikonka, wadda ka ba ni" (Dubi: figs_metonymy)
John 17:12-14
na adanasu acikin sunanka
A nan "suna" magana ne da ya na nufin karfi da kiyayewar Allah. AT: "Na adanasu da kiyayewarka" (Dubi: figs_metonymy)
ko daya kuwa daga cikinsu ba ya bace ba, sai dai dan hallakar nan
"wadda an hallakar a cikin su shi ne ɗan hallaka kadai"
dan hallakar nan
Wannan ya na nufin Yahuza, wadda ya bashe Yesu. AT: "wadda tun da dadewa ka zaba ka hallakar" (Dubi: figs_explicit)
domin Nassi ya cika
AT: "domin a cika annabci game da shi a cikin nassi" (Dubi: figs_activepassive)
domin farin cikina ya zama cikakke a zukatansu
AT: "domin ku iya basu babban farin ciki" (Dubi: figs_activepassive)
Na ba su maganarka
"Na faɗa masu sakon ka"
duniya ... domin su ba na duniya ba ne ... ni ba na duniya ba ne
A nan "su" duniya" magana ne da ya na nufin mutanen da sun yi hamayya da Allah. AT: "Mutanen da sun yi hamayya da ku sun tsane masubi na domin su ba na waɗanda ba su gaskanta ba ne, kamar yadda ni ba na su ba"(Dubi: figs_metonymy)
John 17:15-17
duniya
A cikin wannan magana, "duniya" magana ne na mutane da suka yi hamayya da Allah. (Dubi: figs_metonymy)
tsare su daga mugun nan
Wannan ya na nufin Shaidan. AT: "kiyaye su daga Shaidan, mugun nan" (Dubi: figs_explicit)
kebe su domin kanka cikin gaskiya
Ana iya sa a bayyane dalilin kebe su. Jumlar "ta gaskiya" anan ya na wakilcin ta wurin koyar da gaskiyan. AT: "Sa su su zama mutanen ka ta wurin koya masu gaskiyan" (Dubi: figs_explicit)
maganarka gaskiya ce
"Sakon ka gaskiya ne" ko "Abin da ka faɗa gaskiya ne"
John 17:18-19
cikin duniya
A nan cikin "duniya" magana ne da ya na nufin mutane da suke zama a cikin duniya. AT: "ga mutanin duniya" (Dubi: figs_metonymy)
domin su ma kansu a kebe su gareka cikin gaskiya
AT: "domin su kebe kansu da gaskiye ma ka"(Dubi: figs_activepassive)
John 17:20-21
waɗanda zasu gaskata da ni ta wurin maganarsu
"waɗanda za su gaskanta da ni domin su na koyarswa game da ni"
za su zama ɗaya kamar yadda kai, ya Uba, ka ke ciki na, ni kuma na ke cikin ka. Ina roko suma su kasance a cikinmu
Waɗanda sun gaskanta da Yesu sun zama daya da Uba da kuma Ɗan loƙacin da sun ba da gaskiya.
John 17:22-23
Ɗaukakar da ka bani, ita nake basu
"Na ɗaukaka masubi na kamar yadda kun ɗaukaka ni"
domin su zama daya, kamar yadda mu ke daya
AT: "domin ku hada su kamar yadda kun hada mu" (Dubi: figs_activepassive)
domin su kammalu cikin zama daya
"domin su zama ɗaya cikakke"
domin duniya ta sani
A nan "duniya" magana ne da ya na nufin mutanin da ba su san Allah ba. AT: "domin dukka mutane su sani" (Dubi: figs_metonymy)
kaunace
Wannan irin kauna ya na zuwa daga Allah ne ya na bisa kyaun mutane, ko bai amfani wani ba. Irin wannan kauna ya na kula da mutane, ko mai abin da sun yi
John 17:24
inda nake
A nan "inda nake" ya na nufin sama. AT: "da ni a sama" (Dubi: figs_explicit)
domin su dubi ɗaukakata
"domin su gan girma na"
kafin halittar duniya
A nan Yesu ya na nufin lokaci kafin halitta AT: "kafin halitta duniya" (Dubi: figs_explicit)
John 17:25-26
Uba mai adalci
A nan "Uba" muhimmin lakabi ne. (Dubi: guidelines_sonofgodprinciples)
duniya ba ta san ka ba
"duniya" magana ne na mutanin da ba na Allah ba. AT: "waɗanda ba naka ba ne ba su san yadda ka ke ba"(Dubi: figs_metonymy)
Na sanar masu da sunanka
Kalmar "suna" ya na nufin Allah. AT: "Na bayyana maku yadda ka ke" (dubi: figs_metonymy)
kauna ... kaunar
Wannan irin kauna ya na zuwa daga Allah ne ya na bisa kyaun mutane, ko bai amfani wani ba. Irin wannan kauna ya na kula da mutane, ko mai abin da sun yi
John 18
John 18:1-3
Muhimmin Bayani:
Aya 1-2 ya ba da tushen bayani na abin da zai faru. Aya 1 ya faɗa inda an yi, kuma Aya 2 ya ba da tushen bayani game da Yahuza. (Dubi: writing_background)
Bayan Yesu ya fadi wadannan maganganu
Marubucin ya yi amfani da wannan kalmomi domin a nuna farkon sabon abu. (Dubi: writing_newevent)
kwarin Kidiron
Kwarin ne a Urushalima da ya ke raba Dutsen haikali daga Dutsen Olives. (Dubi: translate_names)
inda wani lambu ya ke
Wannan taron itacunan zaitun ne. AT: "inda akwai taron itacunan zaitun" (Dubi: figs_explicit)
John 18:4-5
Sai Yesu, da ya san duk abinda ke faruwa da shi
"Sai Yesu, wadda ya san komai da ya yi kusa ya faru da shi"
Yesu Banazare
"Yesu, mutumin daga Nazare"
Ni ne
Kalmar "shi" bayani ne a wannan littafi. AT: "Ni ne shi" (Dubi: figs_explicit)
wadda ya bashe shi
"wadda ya ba da shi"
John 18:6-7
fadi a kasa
Mazan sun fadi a kasa saboda ikon Yesu. AT: "fadi a kasa saboda ikon Yesu" (Dubi: figs_explicit)
John 18:8-9
Wannan kuwa domin maganar daya fada ta cika
A nan "duniya" ya na nufin kalmomin da Yesu ya yi addu'a. AT: "Wannan ya faru domin a cika kalmomin da ya faɗa a loƙacin da ya na yin addu'a wa Ubansa" (Dubi: figs_explicit and figs_activepassive)
John 18:10-11
Malkus
Malkus bawa ne na babban firist. (Dubi: translate_names)
kubenta
murfin wuka mai tsini, don wukan kar ya yanka mai shi
kada in sha kokon da Uba ya ba ni?
Wannan ya bayyana kamar tambaya ne domin a kara nanata jimlar Yesu. AT: "Dole ne in sha daga kokon da Uban ya ba ni!" (Dubi: figs_rquestion)
kokon
A nan "kokon" magana ne da ya na nufin wahala da dole ne Yesu ya jure. (Dubi: figs_metaphor)
Uba
Wannan muhimmin lakabi ne wa Allah. (Dubi: guidelines_sonofgodprinciples)
John 18:12-14
Yahudawa
A nan "Yahudawa" magana ne na shugabanin Yahudawa wadda sun yi hamayya da Yesu. AT: "shugabanin Yahudawa" (Dubi: figs_synecdoche)
suka kama Yesu, suka daure shi
Sojoji suka daure hanayen Yesu domin a hana shi kuɓucewa. AT: "sun kama Yesu sun kuma daura shi domin a hana shi kuɓucewa" (Dubi: figs_explicit)
John 18:15-16
Almajirin nan kuwa sananne ne ga babban firist, sai ya shiga tare da Yesu
AT: "Yanzu babban firist din ya san wannan almajiran don haka ya iya ya shiga tare da Yesu"(Dubi: figs_activepassive)
Sai aya almajirin da ya ke sananne ga babban firist
AT: "Sai ɗayan almajirin, wadda babban firist ya sani" (Dubi: figs_activepassive)
John 18:17-18
kai ma ba kana cikin almajiran mutumin nan ba?
Wannan ya bayyana kamar tambaya ne domin ya sa baiwan ta iya bayana maganar ta da hankali. AT: "Kai ma ɗaya ne daga almajiran mutumin nan da an kama! Ba kai ba ne? (Dubi: figs_rquestion)
Yanzu, barorin da dogaran Haikali suna tsaye a wurin, sun kuwa hura wutar gawayi, suna jin dumi, gama ana sanyi
Waɗannan su bayin babban firist ne da kuma dogaran haikali. AT: "An yi tsanyi, sai bayin babban firist da kuma dogaran haikali su yi shirya wutan gawayi sai sun tsaya su na ɗuma kansu a kewaye da shi" (Dubi: figs_explicit)
Yanzu
An yi amfani da wannan kalma anan domin a sa fashi daga ainahin labarin domin Yahaya ya iya kara bayani game da mutane da suke ɗuma kansu a kewaye da wuta. (Dubi: writing_background)
John 18:19-21
babban firist
Wannan kefas ne. Dubi 18:13
game da almajiransa da koyarwarsa
Anan "koyarswansa" ya na nufin abin da Yesu ya yi ta koya wa mutane. AT: "game da almajiransa da abin da ya koya wa mutane" (Dubi: figs_explicit)
na yi wa duniya magana a bayyane
Za ku iya sa wannan a bayyane cewa kalmar "duniya" magana ne na mutane da sun ji koyarswan Yesu. Anan zuguiguitawar "duniya" ya nanata cewa Yesu ya yi magana a bayyane. (Dubi: figs_explicit and figs_metonymy and figs_hyperbole)e.
in da Yahudawa duka sukan taru
A nan "dukka Yahudawa" zuguiguitawa na da ya na nanata cewa Yesu ya yi magana a inda duk wadda zai ji zai iya jin shi. (Dubi: figs_hyperbole)
Don me kake tambaya ta?
Wannan magana ya bayyana kamar tambaya ne domin a kara bayani a abin da Yesu ya na faɗa. AT: "Kadda ku dinga yi mun wannan tambaya!" (Dubi: figs_rquestion)
John 18:22-24
'Kana amsa wa babban firist haka?
Wannan ya bayyana kamar tambaya ne domin karin nanaci. AT: "ba haka ne ya kamata ka amsa babban firist ba!" (Dubi: figs_rquestion)
ka bada shaida akan abin da ba daidai ba
"gaya mani abin da na faɗa da ba daidai ba"
In kuwa dai dai na fada, to, dan me za ka nushe ni?
Wannan magana ya bayyana kamar tambaya ne domin a kara nanata abin da Yesu ya na faɗa. AT: "Inda na faɗa abin da daidai ne kadai, kada ku dinga nushe na!" (See: figs_rquestion)
John 18:25-27
kai ma ba cikin almajiransa ka ke ba?
Wannan magana ya bayyana kamar tambaya ne domin a kara nanatawa. AT: "Kai ma ɗaya daga cikin almajiransa ne!" (Dubi: figs_rquestion)
ban gan ka tare da shi a lambun ba?
Wannan magana ya bayyana ne kamar tambaya domin karin nanaci. A nan "shi" ya na nufin Yesu. AT: "Na gan ku tare da mutumin da an kama a cikin taron itacen zaitun! ko ba haka?" (Dubi: figs_rquestion and figs_explicit)
Bitrus ya sake musunta
A nan Ya na nufin cewa Bitrus ya yi musan sanin da kuma zama tare da Yesu. AT: "Bitrus ya kuma musanta cewa ya san Yesu ko ya yi zama tare da shi" (Dubi: figs_explicit)
nan da nan kuwa zakara yayi cara
A nan ana zaton cewa mai karatun zai tuna cewa Yesu ya ce Bitrus zai musanta shi kafin zakara yayi cara. AT: "yadda Yesu ya ce zai faru" (Dubi: figs_explicit)
John 18:28-30
Daga wurin Kayafa kuma suka kai Yesu
A nan ya na nufin cewa su na kai Yesu gidan Kafaya. AT: "Sai suka tafi da Yesu daga gidan Kayafa" (Dubi: figs_explicit)
ba su shiga fadar Gwamnan ba, wai don kada su kazantu
Bilatus ba Bayahude ba ne, don haka indan shugabanin Yahudawa sun shiga cikin fadar sa, za su kazantu. Da wannan ya hana su yin hidimar ketarewa. AT: "su kansu sun tsaya a wajen fadar Bilatus domin Bilatus ɗan Al'umma ne. Ba su so su zama da kazanta" (Dubi: figs_explicit and figs_doublenegatives)
idan da mutumin nan bai yi mugun abu ba, me zai sa mu yi kararsa a wurin ka
AT: "Wannan mutumin nan ya na aikata mugun abu, shi ya sa mun kawo maka don hukunci"(Dubi: figs_doublenegatives)
yi kararsa
Wannan jumla ya na nufin ba ma makiya.
John 18:31-32
Yahudawa su kace masa
A nan "Yahudawa" magana ne na shugabanin Yahudawa da suka yi hamayya da Yesu sun kuma kama shi. AT: "Su shugabanin Yahudawan suka ce masa" (Dubi: figs_synecdoche)
ba mu da ikon zartar da hukuncin kisa akan kowa
Bisa ga dokan Romawa, Yahudawa ba su iya kashe mutum. AT: "Bisa ga dokan Romawa, ba za mu iya kashe mutum ba" (Dubi: figs_explicit)
don a cika maganar da Yesu yayi
AT: "domin a cika abin da Yesu ya faɗa a farko"(Dubi: figs_activepassive)
ta kwatanta irin mutuwar da zai yi
"bisa ga yadda zai mutu"
John 18:33-35
Ni ba Bayahude bane, ko kuwa?
Wannan magana ya bayyana kamar tambaya ne domin Bilatus ya iya nanata cikakken rashin son abubuwan al'adun mutanen Yahudawa. AT: "To, hakika ni ba Bayahude ba ne, kuma ban damu da waɗannan zancen ba!" (Dubi: figs_rquestion)
jama'arka
"'yan'uwanka Yahudawa"
John 18:36-37
Mulkina ba na duniya nan ba ne
A nan "duniya" magana ne na mutane da sun hamayya da Yesu. AT: 1) "Mulki na ba na duniya ba ne" ko kuma 2) "Ba na son umurnin wannan duniya domin in yi mulki kamar sarkinsu" ko kuma "Ba daga wannan duniya ne ina da ikon zaman sarki ba." (Dubi: figs_metonymy)
domin kada a bashe ni ga Yahudawa
AT: "a kuma hana shugabanin Yahudawa daga kama ni" (Dubi: figs_activepassive)
Na zo cikin wannan duniya
A nan "duniya" magana ne da na nufin mutanen da suke cikin duniya. (Dubi: figs_synecdoche)
bada shaida game da gaskiya
A nan "gaskiya" ya na nufin game da Allah. AT: "gaya wa mutane gaskiya game da Allah" (Dubi: figs_explicit)
wadda ya ke na gaskiya
Wannan karin magana ne da ya na nufin kowane mutum da ya na kaunar gaskiya game da Allah.(Dubi: figs_idiom)
muryata
A nan "murya" magana ne da ya na nufin kalmomin da Yesu ya yi. AT: "abubuwan da na faɗa" ko "ni"(Dubi: figs_synecdoche)
John 18:38-40
Menene gaskiya?
Wannan magana ya bayyana kamar tambaya ne domin ya nuna yadda Bilatus ya yarda da cewa ba bu wadda ya san gaskiya. AT: "Ba bu wadda zai san menene gaskiya!" (Dubi: figs_rquestion)
ba wannan mutum ba, sai dai Barabbas
Wannan karin magana ne. AT: "Ba bu! Kada ku sake wannan mutum! Ku sake Barabbas a maimako" (Dubi: figs_ellipsis)
Barabbas din nan kuwa dan fashi ne
A nan Yahaya ya ba da tushen bayani game da Barabbas. (Dubi: writing_background)
John 19
John 19:1-3
Mahaɗin Zance:
An cigaba da sashin labarin daga Aya da ta wuce. Yesu ya na tsaye a gaban Bilatus a yayin da Yahudawa suke zargin shi.
Sai Bilatus yayi wa Yesu bulala
Bilatus bai duke Yesu da kansa ba. Anan "Bilatus" magana ne na sojojin da Bilatus ya umurta su duki Yesu. AT: "Sai Bilatus ya sa sojoin su duke Yesu" (Dubi: figs_synecdoche)
Ranka ya dade, sarkin Yahudawa
A nan amfani da gaisuwan "ranka ya dade" da hanu a sama a gaishe da Caesar ne kadai. A yayin da sojojin su na amfani da kayoyi da kaya irin na sarauta su na yi wa Yesu ba'a, da mamaki ne cewa ba su gane wai a hakika shi sarki ne ba. (Dubi: figs_irony)
John 19:4-6
ban same shi da wani laifi ba
Bilatus ya faɗi wannan so biyu domin ya nu na bai yarda cewa Yesu ba shi da laifi ba. Bai so ya hukunta shi. AT: "ban gan dalilin hukunta shi ba" (Dubi: figs_explicit)
rawanin ƙaya ... kaya irin na sarauta
Rawanin da kaya irin na sarauta kaya ne da sarakuna ne kadai suke sa. Sojojin su yi wa Yesu sutura haka domin su yi mashi ba'a. Dubi 19: 2.
John 19:7-9
Yahudawa suka amsa masa
A nan "Yahudawa" magana ne na shugabanin Yahudawa da suka yi hamayya da Yesu. AT: "Shugabanin Yahudawa suka amsa Bilatus" (Dubi: figs_synecdoche)
ya cancanci mutuwa domin ya mai da kansa Ɗan Allah
An hukunta Yesu har ga mutuwa a kan giciye domin ya ce shi ne "Ɗan Allah."
Ɗan Allah
Wannan muhimmin lakabi ne wa Allah. (Dubi: guidelines_sonofgodprinciples)
John 19:10-11
Ba zaka yi mani magana ba?
Wannan magan ya bayyana kamar tambaya ne. A nan Bilatus ya bayyana mamakinsa cewa Yesu bai yi amfani da loƙacin don ya kare kansa ba. AT: "Ban iya yarda cewa kana kin magana da ni ba!" ko "Amsa ni!" (Dubi: figs_rquestion)
Baka san ina da iko in sake ka ba, kuma in gicciye ka?
Wannan magana ya bayyana domin karin nanaci. AT: "Ya kamata ka san cewa zan iya sake ka ko kuma in umurce sojoji na su giciye ka!" (Dubi: figs_rquestion)
iko
A nan "iko" magana ne da ya na nufin iya yin wani abu ko kuma sa abu ya faru. (Dubi: figs_metonymy)
Da ka da iko a kaina sai dai in an baka daga sama
AT: "kun na iya aikata ba da son rai na ba saboda Allah ya sa ku" (Dubi: figs_doublenegatives and figs_activepassive)
daga sama
Wannan hanya ne na daraja Allah.
mika ni mini
Wannan jumla anan na nufin mika wa makiya.
John 19:12-13
Da jin haka
A nan " jin haka" na nufin amsar Yesu. AT: "A loƙacin da Bilatus ya ji amsar Yesu" (Dubi: figs_explicit)
Bilatus yayi kokari a sake shi
"yi kokari" a asali ya nuna cewa Bilatus ya yi kokari " ƙwarai ko kuma "sake" don a saki Yesu. AT: "ya yi kokari ƙwarai don a sake Yesu" ko "ya yi ta kokari don a sake Yesu" (Dubi: figs_explicit)
amma sai Yahudawa suka tada murya
A nan "Yahudawa" magana ne da ya na nufin shugabanin Yahudawa da suka yi hamayya da Yesu. A cikin ainahin, " tada murya" ya na nuna cewa sun yi ta ihu. AT: "amma shugabanin Yahudawa suka cigaba da yin ihu" (Dubi: figs_synecdoche and figs_explicit)
kai ba abokin Kaisar
"kana hamayya da Kaisar"
maida kansa sarki
"ya ce shi na sarki"
ya fito da Yesu waje
A nan "shi" na nufin Bilatus kuma magana ne na "Bilatus ya umurce sojojin." AT: " ya umurce sojojin su kawo Yesu waje" (Dubi: figs_synecdoche)
zauna
Mutane masu daraja kamar Bilatus su ke zaune a loƙacin da su na yin aiki, sai mutane da ba su da daraja sosai su na tsaye.
a kan kujeran shari'a
Wannan kujera ne na musamman da mutum mai daraja kamar Bilatus ya ke zauna akai a lokacin da ya na yin hukunci. Idan harshenku ya na da yadda za a kwatanta wannan abu, za ku iya yin amfani da shi a anan.
a inda ake kira "Dakalin shari'a," amma
Wannan dakalin dutse ne da mutane masu daraja ake yarda su je. AT: "a wurin da mutane sun kira Dakalin shari'a, amma" (Dubi: figs_activepassive)
Yahudanci
Wannan ya na nufin harshen da mutanen Israi'la suke yi.
John 19:14-16
Yanzu
Wannan magana ya sa fashi a cikin labarin domin Yahaya ya iya ba da bayani game da idin ketarewa mai zuwa da rana. (Dubi: writing_background)
sa'a ta shidda
"kusan tsakar rana"
Bilatus yace wa Yahudawan
A nan "Yahudawa" magana ne da ya na nufin shugabanin Yahudawa wadda sun yi hamayya da Yesu. AT: "Bilatus ya ce wa shugabanin Yahudawan" (Dubi: figs_synecdoche)
In gicciye sarkin ku?
A nan "in" magana ne da ya na nufin sojojin Bilatus wadda zai yi gicciyewan. AT: "Ku na so in gaya wa sojoji na cewa su gicciye sarkin ku a kan gicciye?" (Dubi: figs_synecdoche)
Sai Bilatus ya mika Yesu domin su gicciye shi
A nan Bilatus ya ba da umurni da sojojin don su gicciye Yesu. AT: "Bilatus ya sa sojojin su gicciye Yesu" (Dubi: figs_explicit and figs_activepassive)
John 19:17-18
wurin da ake kira "Wurin kwakwalluwa"
AT: "zuwa wurin da mutane suke kira "Wurin kwakwalluwa," (Dubi: figs_activepassive)
waada a Yahudanci kuma ana kira "Golgota".
Yahudanci harshen mutanene Isra'ila ne. AT: "waada a ke kira a Yahudanci "Golgota."
mutum biyu tare da shi
Wannan karin magana ne. AT: "sun kuma gicciye shi da waɗansu barayi a kan su gicciyensu" (Dubi: figs_ellipsis)
John 19:19-20
Bilatus kuwa ya rubuta wata alama a kan gicciyen
A nan "Bilatus" magana ne na mutumin da ya yi rubutu a kan alaman. Anan "a kan gicciye" ya na nufin gicciyen Yesu. AT: "Bilatus ya kuma umurce wani ya rubuta a alama ya kuma sa shi a kan gicciyen Yesu" (Dubi: figs_synecdoche)
A nan an rubuto: YESU BANAZARE, SARKIN YAHUDAWA
AT: "Sai mutumin ya rubuto kalmomin: Yesu Banazare, sarkin Yahudawa" (Dubi: figs_activepassive)
wurin da aka gicciye Yesu
AT: "wurin da sojojin suka gicciye Yesu" (Dubi: figs_activepassive)
Alamar kuwa an rubuta ta da Yahudanci, da Romanci, da Helenanci
AT: "wadda ya shirya alama ne ya rubuto kalmomin a harshuna uku: Yahudanci, da Romanci, da Helenanci" (Dubi: figs_activepassive)
Romanci
Wannan harshe ne na gwamnatin Romawa.
John 19:21-22
Sai manyan firistocin yahudawa sukace wa Bilatus
Manyan firistocin sun koma zuwa wurin fadan Bilatus don su yi zangazanga game da maganganun a alaman. AT: "Manyan firistocin sun koma wurin Bilatus sai ya ce" (Dubi: figs_explicit)
Abinda na rubuta na rubuta kenan
Bilatus ya na nufin cewa ba zai canza kalmomin a kan alaman ba. AT: "Na riga na rubuto abin da na ke so in rubuta, kuma ba zan canza ta ba" (Dubi: figs_explicit)
John 19:23-24
Muhimmin Bayani:
A karshen aya 24 an yi fashi daga ainahin labari a yayin da Yahaya faɗa yadda wannan abu ya ciika nassi. (Dubi: writing_background)
da kuma alkyabbar
sun kuam dauke alyabbarsa." Sojojin sun ajiye alkyabbar dabam, ba su raba shi ba. AT: "sun ajiye alkyabbar dabam" (Dubi: figs_explicit)
mu jefa kuri'a a kan ta mu gani ko wanene zai dauke ta
Sojojin za su yi caca da alkyabbar kuma wadda ya ci ne zai dauka rigan. AT: "mu yi caca da alkyabbar sai wadda ya ci ne zai samu ya ajiye"(Dubi: figs_explicit)
domin a cika nassi cewa
AT: "Wannan ya cika nassi da ya ce" ko "Wannan ya faru ne domin ya sa nassi ya zama gaskiya"
jefa kuri'a
Hakane sojojin su ka raba kayan Yesu a sakaninsu. AT: "sun yi caca"
John 19:25-27
almajirin nan da yake kauna
Wannan Yahaya ne, marubucin wannan bishara.
Mace, dubi, dan ki
A nan kalmar "ɗan" karin magana ne. Yesu ya na son almajiransa, Yahaya, ya zama kamar ɗa wa uwarsa. AT: "Mace, ga mutumin da zai zama kamar ɗa maki" (Dubi: figs_metaphor)
Dubi, mahaifiyarka
A nan kalmar "uwa" karin magana ne. Yesu ya na son uwarshi ta zama kamar uwa wa almajiransa, Yahaya. AT: "Yi tunanin wannan macen kamar uwarka ce" (Dubi: figs_metaphor)
Daga wannan sa'a
"daga wannan loƙaci"
John 19:28-30
da sanin cewa komai ya kammala
AT: "ya san cewa ya yi komai da Allah ya aike shi ya yi" (Dubi: figs_activepassive)
gora cike da ruwan inabi mai tsami na ajiye a wurin
AT: "Wani ya ajiye awurin gorar ruwan inabi mai tsami" (Dubi: figs_activepassive)
ruwa mai tsami
"ruwa mai daci"
sun sa
A nan "su" na nufin masu gadin Romawa.
soso
karamin abu wadda na iya jikuwa har ya kuma rike ruwa
a kan sandan hissop
"a kan rashe a tushe da ake kira hissop"
ya sunkuyar da kansa ya kuwa saki ruhunsa
Yahaya ya na nufin cewa Yesu ya ba da Ruhunsa wa Allah. AT: " ya sunkuyar da kansa ya kuwa ba wa Allah ruhunsa" ko kuma "ya sunkuyar da kansa ya mutu" (Dubi: figs_explicit)
John 19:31-33
Yahudawan
A nan "Yahudawa" magana ne na shugabanin Yahudawa da suka yi hamayya da Yesu. AT: "shugabanin Yahudawa" (Dubi: figs_synecdoche)
ranar shirye shirye ne
Wannan lokaci ne kafin idin ketarewa da mutane su na shirya abinci don idin ketarewa.
kakkarye kafafunsu kuma ya saukar da su
AT: "kakkarye kafafun mutanen da an yi masu hukunci an kuma saukar da jikunansa daga su gicciye" (Dubi: figs_activepassive)
waɗanda aka gicciye tare da Yesu
AT: "wadda an gicciye shi kusa da Yesu" (Dubi: figs_activepassive)
John 19:34-35
Wanda ya ga wannan
Wannan jimla ya ba da tushen bayani ga labarin. Yahaya ya na faɗa wa masu karatu cewa ya na wurin kuma za mu iya gaskanta abin da ya rubuto. (Dubi: writing_background)
ya shaida, shaidarsa kuwa gaskiya ce
"Shaida" ya na nufin faɗa abin da wani ya gani. AT: "ya faɗa gaskiya game da abin da ya gani"(Dubi: figs_explicit)
saboda ku ma ku gaskanta
A nan "gaskanta" ya na nufin sa yardan mu a Yesu. AT: "domin ku sa yardan ku a Yesu" (Dubi: figs_explicit)
John 19:36-37
domin a cika nassi
AT: "ciki magana ne da wani ya rubuto a cikin nassi" (Dubi: figs_activepassive)
Babu ko ɗaya daga cikin kasusuwansa da za'a karya
Wannan magana ne daga Zabura 34. AT: "ba bu wadda zai karya kasusuwansa" (Dubi: figs_activepassive)
Zasu dube shi wanda suka soka
Wannan magana ne da Zechariah 12.
John 19:38-39
Yusufu na Arimatiya
Arimatiya karamin gari ne. AT: "Yusufu daga garin Arimatiya" (Dubi: translate_names)
saboda tsoron Yahudawa
A nan "Yahudawa" magana ne na shugabanin Yahudawa da suka yi hamayya da Yesu. AT: " saboda tsoron shugabanin Yahudawa" (Dubi: figs_synecdoche)
ko zai iya ya ɗauke jikin Yesu
Yahaya ya na nufin cewa Yusufu na Arimatiya ya na so ya binne jikin Yesu. AT: "izini don a ɗauke jikin Yesu daga gicciye" (Dubi: figs_explicit)
Nikodimu
Nikodimu ɗaya ne daga cikin Firistoci wadda sun gaskanta da Yesu. Dubi yadda kun fasara wannan a cikin 3:1.
mur da al'ul
Waɗannan abubuwan kamshi ne da mutane na shirya gawa don biso.
wajen nauyin awo lita dari
Za ku iya sa wannan a awu na zamani. "lita" na nan kamar rabin kilo. AT: "kamar kilo 33 a nauyi" (Dubi: translate_bweight)
dari ɗaya
"100" (Dubi: translate_numbers)
John 19:40-42
Yanzu a wurin da aka gicciye shi kuwa akwai wani lambu ... ba'a taba binne kowa ba
A nan Yahaya ya sa fashi a cikin labarin domin a ba da tushen bayani game da inda kabarin da za a binne Yesu yake. (Dubi: writing_background)
Yanzu a wurin da aka gicciye shi kuwa akwai wani lambu
AT: "Yanzu a wurin da an gicciye Yesu akwai lambu" (Dubi: figs_activepassive)
wadda ba'a taba sa kowa ba
AT: "wadda mutane ba su binne kowa ba" (Dubi: figs_activepassive)
Da yake ranar shirye shirye ce ta Yahudawa
Bisa shari'an Yahudawa, ba bu wadda zai yi aiki bayan rana ya fadi ranar Juma'a. Farkon Asabar da kuma ketarewa. AT: "An yi kusa a fara idin ketarewa a yamman" (Dubi: figs_explicit)
John 20
John 20:1-2
Muhimmin Bayani:
Wannan ne ranar ta mako bayan da an binne Yesu.
ranar farko ta mako
"Lahadi"
ta tarar an kawar da dutsen
AT: "ta tarar cewa wani ya kawar da dutsen" (Dubi: figs_activepassive)
almajirin nan da Yesu ke kauna
Wannan jumla ya bayyana a yadda Yahaya kira kansa a cikin littafinsa. Anan kalmar "kauna" ya na nufin kaunar yan'uwa ko kauna wa abokai ko ɗan iyali.
Sun dauke Ubangiji daga kabarin
Maryamu Magadaliya ta yi tunani cewa wani ya sata jikin Ubangiji. AT: "Wani ya riga ya ɗauka jikin Ubangiji daga kabari" (Dubi: figs_explicit)
John 20:3-5
ɗayan almajirin
Yahaya ya nuna kaskancin shi ta wurin kiran kansa anan "ɗayan almajirin," a maimakon saka sunansa.
fita
Yahaya ya na nufin cewa waɗannan almajiran su na tafiya zuwa wurin kabarin. AT: "ruga daga kabarin" (Dubi: figs_explicit)
likkafanin lillin
Waɗannan kayakin bison Yesu ne da mutane sun kinsa jikin Yesu.
John 20:6-7
fallen kuma da yake kansa
A nan "kansa" na nufin Yesu." AT: "kayan da wani ya rufe fuskan Yesu da shi" (Dubi: figs_activepassive)
amma aka linkeshi ya kuma ajiyu da kansa
AT: "amma wani ya riga ya linkeshi ya kuma sa a gefe, dabam daga likkafanin lillin" (Dubi: figs_activepassive)
John 20:8-10
ya gani, sai ya ba da gaskiya
Da ya gan cewa ba komai a kabarin, ya ba da gakiya cewa Yesu ya tashi daga matattu. AT: "ya gan waɗannan abubuwa sai ya fara gaskantawa cewa Yesu ya tashi daga matattu" (Dubi: figs_explicit)
Har yanzu basu san nassin ba
Anan kalmar "su" ya na nufin almajiran da ba su fahimci nissin da ya ce Yesu zai tashi kuma ba. AT: "Har yanzu almajiran ba su fahimci nassin ba" (Dubi: figs_explicit)
tashi
zama rayeye kuma
daga matattu
Daga dukka waɗanda sun riga sun mutu. Wannan magana ya kwatanta dukka matattu a cikin duniya.
sake koma gida kuma
Almajiran sun cigaba da zama a Urushalima. AT: "sun koma inda suke zama a cikin Urushalima" (Dubi: figs_explicit)
John 20:11-13
Ta ga mala'iku guda biyu cikin fari
Mala'ikun sun sa fararen kaya. AT: "ta ga mala'iku guda biyu cikin fararen kaya" (Dubi: figs_explicit)
Sukace mata
"Sun tambaye ta"
Domin sun dauke Ubangijina
"Domin sun dauke jikin Ubangijina"
ban kuwa san inda suka ajiye shi ba
"ban kuwa san inda suka ajiye shi ba"
John 20:14-15
Yesu yace mata
"Yesu ya tambaye ta"
Maigida, ko kaine ka dauke shi
A nan kalmar "shi" na nufin Yesu. AT: "idan ka dauke jikin Yesu" (Dubi: figs_explicit)
gaya mani inda ka sa shi
"gaya mani inda ka sa shi"
zan dauke shi
Maryamu Magadaliya ta na so ta samu jikin Yesu don ta binne kuma. AT: "zan samu jikin in kuma binne kuma" (Dubi: figs_explicit)
John 20:16-18
Rabboni
Kalmar "Rabboni" ya na nufin mallam a Aramaik, harshen da Yesu da almajiran sa suke yi.
'yan'uwa
Yesu ya na nufin almajiransa ne da ya yi amfani kalmar "'yan'uwa."
zan je wurin Ubana da Ubanku, Allahna da kuma Allahnku
Yesu ya tashi daga matattu ya kuma faɗi cewa zai je sama, zuwa wurin Ubansa, wadda shi ne Allah. AT: "Na yi kusa in koma sama domin in kasance da Ubana da kuma Ubanku, zuwa wadda shi ne Allahna da kuma Allahnku" (Dubi: figs_explicit)
Ubana da Ubanku
Waɗannan muhimmin lakabi ne da ya kwatanta dangantaka a sakanin Yesu da Allah, da kuma masubi da Allah. (Dubi: guidelines_sonofgodprinciples)
Maryamu Magadaliya ta je tace wa almajiran
Maryamu Magadaliya ta je inda almajiran suke zama sai ta faɗa masu abin da ta gani ta kuma ji. AT: "Maryamu Magadaliya ta je inda almajiran suke sai ta gaya masu" (Dubi: figs_explicit)
John 20:19-20
wannan rana, a rana ta farko ta mako
Wannan na nufin Lahadi.
Kofofin da almajiran suke, an kulle
AT: "almajiran sun kulle kofofin inda suke" (Dubi: figs_activepassive)
saboda tsoron Yahudawa
A nan "Yahudawa" magana ne na shugabanin Yahudawa wadda za su iya kama almajiran. AT: "domin sun ji tsoron cewa shugabanin Yahudawa za su kama su" (Dubi: figs_explicit)
Salama Agareku
Wannan sanannan suna ne da ke nufin "Bari Allah ya ba ku salama".
ya nuna masu hannuwansa da kuibinsa
AT: "ya nuna masu rauni a hannuwansa da kuibinsa" (Dubi: figs_explicit)
John 20:21-23
Kamar yadda Uba ya aiko ni, haka Ni ma na aike ku ... fadi masu haka, "Karbi Ruhu Mai Tsarki
Allah Uba ya aiko Allah Ɗa wadda yanzu ya ke aikan masubi a cikin ikon Allah Ruhu mai Tsarki.
Uba
Wannan muhimmin lakabi ne wa Allah. (Dubi: guidelines_sonofgodprinciples)
an gafarta masa
AT: "Allah zai gafarta masu" (Dubi: figs_activepassive)
mutumin da kuka rike zunubansa
"Idan ba ku gafarta zunuban wani ba"
an rikesu
AT: "Allah ba zai gafarta maku ba" (Dubi: figs_activepassive)
John 20:24-25
Ɗan Tagwai
Wannan sunan na miji ne da ke nufin "'yan biyu." Dubi yadda kun fasar wannan a cikin 11:15. (Dubi: translate_names)
almajiran daga baya sukace masa
Kalmar "shi" nanufin Toma.
Sa dai in na gani ... kuibinsa, ba zan gaskanta ba
AT: "Zan gaskanta idan na gan ... kuibinsa" (Dubi: figs_doublenegatives)
a cikin hannunsa ... kuibinsa
Kalmar "shi" na nufin Yesu.
John 20:26-27
almajiransa
Kalmar "shi" ya na nufin Yesu.
Sa'an da kofofin suna kulle
AT: "loƙacin da sun kulle kofofi" (Dubi: figs_activepassive)
kada ka zama mara bada gaskiya, amma ka bada gaskiya
Yesu ya yi amfani da wadannan maganganu "kada ka zama mara bada gaskiya" domin ya nanata kalmomin na biye, "amma ka bada gaskiya." Idan harshen ku bai yarda da abu biyu da ke a karkaceba, ko mai karatun ba zai gane cewa Yesu ya na nanata kalmomin da ka biye, ba sai kun fasara wannan magana. AT: "Wannan ne ma fi muhimmi a gare ku: dole ne ku gaskanta" (Dubi: figs_doublenegatives)
gaskanta
A nan "gaskanta" na nufin ba da gaskiya ga Yesu. AT: "ba da gaskiyan ku ga Yesu" (Dubi: figs_explicit)
John 20:28-29
ka bada gaskiya
Toma ya gaskanta cewa Yesu ya na da rai domin ya gan shi. AT: "ka gaskanta cewa ina da rai" (Dubi: figs_explicit)
Albarka ta tabbata ga wadanda
Wannan ya na nufin "Allah ya na ba da babban farin ciki ga wadanda."
wadanda basu gani ba
Wannan na nufin wadanda ba su san Yesu ba. AT: "wadanda basu gan shi da rai ba" (Dubi: figs_explicit)
John 20:30-31
alamu
Kalmar "alamu" ya na nufin abin al'ajibi da ya nuna cewa Allah ne mai dukka karfi wadda ya ke da cikakken iko a duniya.
alamu wadanda ba'a rubuta a littafin nan ba
AT: "alamun da marubucin bai rubuta akai ba a cikin wannan littafi" (Dubi: figs_activepassive)
Amma an rubuta wadannan
AT: "amma marubucin ya rubuta game da waɗannan alamun" (Dubi: figs_activepassive)
Dan Allah
Wannan muhimmin lakabi ne wa Allah. (Dubi: guidelines_sonofgodprinciples)
rai cikin sunansa
A nan "rai" magana ne da ya na nufin Yesu ya ba da rai. "za ku iya sami rai saboda Yesu" (Dubi: figs_metonymy)
Rai
Wannan ya na nufin rai na ruhaniya.
John 21
John 21:1-3
Muhimmin Bayani:
Yesu ya nuna kansa kuma ga almajiran a Tekun Tibariya. Aya 2 da 3 ya faɗa mana abin da zai faru a cikin labarin kafin Yesu ya bayyana. (Dubi: writing_background)
Bayan wadannan abubuwa
"Bayan waɗansu loƙaci"
da Toma wanda ake kira Ɗan Tagwai
AT: "da Toma wanda ake kira Ɗan Tagwai" (Dubi: figs_activepassive)
Ɗan Tagwai
Wannan sunan na miji ne da ya na nufin "yan biyu." Dubi yadda an fasara wannan suna a cikin 11:15. (Dubi: translate_names)
John 21:4-6
Samari
Wannan magana ne na kalma mai daɗi da ya na nufin "Abokai na na ƙwarai."
zaku samu wasu
Anan "wasu" na nufin kifi. AT: "za ku kama wasu kifi a cikin taru ku" (Dubi: figs_explicit)
jawo shi ciki
"jawo taru ciki
John 21:7-9
kauna
Wannan irin kauna ya na zuwa daga Allah ne ya na bisa kyaun mutane, ko bai amfani wani ba. Irin wannan kauna ya na kula da mutane, ko mai abin da sun yi
yayi damara da taguwarsa
"ya tsare taguwarsa a kewaye da shi" ko "ya sa kayansa"
don a tube yake
Wannan tushen bayani ne. Bitrus ya cire kayakin shi domin ya iya yin aiki, amma yanzu da zai gai da Ubangiji, ya so ya kara sa kaya. AT: "don ya tube waɗansu kayakin shi" (Dubi: writing_background)
jefa kanshi a cikin teku
Bitrus ya yi tsalle a cikin ruwa sai ya yi yanƙayi zuwa gaɓa. AT: "tsalle zuwa cikin tekun sai ya yi yanƙari zuwa gaɓa" (Dubi: figs_explicit)
jefa kanshi
Wannan karin magana ne da ya na nufin cewa Bitrus ya yi tsalle a cikin ruwa da sauri. (Dubi: figs_idiom)
domin basu da nisa da kasa, kamar kamu dari biyu zuwa sama
Wannan tushen bayani ne. (Dubi: writing_background)
kamu dari biyu
"mita 90." Kamu kaɗan ne da rabin mita. (Dubi: translate_bdistance)
John 21:10-11
Sai Saminu Bitrus ya hau sama
A nan "hau sama" na nufin Saminu Bitrus ya koma wurin kwalekwalen. AT: "Sai Saminu Bitrus ya kuma wurin kwalekwalen" (Dubi: figs_explicit)
ya jawo tarun gaci
"jawo taru zuwa gaci"
tarun bai tsage ba
AT: "basu karye ba" (Dubi: figs_activepassive)
cike da manyan kifaye dari da hamsin da uku (153)
"cike da manyan kifaye, dari da hamsin da uku." Akwai kifi 153. (Dubi: translate_numbers)
John 21:12-14
karya kumallo
abincin safe
karo na uku
Za ku iya fasara wannan maganan adadin jerantawa "uku" kamar "loƙaci 3." (Dubi: translate_ordinal)
John 21:15-16
kana kaunata ... kana kaunata
A nan "kauna" na nufin irin kauna dake zuwa daga Allah, wadda ya ke bisa kyaun mutane, ko bai amfani wani ba.
ka sani ina kaunarka
A loƙacin da Bitrus ya amsa, ya yi amfani da kalmar "kauna" wadda yake nufin kaunar 'yan'uwa ko kaunar aboki ko kuma ɗan iyali.
Ka ciyar da 'ya'yan tumakina
A nan "tumaki" magana ne na mutanen da suke kaunar Yesu kuma suna bin shi. AT: "ka ciyar da mutanen da ina kula da su" (Dubi: figs_metaphor)
Ka lura da Tumakina
A nan "tumaki" magana ne na mutanen da suke kaunar Yesu kuma suna bin shi. AT: "lura da mutanen da ina kula da su" (Dubi: figs_metaphor)
John 21:17-18
ya ce mashi na karo na uku
Kalmar "shi" ya na nufin Yesu. Anan "na uku" na nufin "loƙaci na uku." AT: "Yesu ya ce mashi na uku" (Dubi: translate_ordinal)
ka na kaunata
Wannan loƙacin da Yesu ya yi wannan tambaya ya yi amfani da kalmar "kauna" wadda ya ke nufin kaunar 'yan'uwa ko kaunar aboki ko kuma ɗan iyali.
ciyar da 'ya'yan tumakina
A nan "tumaki" magana ne da ya na wakilcin waɗanda sun zama na Yesu kuma suna bin shi. AT: "lura da mutanen da ina kula da su" (Dubi: figs_metaphor)
Hakika, hakika
Dubi yadda kun fasara wannan a cikin 15: 51.
John 21:19
Yanzu
Yahaya ya yi amfani da wannan kalma domin ya nuna cewa ya na ba da tushen bayani ne kafin ya cigaba da labarin. (Dubi: writing_background)
domin ya nuna irin mutuwar da Bitrus zai yi ga ɗaukakar Alla
A nan Yahaya ya na nufin cewa Bitrus zai mutu a kan gicciye. AT: "don ya nuna cewa Bitrus zai mutu a kan gicciye domin ya ɗaukaka Allah" (Dubi: figs_explicit)
ka biyo ni
A nan kalmar "biyo" na nufin "zaman Almajiri." AT: "cigaba da zama almajiran" (Dubi: figs_explicit)
John 21:20-21
almajirin da Yesu yake kauna
Yahaya ya kira kansa haka a duk lokaci a littafin, a maimakon kiran sunansa.
a cin abinci
Wannan ya na nufin abincin dare na karshe. (Dubi: John Chapter 13)
Bitrus ya gan shi
A nan "shi" na nufin "almajirin da Yesu yake kauna."
"Ya Ubangiji, Me mutumin nan zai yi?
Bitrus ya na so ya san abin da zai faru da Yahaya. AT: "Ya Ubangiji, me nene zai faru da wannan mutum?" (Dubi: figs_explicit)
John 21:22-23
Yesu yace masa
"Yesu yace wa Bitrus"
Idan ina so ya zauna
A nan "shi" ya na nufin ""almajirin da Yesu yake kauna" a cikin 21:20.
na zo
Wannan ya na nufin zuwan Yesu na biyu, dawowar sa duniya daga sama.
ina ruwanka?
Wannan magana ya bayyana kamar tambaya ne don ya bayana tsawa mara tsanani. AT: "ka da ku damu da wannan." (Dubi: figs_rquestion)
cikin 'yan'uwa
A nan "'yan'uwa" na nufin dukka masubin Yesu.
John 21:24-25
almajirin
" almajirin Yahaya"
wadda ya ke shaida game da wadannan abubuwa
A nan "shaida" ya na nufin cewa shi da kansa ya na gannin abubuwa. AT: "wadda ya gan dukka wadannan abubuwa" (Dubi: figs_explicit)
mun sani
A nan "mu" ya na nufin wadanda sun gaskanta da Yesu. AT: "mu da mun gaskanta da Yesu mun san" (Dubi: figs_explicit)
Idan da an rubuta kowannensu
AT: "Idan wani ya rubuto dukkansu" (Dubi: figs_activepassive)
ko duniya ba ta iya daukar litattafan ba
Yahaya ya zuguiguita domin ya nanata cewa Yesu ya yi abin al'ajibi dayawa fiye da abin da mutane na iya rubutawa a kai a cikin wannan littatafan. (Dubi: figs_hyperbole)
litattafan da za a rubuta
AT: "litattafan da mutane na iya rubutawa game da abin da yi" (Dubi: figs_activepassive)